21/07/2025
⚽ Kasuwar ’Yan Wasa: Sabbin Labarai.
• James McAtee (22, Man City)
Manchester City ta sanya farashin fam miliyan 35 kan ɗan wasanta James McAtee. Kungiyoyin West Ham da Eintracht Frankfurt na zawarcinsa.
• Marcus Rashford (Man United ➡️ Barcelona)
A cike da mamaki, Barcelona ta sanar da ɗaukar Marcus Rashford a matsayin aro daga Manchester United.
• Ibrahima Konaté (Liverpool)
Real Madrid na sha’awar ɗan wasan baya na Liverpool, Konaté (Faransa), amma za ta jira har zuwa badi kafin ta shiga tattaunawa.
• Vinicius Jr (Real Madrid)
Sabunta kwantiragin ɗan wasan gaba na Brazil, Vinicius Jr (25), an dage shi har zuwa shekarar 2026.
• William Saliba (Arsenal)
Real Madrid na ci gaba da sa ido kan ɗan bayan Arsenal, William Saliba (24).
• Mateo Joseph (Leeds United)
Leeds na duba yiwuwar sayar da Mateo Joseph (21, Spain) domin tara kuɗin da za ta sayo Rodrigo Muniz (24, Brazil) daga Fulham.
• Manchester United da Ruben Amorim
Kocin United, Ruben Amorim, na shirin ƙaro sababbin ‘yan wasa kafin fara kakar sabuwa.
• Viktor Gyökeres (Sporting CP)
United ta shiga zawarcin ɗan wasan gaba na Sporting, Viktor Gyökeres (27), tana fafatawa da Arsenal domin mallakarsa.
• Francesco Pio Esposito (20, Inter Milan)
Manchester United ta dawo da tayin da Inter Milan ta yi watsi da shi a Janairu domin ɗauko matashin ɗan wasan gaba na Italiya, Esposito.
• Bryan Mbeumo (Brentford ➡️ Man United)
United ta kammala binciken lafiyar ɗan wasan gaba na Kamaru, Bryan Mbeumo (25), daga Brentford.
• Jacob Ramsey (Aston Villa ➡️ Nottingham Forest)
Nottingham Forest na kan gaba wajen neman ɗan wasan tsakiya na Aston Villa, Jacob Ramsey (24).