ALU TV News

ALU TV News Nose for News — We share stories that matter.

12/08/2026

RANAR MATASA TA DUNIYA:

Rahoton Wakilinmu Naziru Alhaji Sani

As part of the ongoing international conference, Diversity and Social Peace (Partnership and Social Harmony), His Excell...
12/08/2026

As part of the ongoing international conference, Diversity and Social Peace (Partnership and Social Harmony), His Excellency Senator Aliyu M. Wamakko today attended the high-level meeting between Islamic and Christian leaders. The session, titled Religion and Building Social Harmony, was held at the Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre.

12th August, 2026

12/08/2026

ALU TV NEWS WEDNESDAY 12-8-2026

ƊAN TAKARAR MAJALISAR TARAYYA A JAM’IYYAR ADC, MANIRU SHUNI, YA KOMA APC A SOKOTO Yayin da siyasa ke daf da ɗaukar zafi ...
12/08/2026

ƊAN TAKARAR MAJALISAR TARAYYA A JAM’IYYAR ADC, MANIRU SHUNI, YA KOMA APC A SOKOTO

Yayin da siyasa ke daf da ɗaukar zafi a gabanin zaɓen shekarar 2027, siyasar Jihar Sokoto na ci gaba da fuskantar sauye-sauye, musamman tare da sauya sheƙa daga jam’iyyar adawa ta ADC) zuwa jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC).

Sabon sauyin da aka samu shi ne na ɗan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Bodinga/Dange Shuni/Tureta, Hon. Maniru Ibrahim Shuni, wanda aka fi sani da Barden Shuni, daga ADC zuwa APC.

Da yake bayyana dalilin matakin nasa, Hon. Maniru Shuni ya ce ya yanke shawarar barin tsohuwar jam’iyyarsa ne saboda abin da ya bayyana a matsayin rashin hangen nesa da ingantaccen shugabanci a cikinta.

Ya kuma ce matakin komawarsa APC ya samo asali ne daga ayyukan ci gaba da shirye-shiryen raya kasa da gwamnatin Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, ke aiwatarwa.

Da yake karɓar sabon ɗan jam’iyyar APC a gidansa da ke Asokoro a Abuja, jagoran APC a Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya yi maraba da Hon. Maniru Shuni zuwa jam’iyyar, tare da tabbatar masa da cewa za a ba shi dama da kuma yi masa adalci kamar sauran ’yan jam’iyyar.

Sanata Wamakko ya sake jaddada aniyar APC na ci gaba da tallafawa shirye-shirye da ayyukan raya kasa da za su inganta rayuwar al’ummar Jihar Sokoto.

Taron maraba da sabon ɗan jam’iyyar ya samu halartar Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyadi; Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Sokoto, Rt. Hon. Tukur Bala Bodinga; da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Sa hannu:
Bashar Abubakar
Mai Ba Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a

12 ga Agusta, 2026

Kamfanin Talla na FATSAM Advertising and Media Limited ta ƙaddamar da wani shiri na haɗin gwiwa da ALU TV Nigeria, da nu...
12/08/2026

Kamfanin Talla na FATSAM Advertising and Media Limited ta ƙaddamar da wani shiri na haɗin gwiwa da ALU TV Nigeria, da nufin faɗaɗa damar talla tare da ƙarfafa hulɗa da ’yan kasuwa, ƙungiyoyin kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki.

A yayin ziyarar ban girma da s**a kai ALU TV Nigeria, Manajan Darakta naFATSAM, Abdulfatai Abdusalam, ya ce haɗin gwiwar da ake shirin kafawa zai taimaka wa ’yan kasuwa da ƙungiyoyi wajen tallata kamfanoninsu, kayayyaki, ayyuka da shirye-shiryensu ga dimbin masu kallo ta kafafen watsa shirye-shiryen ALU TV.

Ya jaddada muhimmancin ingantaccen talla wajen gina martabar kamfani, faɗaɗa kasuwa da kuma haɗa ƙungiyoyi da masu kallo da sauraro.

Da yake karɓar tawagar, Babban Manajan ALU TV Nigeria, Bashar Abubakar, ya yi maraba da wannan shiri, tare da bayyana shirye-shiryen tashar na yin aiki tare da FATSAM wajen samar da ingantattun hanyoyin talla da tallata hajojin abokan hulɗa.

Ya kuma bayyana shirin ƙaddamar da wani shirin talabijin mai amfani da harsuna da dama, wanda zai ƙunshi Hausa, Yarbanci da Igbo, da nufin tallata ’yan kasuwa da kamfanoni, tare da inganta haɗin kan ƙasa, fahimtar al’adu da zaman lafiya tsakanin al’umma.

A yayin ziyarar, Bashir Rabe Mani ya gabatar da jawabi cikin Hausa, Mustapha Olatunde cikin Yarbanci, yayin da Sandra Ogechi Nwabueze ta gabatar cikin Igbo. Wannan ya nuna irin damar da shirye-shiryen harsuna da dama ke da wajen haɗa masu talla da al’umma masu bambancin harsuna a faɗin Najeriya.

Ana sa ran haɗin gwiwar zai ƙara faɗaɗa damar talla, bunƙasa kasuwannitare da ƙarfafa hulɗar kasuwanci tsakanin kafafen yaɗa labarai da ’yan kasuwa.

Ku kasance tare da ALU TV Nigeria Domin Haɗa ’Yan Kasuwa, Kamfanoni da Masu Kallo da Sauraro.

Talata, 11/8/2026

11/08/2026

ALU TV NEWS TUESDAY 11-8-2026

A yau, Mai Girma Sanata Aliyu M. Wamakko ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da haɗin kan ƙasa da aka gudanar a Abuj...
11/08/2026

A yau, Mai Girma Sanata Aliyu M. Wamakko ya halarci taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da haɗin kan ƙasa da aka gudanar a Abuja. An gudanar da taron ne a ranar Talata, wanda ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Najeriya ta shirya, tare da haɗin gwiwar Majalisar Musulmi ta Duniya (Muslim World League) ta ƙasar Saudiyya.

Taron na kwanaki biyu, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu, ya haɗa shugabannin addini, masu tsara manufofi, sarakunan gargajiya, jami’an diflomasiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna batutuwan tsaro da zaman lafiya tsakanin al’umma.

Daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna sun haɗa da satar mutane domin neman kuɗin fansa, ’yan bindiga, ta’addanci, yaƙi da tsattsauran ra’ayi, ƙarfafa al’umma, haɗin kan ƙasa, haƙuri a addini da bunƙasar tattalin arziki da zamantakewa.

Babban Sakataren Majalisar Musulmi, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Malaman Musulunci ta Duniya, ya iso Abuja jiya domin halartar taron.

Sheikh Al-Issa ya bayyana cewa ziyararsa ta mayar da hankali ne wajen ƙarfafa zaman lafiya da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin al’umma, yana mai jaddada cewa samun kwanciyar hankali a Najeriya zai taimaka matuƙa wajen tabbatar da zaman lafiya a Yammacin Afirka da ma sauran sassan duniya.

Ya kuma yaba da ƙoƙarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na inganta zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba a Najeriya.

11 ga Agusta, 2026

SANATA WAMAKKO YA HALARCI TARBAR BABBAN SAKATAREN MAJALISAR MUSULMI TA DUNIYA A ABUJAMai Girma Sanata Aliyu M. Wamakko, ...
10/08/2026

SANATA WAMAKKO YA HALARCI TARBAR BABBAN SAKATAREN MAJALISAR MUSULMI TA DUNIYA A ABUJA

Mai Girma Sanata Aliyu M. Wamakko, mamba a Majalisar Musulmi ta Duniya (Muslim World League), tare da sauran manyan wajen tarbar Sakataren, Rabitat al-Alam al-Islami, a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Wannan ziyara mai muhimmanci na zuwa ne gabanin taron ƙasa da ƙasa da ake shirin gudanarwa, wanda zai haɗa manyan malamai da shugabannin Musulunci, da sauran fitattun mutane domin tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi zaman lafiya, tsaro, haɗin kai da kuma ɗorewar ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Sanata Wamakko ya kasance tare da wata tawaga mai ƙarfi da ta haɗa da Gwamnan Jihar Sakkwato, Mai Girma Ahmad Aliyu Sokoto; Mai Girma Sanata Danjuma Goje; da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Alhaji Mohammad Maigari Dingyadi, da sauran manyan baki.

Allah Ya sanya albarka a wannan taro, Ya ba shi nasara, Ya kuma sanya shi zama sanadin inganta zaman lafiya, haɗin kai, ilimi da ci gaba ga al’ummar Musulmi da bil’adama baki ɗaya.

Litinin, 10 ga Agusta, 2026.

10/08/2026

07. MURADU 9 AKAN LAMURAN ADDININ MUSULUNCI

Address

Zoo Lane Area, Maiduguri Road
Sokoto

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ALU TV News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to ALU TV News:

Shortcuts

Share