15/08/2025
MAIGIRMA TSOHON MATAIMAKIN GWAMNAN JAHAR SOKOTO HON.DR.MANIR MUHAMMAD DAN IYA FCNA,CNA(WALIN SOKOTO)YA HALARCI DAURIN AUREN DIYAR ALH BALA LAWALI SABON BIRNI A GARIN KADUNA
A ya 15/08/2025 Maigirma Tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Sokoto Hon Dr Muhammad Manir Dan Iya FCNA,CNA(Walin Sokoto)ya halarci Ɗaurin diyar Alhaji Bala Sabon Birni wato Gimbiya Hadiza Lawali Bala Sabon Birni a Jahar kaduna
An dai daura Auren ne tsakanin Ango Mal. Ibrahim Alhaji Mu'azu da Gimbiyar sa Hadiza Lawali Bala Sabon Birni in da Danmajen sokoto ya nemi daurin auren a wajen Ministan tsaro wato Alh. Mohammed Badaru in da ya aminta ya bada auren akan sadaki naira dubu dari ukku(300,000)lakadan kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada
A wajen ɗaurin auren His Excellency Hon.Dr. Muhammad Manir Dan Iya FCNA,CNA(Walin Sokoto)na tare da Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa H.E Alhaji Muhammad Badaru da Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara H.E Mahmud Aliyu Shinkafi da Tsohon Mataimakin Gwamnan Jahar Katsina H.E Munir Abubakar da Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Sokoto Rt.Hon. Aminu Manyan Achida da Tsohon mai kula da ka'idojin Shugaban kasa Alh. Inuwa Baba(Protocol)hadi da Alh Sani Gobir(Yariman Gobir)da Alh Abubakar Dasuki(Danmajen Sokoto)
Daga Karshe Malamman addinin musulunci ne s**a Jagoranci Addu'o'i na musamman domin sanyawa wadan nan auren guda biyu Albarka
Allah SWT ya sanya Albarka a cikin wannan Auren na su ya ba su zaman lafiya tare da zuri'a dayyiba📿🙏
Shamsudeen Bello Hamma'ali
15 Aug 2025