
15/05/2025
🟢 HANYOYI BIYAR NA SAMUN JARI A NAJERIYA. (Part 6)
- Daga Littafin “TUSHEN JARIN KOWANE DAN KASUWA”
• Kusan kowane ɗan kasuwa ko mai sana’a ta wa’enan hanyoyin ya samu jarin sa.
🔵 HANYA TA SHIDA
— GUN UBANGIDA.
- BONUS!!! -
• A yau mutane da dama suna aiki ne ƙarƙashin wasu a matsayin iyayen gidan su.
• Mafi yawan lokuta za ka ci gaba da aiki ne ƙarƙashin ubangidan ka har na tsawon wasu shekaru inda a ƙarshe zai salame ka ko ya yaye ka.
• Sau da dama ba zai bar ka hannu rabbana ba, wani ubangidan zai baka jari domin kaima ka fara naka kasuwancin.
• Idan ka yi dace da wani ubangidan, zai siya maka fili kuma ya ɗau hidimar auren ka.
• Ama mafi ƙarancin abun da zaka samu a gun ubangida shine jarin fara naka kasuwancin. Wanda shine alƙiblar wanan littafin.
— DARASI:
• Za ka ɗau tsawon lokaci kana aiki ƙarƙashin wani kafin ka samu ƴancin fara naka kasuwancin.
• Tsawon shekaru kana aiki ƙarƙashin wani na nufin yawan ƙwarewar da zaka samu a wanan kasuwancin.
_______________________________
MASHA’ALLAH WA’ENAN SUNE HANYOYI SHIDA NA SAMUN JARI A NAJERIYA.
KU KALLI VIDEON DA NA ƊAURA A TASHAR MU TA YOUTUBE INDA NA YI BAYANI DALA DALA AKAN WA’ENAN HANYOYIN GUDA SHIDA.
Sunan Tashar: MU KOYA TARE
• Ku yi magana ta whatsApp 07072878168 domin mallakar kwafin littafin “TUSHEN JARIN KOWANE DAN KASUWA”
• Ku yi fallowing dina domin koyon ilimi da dubarun kasuwanci 👉 MU KOYA TARE