Iconic FM Nigeria

Iconic FM Nigeria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Iconic FM Nigeria, Broadcasting & media production company, 1B After Miyetti Allah Roundabout, Sokoto.
(2)

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya a 2027...
10/09/2026

Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya ce idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya a 2027, zai yi hutun Sallah tare da Sarkin Musulmi, Sultan na Sokoto.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya soki Shugaba Bola Tinubu kan yadda yake gudanar da hutun Sallah a Legas.

Ya ce a matsayinsa na shugaban ƙasa, zai yi amfani da lokacin Sallah wajen haɗa kan ’yan Najeriya, musamman a arewacin ƙasar.

"Sallah da komai, shi (Tinubu) yana yin sa ne a Legas. Musulmi ne. Ni zan je Sokoto in yi Sallah tare da Sultan, mu haɗa kowa wuri guda, mu tattauna makomar ƙasar. Zan je Kano,” in ji Obi.

A wani ɓangare na hirar, Obi ya ce NDC za ta kafa wani tsarin da zai ba ta damar tura sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe kai tsaye zuwa cibiyar tattara bayanai ta jam’iyyar a babban zaɓen 2027.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubak...
10/09/2026

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga Musulmi a faɗin ƙasar da su sanya ido domin fara duban sabon jinjirin watan Rabi’ul Thani na shekarar 1448 bayan hijira, daga ranar Juma’a 11 ga Satumban 2026.

Kiran na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Wazirin Sokoto kuma Shugaban Kwamitin Shawara kan Harkokin Addini na Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce ranar Juma’a 11 ga Satumba za ta kasance ranar 29 ga watan Rabi’ul Awwal na shekarar 1448 bayan hijira, inda ta buƙaci Musulmi da su yi ƙoƙarin ganin sabon jinjirin watan.

Sanarwar ta kuma buƙaci duk wanda ya ga jinjirin watan da ya gaggauta sanar da shugaban ƙauyen da yake ko Dagaci mafi kusa da shi.

A cewar sanarwar, shugaban ƙauyen ko Dagacin ne zai isar da bayanin ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi domin tabbatar da ganin watan da kuma fitar da sanarwar a hukumance.

Akalla mutum 24 ne s**a mutu bayan da ake zargin sun sha wata barasa da ake haɗawa a gida a ƙaramar hukumar Odigbo ta ji...
10/09/2026

Akalla mutum 24 ne s**a mutu bayan da ake zargin sun sha wata barasa da ake haɗawa a gida a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.

Gwamnatin jihar ta ce ta ƙaddamar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen, wadanda s**a mutu tsakanin ranar 3 zuwa 7 ga watan Satumban 2026.

Ƙarin bayani 👇

https://iconicfmhausa.online/mutum-24-sun-mutu-bayan-sun-sha-giya-a-jihar-ondo/

10/09/2026

ICONIC NEWS 10=9=2026

10/09/2026

LABARAN ICONIC 10 09 2026

Kwamishinan ’yan sandan jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shafa, ya gargaɗi shugabannin dukkan jam’iyyun siyasa na jihar ce...
10/09/2026

Kwamishinan ’yan sandan jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shafa, ya gargaɗi shugabannin dukkan jam’iyyun siyasa na jihar cewa rundunar za ta ɗora alhaki kai-tsaye a kansu tare da hukunta su idan magoya bayansu, ƙungiyoyin matasansu, ko masu amfani da kafafen sada zumuntarsu s**a tada zaune-tsaye a lokacin yaƙin neman zaɓen 2027.

​Shafa ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Laraba a birnin Sokoto yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya kira tare da shugabannin dukkan jam’iyyun siyasa na jihar, inda ya jaddada cewa rundunar za ta aiwatar da dokar zaɓe ta 2022 ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, kuma kwanakin zuba ido ana kallon masu laifi sun wuce.

​A cikin wata sanarwar manema labarai da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar a madadin kwamishinan, an bayyana cewa CP Shafa ya umarci dukkan jam’iyyun siyasa da su gaggauta miƙa jadawalin tarukan yaƙin neman zaɓensu ga rundunar ’yan sanda, domin kauce wa kiciɓus ɗin gangamin siyasa a rana ko wuri guda da zai iya janyo rikici.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addinai da su guji bayya...
10/09/2026

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya buƙaci shugabannin addinai da su guji bayyana matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a matsayin yaƙin addini.

Ministan ya gargaɗi cewa irin wannan fahimta ko furuci na iya ƙara raba kan ’yan ƙasa tare da kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kan Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Mohammed Idris ya kuma yi kira ga shugabannin Kirista da su yi amfani da matsayinsu da tasirinsu wajen yaɗa gaskiya, zaman lafiya, kishin ƙasa da kuma haƙuri tsakanin al’ummar Najeriya.

Ya jaddada cewa bai kamata a kai wa kowane ɗan Najeriya hari, ko kuma a nuna masa wariya saboda addininsa ko imaninsa ba, yana mai kira ga kowa da kowa da ya rungumi zaman lafiya da haɗin kai domin ci gaban ƙasa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta gana da shugabannin jam’iyyun siyasa da zababbun shugabannin kananan hukumomi domin...
10/09/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto ta gana da shugabannin jam’iyyun siyasa da zababbun shugabannin kananan hukumomi domin tattauna kalubalen tsaro gabanin fara yakin neman zabe da kuma zabukan da ke tafe a jihar.

An gudanar da tarukan daban-daban a hedikwatar rundunar ranar Laraba, inda s**a hada da jami’an ’yan sanda masu kula da sassa wato (DPOs), manyan jami’an ’yan sanda da wakilan jam’iyyun siyasa.

Ƙarin bayani 👇

https://iconicfmhausa.online/yan-sanda-sun-gana-da-jamiyyun-siyasa-a-sokoto-kan-yakin-neman-zabe/

10/09/2026

Shirin Gaskiyar Lamari kan yadda hare-haren 'yan bindiga ke ƙara yaɗuwa a sassan jihar Sokoto tare da Comrade, Nura Bodinga.

Address

1B After Miyetti Allah Roundabout
Sokoto
840101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Iconic FM Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share