12/09/2025
MATSAYIN MATAR DUNIYA ACIKIN ALJANNAH
A cikin Alkur’ani da Hadisan Annabi صلى الله عليه وسلم an bayyana cewa matan duniya masu biyayya da imani suna da matsayi mai girma a Aljannah. Ga wasu bayanai:
1. Matar duniya ta fi hurul-‘een
Annabi ﷺ ya ce:
Mata na duniya sun fi hurul-‘een da ibada da addu’a.
(Hadisi ya zo daga Ibnul Qayyim a Hadiyyatul Arwah).
Wannan yana nuna cewa mace ta duniya wadda ta yi imani, ta yi ibada, ta yi hakuri da addini, darajarta ta fi hurul-‘een.
2. Matar duniya za ta kasance tare da mijinta a Aljannah
Allah ya ce:
جَنَّاتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا وَمَنْ صَلَحَ مِنْ آبَائِهِمْ وَأَزْوَاجِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ
(Ar-Ra’d: 23)
Ma’ana:
Za su shiga Aljannah, tare da iyayensu, da matansu, da ‘ya’yansu waɗanda s**a yi salihi.
Wannan yana nuna cewa mace mai imani za ta kasance tare da mijinta na duniya idan shi ma ya shiga Aljannah.
3. Mace za ta kasance ‘yar Aljannah idan ta yi kyakkyawan hali
Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:
"Idan mace ta yi sallar ta, ta yi azuminta, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, za a ce mata:
Shiga Aljannah ta kowace ƙofa da k**e so.
(Ahmad da Ibn Hibban).
4. Matar duniya zata kasance mafi kyau da haske fiye da hurul-‘een
A cikin wasu riwayoyi, an ce idan mace ta duniya ta shiga Aljannah, Allah zai mayar da ita cikin siffar matashiya mai kyau fiye da hurul-‘een.
Za ta kasance ba ta tsufa, ba ta cutuwa, kuma kyawunta ba zai gushe ba.
ATAKAICE
Hurul-‘een za su kasance ne domin mazajen Aljannah.
Amma matar duniya mai imani darajarta ta fi su, saboda ta yi ibada da juriya.
Za ta kasance tare da mijinta idan shi ma ya shiga Aljannah.
Za a ba ta zabi kuma za ta sami matsayi mai girma fiye da yadda mutum zai iya zato.
Ya ALLAH kayimana Rabon dacewa da shiga Aljannah firdausy Ya Hayyu Ya Qayyum 🤲🤲🤲
[email protected]