Alminhajji tahqiq ila sabili najati, malami Abdullahi kaura yabo

  • Home
  • Nigeria
  • Sokoto
  • Alminhajji tahqiq ila sabili najati, malami Abdullahi kaura yabo

Alminhajji tahqiq ila sabili najati, malami Abdullahi kaura yabo I born in kaura yabo town 2/6/1986

NASIHACE : YANA DAGA ABINDA YAKE KYAUTATA RAYUWAR MUTUM IDAN YAKULA DA WADANNAN AZKAR ZAI SAMU KAMALA RAYUWA.:::::::::::...
16/06/2025

NASIHACE : YANA DAGA ABINDA YAKE KYAUTATA RAYUWAR MUTUM IDAN YAKULA DA WADANNAN AZKAR ZAI SAMU KAMALA RAYUWA.::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::: INSHALLAH ALLAH

​1. Hamdala tana yaye damuwa.​

​2. Hailala tana karfafa zuciya.​

​3.La-haula tana warware matsaloli.​

​4. Istigfari Yana Kawo Arziki.​

​5. Salati Yana daga darajar mutum.​

​​Allah yasa mu dace duniya da lahira.

19/04/2025

*_DIWANIN MAULANA SHEIKHUL ISLAM WA SA'ADATUL ANAM, ALHAJI IBRAHIM NIASS RTA

Shehu yace ;

بليت بحب المصطفى الختم احمد
An jarrabeni da Son Muɗafa(manzon Allah), cikamakin Annabawa, Ahmadu

ابي الكون والاخلاق فرعا ومحتدا
Asalin kasantattu da ɗabi'u, reshe da asali.

اتاني هواه قبل ان اعرف الهوى
Soyayyar sa (SAW) tazo mun, tin kafin insan soyayyar.

صليت بنيران اشتياقي احمد
Na ƙone da wutar begena ga Ahmadu(Manzon Allah SAW).

علقت به والناس في سنة الكرى
Na rataya da Annabi SAW, tun mutane suna cikin gyangƴadin bacci.

تمتعت منه الدهر اذ كنت مفردا
Na samu jindadi da shi, matuqar zamani., tin ina makaɗaici

وزوحمت في هذا الزمان وانني...
(Amma) an matsatseni a cikin wannan zamanin, Lallai ni,...

لفي غيرة ممن يروم محمد
Ina kishi, ga duk wanda yake nufin Annabi Muhammadu SAW.

ولكنني جليت قبل سباقهم
Saidai ni, na tsere musu (na zama na daya) tin kafin zuwansu.

وقد نلت تبريز القرون لاحمدا
Haqiqa na samu wuce tsararraki na wurin Annabi Muhammadu SAW.

ولم لا وعز العبد عز مليكه
Mai yasa bazan zamo haka bah, girman bawa, girman mamallakin shi ne.

فطوع يميني الكون عبدا مسودا
Halitta tana biyayya a dama na, ni bawa ne abun shugabantarwa.

الا يا رسول الله وارفع شكايتي...
Na'am ya Manzon Allah SAW, Ka ɗauki kokena ( kai ƙara ta)...

اليك وحالي ما ترى العبد سودا
Izuwa gareka, Halina yadda ka gani, ka shugabantar da wannan bawan.

فحاجي وحاج المسلمين احلته...
Buƙatuna , da buƙatun musulmai na saukar dasu...

عليك فطبت النفس حرا مسرمدا
A gareka, sai raina yayi daɗi, dan na zama Ɗa (ƴantacce) abun dawwamarwa.

زماني طلق الوجه غير مكدرا
Zamanina, (zamani ne) na sakin fuska, babu gurbata.

اروح واغدو داىما لن اكمدا
Ina yammaci, kuma ina sammako, a dawwame, ba a ɓata mun rai.

اغادي الصبوح عند افضل مرسل
Ina Sammakon karya wa, a wurin fiyayyan manzanni.

ومن برسول الله لم يخش جلمدا
Wanda duk yazamo tare da Manzon Allah SAW, bazai ji tsoron wani tsauri ba.

✍️✍️ Majazubin Baban Shehu 💯🙏

19/04/2025

Ilmin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam zama na 3

18/04/2025
NEMAN TAIMAKON MANZAN ALLAH SAW WAJIBI NE Rubutunnan nada matuqar yawa Ammafa lallai zai qara Qarfafa Mana gwiwa Idan mu...
16/04/2025

NEMAN TAIMAKON MANZAN ALLAH SAW WAJIBI NE

Rubutunnan nada matuqar yawa Ammafa lallai zai qara Qarfafa Mana gwiwa Idan muka daure mukakaranta.

Naga wani malami yana cewa muna rokon wanin Allah. Wannan maganar kawai siyasar addini ne. Mu ba mu taɓa cewa a roki wani da ba Allah ba; illa iyaka dai mun yarda ayyukan mu ba su kai mu roki Allah mu kaɗai ba tare da mun yi kamin kafa da amintaccen saba, wato Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Shi yasa zaka ji muna cewa: "Ya Allah, kabiya mana buƙatun mu albarkacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam)."

Sannan mun ga wata magana da wasu ke yadawa a ƙoƙarin su na fassara wannan aya: "Iyyaka na’budu wa iyyaka nasta’in," sai suke yi wa Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) rashin ɗa’a, suna cewa ko taimakon sa ne ba sa bukata. Ya kamata masu irin wannan su sani cewa za su iya rasa imanin su ba tare da sun sani ba. Domin kuwa ba ya halatta ka yi wa Manzon Allah rashin ɗa’a da sunan tabbatar da tauhidi. Saboda ai shi ɗin da kace ko nashi ɗin ne ba ka bukata, shine wanda Allah ya aiko da ita wannan ayar. Bayan ya zo maka da Islam, kuma ya yi gwagwarmaya domin tabbatar da addinin da shi da abokaninsa, har da wasu baffaninsa da sauran Sahabbai, sai da s**a taimake ka, s**a sadaukar da rayukan su, kafin ita wannan aya ta iso zuwa gare ka.

Ba mu taɓa jin inda ake irin wannan karatun ba na rashin ɗa’a ga Annabi, sai a arewacin Najeriya. Allah ya kyauta.

1. Tawassuli da neman albarka ta wurin Manzon Allah (SAW)

“Ya Allah, kabiya mana buƙatun mu albarkacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam).” irin Wannan ana kiransa Tawassuli ne a ilimin addinin musulunci bawai wanin Allah ake roƙa ba,, kuma yana da asali daga Alƙur’ani da Hadisi.

Alƙur’ani – Surah Al-Mā'idah 5:35

Arabic:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah, ku nemi hanyar kusanci zuwa gare Shi, ku yi jihadi a tafarkinSa, domin ku rabauta.”

Sharhi:
Wasīlah a nan tana nufin hanyar kusanci ga Allah, kamar yadda malaman tafsiri s**a ce itace ayyukan alheri, addu'a da kuma ta wurin wasu bayi nagari irin su Annabi (SAW).

Alƙur’ani – Surah An-Nisā’ 4:64

Arabic:
وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذْ ظَّلَمُوا أَنْفُسَهُمْ جَاؤُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّابًا رَحِيمًا

“Da idan s**a yi wa kansu laifi, sun zo wurinka (Ya Muhammad), s**a nemi gafarar Allah, kai kuma ka roƙa musu, da sun sami Allah Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai.”

Sharhi:
Wannan hujja ce cewa zuwa wurin Annabi (SAW) don roƙon gafara wajan Allah yana daga cikin hanyoyin samun rahamar ALLAH cikin sauki.

2. Girmamawa da biyayya ga Manzon Allah (SAW)

Alƙur’ani – Surah Al-Ḥujurāt 49:1-2

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيِ اللَّهِ وَرَسُولِهِ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ

“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Kada ku yi rashin ɗa'a ko azarɓaɓi a gaban Allah da ManzonSa, ku ji tsoron Allah. Lalle Allah Mai jin magana ne, Masani.”
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Kada ku ɗaga muryarku a bisa muryar Annabi…” rashin ɗa'a

Wannan aya tana tabbatar da cewa ladabi da biyayya ga Annabi (SAW) wajibi ne, kuma yana daga cikin alamun imanin mutum.

Hadisi Sahih al-Bukhari (Hadisi 15, littafin Imani)

لَا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى أَكُونَ أَحَبَّ إِلَيْهِ مِنْ وَالِدِهِ وَوَلَدِهِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ

“Babu wanda zai cika da imani har sai na fi soyuwa a gare shi fiye da mahaifinsa, ɗansa da dukkan mutane.”

3. Hadarin raina matsayin Annabi da sunan Tauhidi

Alƙur’ani – Surah At-Tawbah 9:65-66

وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ
لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ

“Idan ka tambaye su, sai su ce: ‘Ai muna wasa da raha ne.’ Ka ce: ‘Shin da Allah, da ayoyinSa, da ManzonSa kuke yin izgili?’ Kada ku ba da uzuri! Lalle kun kafirta bayan imanin ku.”

Wannan aya tana nuni da cewa raina Manzon Allah (SAW) da sunan wasa ko wani tsari yana iya sa mutum ya fita daga imani.

4. Matsayin Annabi matsayin rahama be ga dukkan duniya

Alƙur’ani – Surah Al-Anbiyā’ 21:107

Arabic:
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ

Fassarar Hausa:
“Ba mu aiko ka ba (Ya Muhammad), sai dai rahama ga dukan talikai.”

5. Shafa’ah Taimakon Annabi (SAW) a Lahira

Hadisi Tirmidhi (3613), Sahihul Jami’:

فَيَأْتُونَ إِلَىٰ مُحَمَّدٍ، فَيَقُولُ: أَنَا لَهَا، أَنَا لَهَا

“Sai mutane su je wurin Muhammad (SAW), sai ya ce: ‘Ni ne wanda zai iya yin ta, ni ne wanda zai yi ta (shafa’ah).’”

Tawassuli ta hanyar Annabi (SAW) ba haramun ba ne matuƙar an yi shi da sanin cewa Allah ne kaɗai Mai iko da amsa.

Girmamawa da biyayya ga Annabi (SAW) wajibi ne, kuma rashin yin hakan yana iya kai mutum ga barazanar rasa imani.

Annabi Muhammad (SAW) yana da matsayi na musamman wanda Allah da kansa ya girmama shi da shi.

Yakai ɗan uwa basai ka riƙa maimaita "Ko na Annabi ne baka buƙata ba" zaka tabbatar da Tauhidi domin kuwa furta irin wannan ka iya sakaka yin biyu babu.

Allah ya kare mu, Ya kare mana imanin mu albarkacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam

15/04/2025

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Alminhajji tahqiq ila sabili najati, malami Abdullahi kaura yabo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category