10/08/2026
SHIRU FA BA TSORO BANE
Idan kana neman Malamin addini wanda baya jin tsoro, kuma baya saka munafurci a lamarinsa idan ka samu Sheikh Sani Yahaya Jingir magana ta kare, har yau ina da yakini Malam Sani Yahaya Jingir ba kudi ya karba yake tallata Muslim ticket ba
Kafin Malam Sani Yahaya Jingir ya fadi abinda ya fada ranar asabar wanda ta jawo makiya Musulunci na zaginsa, wawayen Musulmai kidahumai na aibatashi...
Akwai babban Malamin addinin Nasara na jihar Pilato Rev. Ezekiel Dachomo, ya fadi cewa zasu kulla wata hadaka tsakanin mabiya addininsu, zasu tabbatar wa duniya cewa sune s**a fi Musulmai yawa a Nigeria, yace zaben Census na shekarar 2006 da akayi wanda ya nuna Musulmai sune s**a fi yawa a Nigeria karya ne, wai anyi aringizon nambobi
Ezekiel Dachomo yace sun hada mai da Sarakunan gargajiya na Arewa da suke addini daya, sun b***e daga yiwa Sarkin Musulmai biyayya saboda addini, Sarkin Kabilar TIV na jihar Benue shine jagoransu na Sarakunan Gargajiya masu bin addinin Nasara, sun shirya meeting a Abuja, zasu tabbata Musulmi bai sake zama Shugaban Nigeria ba, (zan sa muku link na bidiyo da yayi wannan maganganu a comment section ku saurara)
Amma saboda tsabagen munafurci da raini baku caccaki Rev Ezekiel Dachomo ba da yayi wadancan maganganu sai Malam Sani Yahaya Jingir kuke caccaka, saboda kun mayar dashi karamar danga saukin hayewa ko?
Kuma abinda Malam Sani Yahaya Jingir ya fada ai gaskiya ne cewa Musulmai ne s**a fi yawa a Nigeria, mu muke auren mata hudu, a gidan Musulmi daya a samu akwai mutane sama da 40, su kuma sun takaita akan mace daya, yara biyu ko uku
Maganar Malam cewa ayi Muslim Muslim ticket ra'ayinsa ne da kuma fahimtarsa, dokar Kasa ta bashi damar yayi haka, k**ar yadda Rev Ezekiel Dachomo yake cewa zasu tabbata Musulmi bai sake zama Shugaban Nigeria ba a zaben 2027, shima Malam Sani Yahaya Jingir dan Nigeria ne da yake da cikakken 'yancin ya kare addininsa
'Yan uwa Musulmai ku yi hankali kar a yaudareku a sa muku tsanar Malamin da yake son ku, duk abinda sukeyi ajanda ne na yakin kwakwalwa domin su cusa mana Peter Obin Biafra, suna son sake yin siyasar addini ne a zaben 2027
Muna tare da Malam Sani Yahaya Jingir dari bisa dari, siyasar addini kuma a zuba a gani waye zai fadi
Ubangiji Allah Ka tsare mana rayuwar Sheikh Sani Yahaya Jingir