
29/07/2025
JIYA BA YAU BA – Idon Afrika
⭕ Abubuwa Hudu da Kan Wargaje Zumunci Idan Kai Zuciya Nesa Ba:
1. Dukiya – rikici na iya faruwa saboda kudi.
2. Biye wa mace har sai zumunci ya shiga hadari.
3. Hassada tsakanin juna – kamar wuta a cikin itace.
4. Mutuwa – ita kuwa dole ce, ba makawa.
⭕ Hanyoyi Hudu da Mace Ke Lalata Gidanta:
1. Raina mijinta ko iyayensa ko danginsa.
2. Nuna bambanci tsakanin 'ya'yanta da sauran yaran gidan.
3. Zargi da tsananin kishi ba tare da hujja ba.
4. Caccaka, gori da kalaman da ke da ciwo – waɗannan ba su cika mantuwa ba.
⭕ Abubuwa Hudu da Ke Rage Darajar Mutum a Idon Jama'a:
1. Yawan magana marar amfani.
2. Dariya marar iyaka irin ta wauta.
3. Karya, cin amana da saba alkawari.
4. Gulma da annamimanci – sun fi cutar da mai yi.
⭕ Hanyoyi Hudu da Miji Ke Dagula Gidansa:
1. Rashin kusanci da iyali da rashin tattaunawa da su.
2. Wulaƙanta haƙƙin gida da nuna babu damuwa.
3. Kiyayya da rashin nuna ƙauna ko tausayi.
4. Rowa da kin ɗaukar nauyin gida – girman kai ne ke gurbata auratayya.
⭕ Idan Ka Karanta Wannan Rubutu, Ga Buƙata Ta Hudu:
1. Ka yi aiki da abin da ka fahimta.
2. Ka tura wa wasu domin su ma su amfana.
3. Ka sanya mu cikin addu’arka – neman ƙarin lafiya, imani, da gafara.
4. Ka roƙi alheri gare ka da kuma musulmi baki ɗaya.