Sokoto post

Sokoto post Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sokoto post, Media/News Company, Sokoto.

Digital journalist
Blogger
Media consultant
writer
Digital Marketer
Media influencer

This is where you will learn About all the latest development in Sokoto State and beyond.............

Babban Kwamitin da uwar jam’iyyar African Democratic Congress ta ƙasa ta tura ya kammala tantance ‘dan takarar majalisa ...
20/05/2026

Babban Kwamitin da uwar jam’iyyar African Democratic Congress ta ƙasa ta tura ya kammala tantance ‘dan takarar majalisa na jaha inda ya amince da Hon. Muzammilu Almu Alkanchi ɗan majalisar jiha daga karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ta 2.

Tantancewar na zuwa ne a matsayin wani muhimmin mataki na shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓe, wanda ke nuni da yadda ADC ke ƙoƙarin tabbatar da sahihanci da bin ka’idoji wajen fitar da ‘yan takara

DA DUMI-DUMI:Peter Obi ya zama halastaccen ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC bayan kwamitin tantancewa ya tabbat...
20/05/2026

DA DUMI-DUMI:
Peter Obi ya zama halastaccen ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC bayan kwamitin tantancewa ya tabbatar da shi a matsayin ɗan takara guda ɗaya tilo kafin zaɓen fidda gwani na 2027.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Sam Egwu ya bayyana cewa Obi ya cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulki da dokar zaɓe, tare da gamsuwa da amsoshin da ya bayar yayin tantancewar.

An kuma miƙa masa takardar shaidar amincewa da fom ɗin tsayawa takara mai lamba 001 bayan ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja tare da rakiyar Victor Umeh.

Yayin da ake kallon zaɓen 2027 da ɗuminsa ke ƙaruwa, wannan mataki na nuna cewa jam’iyyar NDC ta fara tsara tafiyarta ne da cikakken goyon baya ga Peter Obi

20/05/2026

DA DUMI-DUMI: Daruruwan matasa sun mamaye sakateriyar jam'iyyar APC da ke Abuja domin nuna kin amincewar su game da tsayar da tsohon gwaman jihar Kogi Yahya Bello a matsayin dan takarar sanatan Kogi ta tsakiya.

Me za ku ce?

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa gyare-gyaren haraji da gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun ta...
20/05/2026

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa gyare-gyaren haraji da gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun ta’allaka ne kan tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya wajen tafiyar da harkokin haraji a ƙasar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris Malagi ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da shugabannin ofisoshin haraji da jami’an ma’aikatar tattara haraji s**a kai a Abuja.

Ya ce manufar sauye-sauyen ita ce ƙarfafa amincewar jama’a da hukumomin gwamnati, tare da samar da tsarin haraji mai inganci wanda zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da inganta ayyukan gwamnati ga al’umma.

jambiyar ADC a jihar sokoto tanfara tan tan ce yan takarar majalisar dokokin jahar sokoto na Jim iyyar  wato African dem...
20/05/2026

jambiyar ADC a jihar sokoto tanfara tan tan ce yan takarar majalisar dokokin jahar sokoto na Jim iyyar wato African democratic congress ADC

𝗦𝗮𝗻𝗮𝘁𝗮 𝗦𝗮’𝗶𝗱 𝗔𝗵𝗺𝗲𝗱 𝗔𝗹𝗸𝗮𝗹𝗶 𝗬𝗮 𝗞𝗮𝘂𝗿𝗮𝗰𝗲 𝗪𝗮 𝗭𝗮𝗯𝗲𝗻 𝗙𝗶𝗱𝗱𝗮 𝗚𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗻𝗮 𝗔𝗣𝗖 𝗮 𝗚𝗼𝗺𝗯𝗲Tsohon Ministan Sufuri na Najeriya kuma mai nema...
20/05/2026

𝗦𝗮𝗻𝗮𝘁𝗮 𝗦𝗮’𝗶𝗱 𝗔𝗵𝗺𝗲𝗱 𝗔𝗹𝗸𝗮𝗹𝗶 𝗬𝗮 𝗞𝗮𝘂𝗿𝗮𝗰𝗲 𝗪𝗮 𝗭𝗮𝗯𝗲𝗻 𝗙𝗶𝗱𝗱𝗮 𝗚𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗻𝗮 𝗔𝗣𝗖 𝗮 𝗚𝗼𝗺𝗯𝗲

Tsohon Ministan Sufuri na Najeriya kuma mai neman tikitin takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Sanata Sa’id Ahmed Alkali, ya sanar da kaurace wa shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

A cikin sanarwar da aka rawaito, Sanata Alkali ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan abin da ya kira rashin bin kundin tsarin mulki, dokokin ƙasa da kuma ƙa’idojin jam’iyyar APC wajen gudanar da zaɓen fidda gwani.

Ya ce ba zai shiga tsarin da yake ganin an kauce wa adalci da gaskiya ba, yana mai jaddada buƙatar a mutunta dokoki da ƙa’idojin dimokuraɗiyya domin tabbatar da sahihin shugabanci

CIKIN DARE: Obi ya ziyarci gidan Kwankwaso Da Ke Abuja.Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran darikar kwankwasiyya, Rabi...
20/05/2026

CIKIN DARE: Obi ya ziyarci gidan Kwankwaso Da Ke Abuja.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran darikar kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karbi Bakuncin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da ke Abuja.

Ziyarar na zuwa ne awanni kaɗan bayan Obi ya halarci tantancewar neman takarar shugaban ƙasa a shelkwatar jam’iyyar NDC da ke babban birnin tarayya Abuja.

Har yanzu ba a bayyana cikakken abin da jagororin biyu s**a tattauna ba, sai dai masu sa ido na ganin ganawar na da alaƙa da tattaunawar siyasa da ke ci gaba kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Wasu daga cikin manyan mutane a Najeriya da su ka kasance magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal:Aliko Dangote At...
19/05/2026

Wasu daga cikin manyan mutane a Najeriya da su ka kasance magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal:

Aliko Dangote
Atiku Abubakar
Khalipa Muhammad Sunusi
Abubakar Bokala Saraki
Tony Elumelu
Dino Malaye

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Honarabul Yusuf Buhari ya kai ziyarar ban girma ga hamshakin ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal, a gidansa da ke cikin gar...
19/05/2026

Honarabul Yusuf Buhari ya kai ziyarar ban girma ga hamshakin ɗan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal, a gidansa da ke cikin garin Katsina a yau Talata.

Ziyarar ta nuna kyakkyawar alaƙa da girmamawa tsakanin manyan jagorori da masu ruwa da tsaki a jihar, yayin da aka gudanar da ganawar cikin yanayi na mutunta juna da sada zumunci.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina.

DA DUMI-DUMI: T.Y Danjuma Ya Ba da Gudunmawar Naira Biliyan 3 a wajen Kaddamar da Littafin Tarihin Rayuwar Gowon a Abuja...
19/05/2026

DA DUMI-DUMI: T.Y Danjuma Ya Ba da Gudunmawar Naira Biliyan 3 a wajen Kaddamar da Littafin Tarihin Rayuwar Gowon a Abuja

Tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma, ya ba da gudunmawar Naira biliyan 3 a ranar Talata yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Yakubu Gowon, a Abuja.

Littafin mai taken “My Life of Duty and Allegiance” ya jawo halartar manyan baƙi da s**a haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron.

Hamshaƙin attajirin Afirka, Aliko Dangote, shi ma ya tallafa wa ƙaddamarwar da gudunmawar Naira miliyan 500 ta hanyar sayen kwafen littafin, yayin da sauran fitattun ’yan Najeriya s**a bayar da nasu gudunmawar a wajen bikin.

me zakuce

Address

Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sokoto post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share