TrendPost Hausa

TrendPost Hausa Gidan jaridar yanar gizo mai kawo sahihan labarai cikin gaggawa. Muna kawo labaran siyasa, tsaro, nishadi da sauran al’amuran yau da kullum cikin harshen Hausa.

Bikin Al'adun Ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello Zaria Yaja Hankalin Al'umma Sosai. Freedom Radio InternationalPlease follow T...
18/08/2026

Bikin Al'adun Ɗaliban Jami'ar Ahmadu Bello Zaria Yaja Hankalin Al'umma Sosai.

Freedom Radio International

Please follow TrendPost Hausa and share for more updates

AKWAI KURA: GWAMNONIN JAM'IYYAR APC SU SHAFA WA KANSU RUWABabban darasi daga zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da ya guda...
16/08/2026

AKWAI KURA: GWAMNONIN JAM'IYYAR APC SU SHAFA WA KANSU RUWA

Babban darasi daga zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da ya gudana jiya asabar

Ana dab da kammala kirga kuri'un zaben kujeran Gwamnan jihar Osun da aka yi jiya, sakamakon zabe na karamar hukuma daya ne kadai ya rage zuwa yanzu da nake rubutu

Ga sakamakon zaben:
👇
Accord: 487,553
APC: 420,164
ADC: 16,525
Jam'iyyar Accord Party ta bawa jam'iyyar APC mai mulkin Kasa ratar kuri'u 67,389, wanda hakan na nufin jam'iyyar APC ta fadi zaben jihar Osun

Gwamna mai ci Ademola Adeleke ya sake neman tazarce a jam'iyyar Accord Party, ya hadu da manyan kalubale kasancewar ba a jam'iyyar APC mai mulkin Kasa yake ba

Kafin a kai ga gudanar da zaben anyi ta samun manyan rikici na siyasa a jihar musamman tsakanin jam'iyyar Accord da APC da take son kwace mulkin

Akwai wani sanannen mawaki dan uwan Gwamna Adeleke da ake kira Davido, har karan Gwamnatin tarayya ya kai zuwa gaban Shugaban Amurka domin kar ayi amfani da karfin gwamnatin tarayya a murda zaben jihar Osun

Kusan Gwamnonin jam'iyyar APC gaba daya sai da s**a je jihar Osun shekaran jiya domin su bada gudunmawa wajen kwace kujeran mulki, har da Dr Abdullahi Umar Ganduje ya je, an tsaurara dukkan matakai na tsaro

To amma a karshe Allah Ya bawa Gwamna Adeleke nasara duk da karfin da jam'iyyar APC take da shi, zata iya murda zaben, amma ta bari akayi zabe na gaskiya, abinda ba'a yi zato ba

Magana ta gaskiya Gwamnonin jam'iyyar APC su shiga taitayinsu, su shafa wa kansu ruwa, kar su yi tsammanin zasu ci bulus a babban zaben 2027, murdiyan zabe zai zama tarihi, muna digital era ne, komai a fili yake

Duk Gwamnan da ya san bai taimaki talaka ba, bai yi aikin da ya kamata ba, to ya shafa wa kansa ruwa, zaben 2027 iya ruwa ne fidda kai, shima Shugaba Tinubu ta kansa yake a zaben 2027 mai zuwa, pressure ya masa yawa, ana ta kai karansa zuwa Amurka

Zaben jihar Osun babban sako ne da fadakarwa zuwa ga Gwamnonin jam'iyyar APC wadanda suke ganin zasu ci bulus, su sani karfin iko, tururuwan shiga jam'iyyar APC mai mulkin Kasa da yin taron dangi, ba zai basu mulki ba, su yi abinda zai gamsar da talakawa masu zabe kafin lokaci ya kure shine kadai mafitarsu

Muna rokon Allah Ya haramta wa maciya amana nasaran da suke nema a siyasar Nigeria

Daga Datti Assalafy

Ku cigaba da following TrendPost Hausa domin sanin halin da duniya ke ciki

BIKIN RANAR AL’ADUN JAMI’AR AHMADU BELLO, ZARIAAn gudanar da Bikin Ranar Al’adun Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, wani...
15/08/2026

BIKIN RANAR AL’ADUN JAMI’AR AHMADU BELLO, ZARIA

An gudanar da Bikin Ranar Al’adun Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, wani gagarumin biki da ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar Najeriya.

ABU Zaria ta sake nuna matsayinta a matsayin cibiyar ilimi, al’adu da haɗin kan al’umma

Rundunar ’Yan Sanda Ta Tura Jami’ai 15,000 Da Kwamishinoni 30 Domin Kula Zaben Jihar OsunRundunar ’Yan Sanda ta tura jam...
14/08/2026

Rundunar ’Yan Sanda Ta Tura Jami’ai 15,000 Da Kwamishinoni 30 Domin Kula Zaben Jihar Osun

Rundunar ’Yan Sanda ta tura jami’anta guda 15,000 da Kwamishinonin ’Yan Sanda 30 domin kula da zaɓen Gwamnan Jihar Osun da za a gudanar gobe Asabar, 15 ga Agusta 2026.

A gefe guda, INEC ta fara raba kayan zaɓe a Osogbo, yayin da rundunar ’yan sandan ta ce za ta yi amfani da helikwafta da drones wajen sa ido da tabbatar da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.

Please follow TrendPost Hausa and share for more

14/08/2026

Kayyasa🤣🤣 Uwa da 'Da Sun Haɗu akan megida

YAYI AMAI YA LASHE: Bayan Yayi Rantsuwa da Alkur'ani akan ba zai Taba barin Kwankwaso da Kwankwasiyya ba,Daga Karshe Hon...
13/08/2026

YAYI AMAI YA LASHE: Bayan Yayi Rantsuwa da Alkur'ani akan ba zai Taba barin Kwankwaso da Kwankwasiyya ba,Daga Karshe Hon Kabiru Kofar Ruwa Ya fice Daga Jam'iyyar NDC Kwankwasiyya ya Bar Kwankwaso ya Koma Jam'iyya APC Mai Mulki.

Me za ku ce?.

FOLLOW TrendPost Hausa

Erdoğan Ya Karɓi Iyalan Shahidai a Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya.Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya karɓi...
13/08/2026

Erdoğan Ya Karɓi Iyalan Shahidai a Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya.

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya karɓi iyalan jami’an tsaro da sojojin da s**a rasa rayukansu wajen kare ƙasarsu, a fadar shugaban ƙasa ta Cumhurbaşkanlığı Külliyesi da ke Ankara.

A yayin ganawar, Erdoğan ya bayyana muhimmancin girmama juna tare da tunawa da waɗanda s**a sadaukar da rayukansu domin kare ƙasa, tare da jaddada cewa iyalan shahidai suna da matsayi na musamman a cikin al’ummar Turkiyya.

Ganawar ta kasance wani bangare na ayyukan shugaban ƙasar na nuna goyon baya da kulawa ga iyalan waɗanda s**a rasa rayukansu wajen yi wa ƙasa hidima.

Erdoğan ya kuma ci gaba da jaddada cewa ƙasar Turkiyya ba za ta manta da sadaukarwar da jami’an tsaro da sojojin ƙasar s**a yi ba, musamman waɗanda s**a mutu suna gudanar da ayyukansu na kare rayuka da tsaron ƙasa.

Ku cigaba da following TrendPost Hausa da share

13/08/2026

Ance gasa suke saboda budurwa 😂🤣

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Aminu Abubakar Inyass Arzai, Abubakar Rabiu, Abubakar San...
13/08/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Aminu Abubakar Inyass Arzai, Abubakar Rabiu, Abubakar Sani Aboki

03/05/2026

Idonku biyu ko kunyi Barci?

Address

Kaduna
Sokoto
810282

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TrendPost Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share