27/04/2026
GASKIYA DAYA TV UPDATES
APC ZA TA GUDANAR DA ZABEN FIDDA GWANI NA KAI TSAYE A JIHOHI 36 DA FCT ABUJA
… Ta ce babu batun tsayar da dan takara ta hanyar sulhu!
Shugabancin kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya sanar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da dukkan mambobin jam’iyyar cewa za a gudanar da zaben fidda gwani na kai tsaye a dukkan jihohi 36 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Haka kuma, an fitar da jadawalin zaben fidda gwani kamar haka:
ZABEN FIDDA GWANI NA SHUGABAN KASA:
Jumma’a 15 ga Mayu zuwa Asabar 16 ga Mayu, 2026
ZABEN FIDDA GWANI NA ‘YAN MAJALISAR WAKILAI:
Litinin 18 ga Mayu, 2026
ZABEN FIDDA GWANI NA SANATA:
Laraba 20 ga Mayu, 2026
ZABEN FIDDA GWANI NA MAJALISAR JIHA:
Alhamis 21 ga Mayu, 2026
ZABEN FIDDA GWANI NA GWAMNA:
Asabar 23 ga Mayu, 2026
Shugabancin jam’iyyar ya kuma bayyana karara cewa ba za a amince da tsarin tsayar da dan takara ta hanyar sulhu ba a wannan zabe na fidda gwani a duk fadin jihohi 36 da Abuja, tare da tabbatar wa duk masu neman takara cewa za a ba kowa dama iri daya.
SIYASA HARKA CE TA KASA (GRASSROOT).
Don haka, ana kira ga duk masu neman takara da su koma mazabunsu, su ci gaba da hulda da jama’a tare da karfafa goyon bayan kasa, su kuma tallafa wa jama’a ta fuskar kudi da sauran hanyoyi, domin samun nasara a zaben fidda gwani na APC.