24/04/2024
Allah ya tabbatar
SABUWAR DOKAR YANCIN MAJALISUN KANANAN HUKUMOMI.
Bayan daukar lokaci mai tsayi ana ta kai ruwa rana game da batun bayar da yancin cin gashin kan kananan hukumomi ta fuskar tasrifin kudaden da doka ta bada damar a basu.
A wannan rana ta talata, majalisun dokokin kasar nan wato wakilai da dattawan sun amince da dokar data bada dama ga kananan hukumomi kasar nan 774 damar cin gashin kansu ta hanyar kashe kudaden su.
Wannan mataki da majalisun s**a dauka, ya aiwatu ne ta hanyar yin gyara ga sashi na 124 na kundin tsarin mulkin kasar nan.
Sashin na 124 dai ya fayyace dokar samar da kananan hukumomin a matsayin daya daga cikin murahun zartarwa wato tarayya da jihohi sai kuma su kananan hukumomin, ba tare da yin katsalandan daga bangaren gwamnatocin jihohin su ba.
Gyaran dokar da majalisun s**a aiwatar na cikin kudurorin da majalisar wakilai ta amince da su a makon da ya gabata wanda majalisar dattawa ta amince da shi a wannan rana.
Kwamitocin zaurukan majalisun na dattawa da wakilai sun hada gyararrakin da s**a aiwatar kan dokar wadda s**a fara tun a watan maris da ya gabata.
Da wannan ci gaba, yanzu a iya cewa majalisun sun amince da dukkan sadarori 23 da kuma sashin da s**a yi gyaran akai.
Za'a aike da sabon kudurin dokar ga zaurukan majalisun dokoki na jihohi domin amincewar su.
Haka zalika zasu amince da dokar samar da mai binciken kudi na kananan hukumomi sai kuma sabuwar hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi ta jihohi.
A gefe guda kuma majalisar ta amince da kwace damar da hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohi ke da su na gudanar da zaben kananan hukumomi, a maimakon hakan, dokar ta mika ragamar hakan ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC.
A bangaren zaben dai, majalisun sun aiwatar da gyara ga sashi na 65 da 106 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, inda ta amince da samar da wani bangaren da zai bada dama ga dan takara mai zaman kansa wato indifenda wanda baya karkashin kowacce jam'iyya tare da baiwa irin wa