20/09/2025
                                            Matashin Jigawa Ya Bayyana: Ismail Muhammad Adam Ya Lashe Miliyan 10 A Gasar Fasaha Ta Afirka
Wani matashi ɗan asalin jihar Jigawa, Ismail Muhammad Adam, ya yi abin alfahari ga Arewa bayan ya zama na uku (2nd Runner-Up) a gasar fasaha mafi girma a Afirka – Digital for All Challenge.
Gasar, wacce Tech4Dev ta shirya tare da haɗin gwiwar Foreign, Commonwealth & Development Office (FCDO), NITDA da UK-International Development Tech Hub, ta tanadi wani dandali na gwada ƙwarewa a fannin fasaha da koyon yadda ake amfani da ita a aikace.
Ismail, wanda ya wakilci Yankin Arewa maso Yamma, ya fito kan gaba a rukuni na matasa (Youth Intermediate Category) wanda shi ne mafi girma a gasar.
A matsayin lada, Ismail Muhammad Adam ya samu ₦10,000,000 tare da takardar shaidar ƙwararren mai haɓaka manhajar kwamfuta (Certified Software Developer) – babban ci gaba a rayuwar aikinsa.
Abin da ya ƙara jan hankali shi ne Ismail shi kaɗai ne ɗan takara da jami’an gwamnatin Jigawa s**a raka zuwa gasar, alamar jajircewar gwamnatin jihar wajen bunƙasa ilimin fasaha da ƙarfafa matasa. Sabon Daraktan Hukumar ICT da Tattalin Arzikin Dijital ta jihar ya kasance tare da shi har zuwa ƙarshen gasar, yana bayar da muhimmin tallafi.
Taƙaitaccen Saƙo:
Matashin ɗan Jigawa ya kafa tarihi a gasar fasaha ta Afirka, ya lashe miliyan 10, kuma ya samu takardar shaidar ƙwarewa a fannin haɓaka manhajar kwamfuta.