24/06/2026
TA'AZIYYA DA ALHINI GA MASOYA ANNABI MUHAMMADU SAWﷺ,
إنا لله وإنا إليه راجعون
Muna miƙa ta'aziyyarmu da alhini mai girma ga ruhin Manzon Allah ﷺ, ga iyalansa tsarkaka, ga matansa masu daraja, ga sahabbansa, ga Ahlul Baiti baki ɗaya, da ga dukkan masoya Annabi Muhammad ﷺ a kan babban abin baƙin ciki da ya faru da jikan Manzon Allah ﷺ, Al-Husayn ibn Ali رضي الله عنه.
Yau, yayin da muke tuna Karbala, zukata suna jin zafi, idanu suna cika da hawaye, ba don mun yi shakka ga ƙaddarar Allah ba, sai dai saboda girman masifar da ta auku ga ɗaya daga cikin mafiya tsarki a cikin al'ummar Muhammad ﷺ
Muna miƙa ta'aziyya ga duk wanda ke son Annabi ﷺ, domin wanda ya so Annabi ﷺ, to lallai yana son Husain. Kuma wanda ya san matsayin Husain a wajen Manzon Allah ﷺ, zuciyarsa ba za ta rasa jin raɗaɗi ba idan ta tuna da abin da ya faru da shi.
Ya Husain!
Kai ne abin ƙaunar Manzon Allah ﷺ
Kai ne furar gidan Annabci.
Kai ne ɗan Fatima Az-Zahra (RA), kuma jinin Aliyu bn Abi Talib (RA).
Ya Allah!
Ka ƙara ɗaukaka darajar Imam Husain (RA)
Ka yarda da shi tare da duk kan Ahalilbaiti da kakansu shugaba jagaba sayyadina rasulillahi sallalahu alaihi Wasallama Manzon Allah ﷺ
Ya Ubangiji bayi
Ka sa ƙaunar Ahlul Baiti ta zauna a cikin zukatanmu Ka haɗa mu da Annabi Muhammad ﷺ, da iyalansa tsarkaka, da sahabbansa da dukkan salihan bayi baki ɗaya a Aljannar Firdausi albarkaci shehu tijjani (RTA) da shehu Ibrahim inyass RTA da mai gidan namu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.
Allahumma salli wa sallim wa barik ala Sayyidina Muhammad, wa ala alihi wa ashabihi ajma'in.
رضي الله عن الحسين، وعن أهل البيت أجمعين.
Ameen.
Muna wa makasan Imam Hussain da dukkan wayan da aka wa kisan gilla a addini musulunci Allah ya la'anci su ya tona musu asiri a Lahira bijahi sayyadina rasulillahi sallalahu alaihi