15/09/2026
๐ SANARWA TA MUSAMMAN
NADIN SABABBIN ALฦALAN MUSABAฦAR KARATUN AL-QURโANI MAI GIRMA
Majalisar Zartaswa ta Jamaโatu Izalatil Bidโah Waโiqamatis Sunnah (JIBWIS), NHQ Jos, Reshen Jihar Zamfara, ฦarฦashin jagorancin Ash-Shaikh Abdullahi Umar Dalla-Dalla, ta amince da nadin sabbin Alฦalan Musabaฦar Karatun Al-Qurโani Mai Girma na matakin Jiha, waษanda za su gudanar da Alฦalanci da tantance gasar Karatun Al-Qurโani Mai Girma karo na 30.
Wannan gasa dai tana daga cikin manyan ayyukan da Jamaโatu Izalatil Bidโah Waโiqamatis Sunnah ke gudanarwa a kowace shekara, domin ฦarfafa ฦaunar Al-Qurโani, inganta karatu da haddar Al-Qurโani, tare da ฦarfafa matasa da ษalibai wajen riฦon Littafin Allah.
Ana gudanar da wannan Musabaฦa ne tun daga matakin Makaranta, Unguwa, Reshe, ฦaramar Hukuma, Zone, Jiha har zuwa matakin ฦasa baki ษaya.
๐จโโ๏ธ JERIN SUNAYEN SABABBIN ALฦALAN MUSABAฦAR
1. Hafiz Jameel Yahya, PhD
Chief Judge โ Babban Alฦali
2. Hafiz Abdulโazeez Shehu Gusau
Secretary โ Sakataren Alฦalai
3. Hafiz Yusuf Sulaiman
D8 โ Alฦali
4. Hafiz Abubakar Ahmad
Talata Mafara โ Alฦali
5. Ustaz Jameel Umar
Adabka โ Alฦali
6. Ustaz Marwanu Umar Gora
Time Keeper โ Mai Kula da Lokaci
Muna roฦon Allah Subhanahu wa Taโala Ya ba su ikon gudanar da Alฦalancin cikin adalci, gaskiya, amana da ฦwarewa, Ya sanya wannan Musabaฦa ta zama sanadin ฦara ษaukaka Al-Qurโani da masu karatunsa.
Allah Ya taimaki Alฦalan Musabaฦar, Ya albarkaci mahalarta, Ya kuma sanya wannan Musabaฦa ta yi nasara. ฤmฤซn.
ูููููู ุฑูุจูู ุฒูุฏูููู ุนูููู
ูุง
Fodio Online TV