18/12/2024
GIMBIYA RUDDA'U EPISODE 111
______________________________
Abdullahi dayyabu tamburawa
[email protected] 08069592193
sannan ta wani bangaren wasu suna murnar canja sarki shardas domin haraji yayi yawa, gashi Kuma ko Ina yankawa yakeyi Yana sayarwa, baruwan Sa da Nan kasuwa ce, ko makabarta, ko wajen bauta, shi kawai ya samu kudi,
Lokacin da gimbiya luzwatu tayi sati Akan karagar mulkin ta, bayan dare yayi sun tafi daki da gimbiya rudda'u, sai taga gimbiya rudda'u tana shirye shirye da Kuma gyare gyare, Kai da gani kasan Shirin tafiya ne, gimbiya luzwatu ta kalle ta cikin rashin fashimta sannan tace ya ke wannan jaruma shin ban fashimci Shirin ki ba, badai tafiya Zaki yi ba? Gimbiya rudda'u ta kalle ta fuskarta cike da fara'a sannan tace Daman ai alkawarin sati daya mukayi dake, Dan haka Babu fashi gobe zanyi harama domin akwai sauran aiki a gaba na, Amma ki sani da zarar na cika buri na Zan dawo wajen ki mu Kara sancewa tare na wani lokaci, Amma dai yanzu tabbas gobe da sassafe kafin kowa ya farka daga bacci mu munbar wannan nashiyar, gimbiya luzwatu ta dire kasa bisa guiwowin ta, tana Mai zubar da hawayen takaici sannan takalli gimbiya rudda'u tace lallai zanfi kowa jin Dadi idan burinki na mallakar duniya ya cika, Amma babban bakin ciki na ta yanda Zaki tafi ki barni tsawon wannan lokaci, gimbiya rudda'u ta bushe da Dari sannan tace lallai kin cika sokuwa Dan kawai Zan tafi k**e kuka, to kenan idan na mutu fa a wannan tafiyar? Da sauri gimbiya luzwatu ta mike sannan tace aikuwa tunda Kika kawo zancen mutuwa na rantse da girman rawanin Kaka na na sittin da shida sarki Arbas, wannan tafiyar da ni za ayi ta domin yanda Kika ceci rayuwata Nima yazama dole na taimaka wajen cikar burin ki, gimbiya rudda'u ta turbune fuska k**ar an Aiko mata da sakon mutuwa, sannan ta kalli luzwatu tace, shin kin rasa hankalin ki ne? Idan Kika bi ni waye zai kular Miki da kasar? Ki cire wannan zancen da ga ranki domin ma bazai yuwu ba........