02/08/2024
WANI DARASI AKAN KYAUTATAWA ALLAH ZATO
“Mahaifina (Imamul Sa’adiy, Allah ya ji ƙansa) yana saman masallaci yana gyara ɗaya daga cikin bututu (inda ruwa ke kwarara), kawai sai wani mutum mai wucewa yace masa, 'Gafarta Mallam, me ya sa kake wannan aikin?'
Sai mahaifina yace masa: "Ai gobe za mu fita Sallar Roƙon Ruwa ne."
- In ji Nūratu, ɗiyar Shaikh Abdurrahmān bn Nāsirus Sa'adiy, a shafinta na Twitter.
____
Allahu Akbar.
Malamai bayin Allah kenan. Ka ga Shaikh Abdurrahman Nasirus Sa’adiy kawai yana da yaƙinin Allah Yana karɓan addu'a ne. Kuma tunda dai ya san sun shirya fita Sallar Roƙon Ruwa gobe, to yana kyautata zaton Allah zai sauko da ruwan sama goben bayan sun roƙe Shi. Don haka yake shiryawa ruwan saman.
Allahu Akbar.
Cikin Hadithul Qudsiy, Allah Maɗaukakin Sarki yace:
أَنَا عِنْدَ ظَنِّ عَبْدِي بِي...
"Ina nan duk yadda bawana yake zato…”
Malamai masu sharhi s**a ce ma’anar wannan maganar ta Allah shine: Idan kana yiwa Allah zaton saukar maka da alheri, to hakan. Idan kuma kana maSa zaton saɓanin haka, to nan ma hakan! Don haka ya rage naka; kai ka san me kake ƙudurcewa gameda Ubangijinka.
Imamul Qurtubiy (Abul-Abbas kenan), cikin sharhinsa na Saheehu Muslim, mai suna “Al-Mufhimu limā Ashkala min Talkhīṣi Kitābi Muslimi” da ya zo sharhin hadisin nan sai yace:
“Ma’anar hadisin shine kayi zaton idan kayi addu'a, to Allah zai amsa. Kayi zaton idan ka tuba, to Allah zai karɓi tubanka. Kayi zaton idan kayi istighfari, to Allah zai gafarta maka. Kayi zaton idan kayi wata ibada bisa sharuɗɗanta, to Allah zai baka lada...."
Don haka ana son musulmi ya ringa kyautatawa Allah zato a cikin komai, cewa Allah zai iya mishi abu kaza. Kada ka munanawa Allah zato, kana cewa addu’ar dai muna yi ne kawai, amma da Allah zai amsa ai da tuntuni ya amsa. Ayya! Shi yasa har yanzu kuwa kuka ji shiru. Ai baku da yaƙinin Allah zai karɓa ne, shi Ya sa ya barku da rashin yaƙininku. Tunda kuna ganin Allah ba zai muku ba, to ku je a hakan- ba za a muku ba.
Amma ida