09/04/2025
Naga wani malami yana cewa muna rokon wanin Allah. Wannan maganar kawai siyasar addini ne. Mu ba mu taɓa cewa a roki wani da ba Allah ba; illa iyaka dai mun yarda ayyukan mu ba su kai mu roki Allah mu kaɗai ba tare da mun yi kamin kafa da amintaccen saba, wato Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam). Shi yasa zaka ji muna cewa: "Ya Allah, kabiya mana buƙatun mu albarkacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam)."
Sannan mun ga wata magana da wasu ke yadawa a ƙoƙarin su na fassara wannan aya: "Iyyaka na’budu wa iyyaka nasta’in," sai suke yi wa Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) rashin ɗa’a, suna cewa ko taimakon sa ne ba sa bukata. Ya kamata masu irin wannan su sani cewa za su iya rasa imanin su ba tare da sun sani ba. Domin kuwa ba ya halatta ka yi wa Manzon Allah rashin ɗa’a da sunan tabbatar da tauhidi. Saboda ai shi ɗin da kace ko nashi ɗin ne ba ka bukata, shine wanda Allah ya aiko da ita wannan ayar. Bayan ya zo maka da Islam, kuma ya yi gwagwarmaya domin tabbatar da addinin da shi da abokaninsa, har da wasu baffaninsa da sauran Sahabbai, sai da s**a taimake ka, s**a sadaukar da rayukan su, kafin ita wannan aya ta iso zuwa gare ka.
Ba mu taɓa jin inda ake irin wannan karatun ba na rashin ɗa’a ga Annabi, sai a arewacin Najeriya. Allah ya kyauta.
1. Tawassuli da neman albarka ta wurin Manzon Allah (SAW)
“Ya Allah, kabiya mana buƙatun mu albarkacin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam).” irin Wannan ana kiransa Tawassuli ne a ilimin addinin musulunci bawai wanin Allah ake roƙa ba,, kuma yana da asali daga Alƙur’ani da Hadisi.
Alƙur’ani – Surah Al-Mā'idah 5:35
Arabic:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah, ku nemi hanyar kusanci zuwa gare Shi, ku yi jihadi a tafarkinSa, domin ku rabauta.”
Sharhi:
Wasīlah a nan tana nufin hanyar kusanci ga Allah, kamar yadda malaman tafsiri s**a ce itace ayyukan alheri, addu'a da kuma ta wurin wasu bayi nagari irin su Annabi (SAW).
Alƙur’ani – Surah An-Nisā’ 4:64
Arabic:
وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذْ ظَّلَمُوا أَنْفُسَهُمْ جَاؤُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّابًا رَحِيمًا
“Da idan s**a yi wa kansu laifi, sun zo wurinka (Ya Muhammad), s**a nemi gafarar Allah, kai kuma ka roƙa musu, da sun sami Allah Mai karɓar tuba, Mai jin ƙai.”
Sharhi:
Wannan hujja ce cewa zuwa wurin Annabi (SAW) don roƙon gafara wajan Allah yana daga cikin hanyoyin samun rahamar ALLAH cikin sauki.
2. Girmamawa da biyayya ga Manzon Allah (SAW)
Alƙur’ani – Surah Al-Ḥujurāt 49:1-2
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تُقَدِّمُوا بَيْنَ يَدَيِ اللَّهِ وَرَسُولِهِ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Kada ku yi rashin ɗa'a ko azarɓaɓi a gaban Allah da ManzonSa, ku ji tsoron Allah. Lalle Allah Mai jin magana ne, Masani.”
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Kada ku ɗaga muryarku a bisa muryar Annabi…” rashin ɗa'a
Wannan aya tana tabbatar da cewa ladabi da biyayya ga Annabi (SAW) wajibi ne, kuma yana daga cikin alamun imanin mutum.
Hadisi Sahih al-Bukhari (Hadisi 15, littafin Imani)
لَا يُؤْمِنُ أَحَدُكُمْ حَتَّى أَكُونَ أَحَبَّ إِلَيْهِ مِنْ وَالِدِهِ وَوَلَدِهِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ
“Babu wanda zai cika da imani har sai na fi soyuwa a gare shi fiye da mahaifinsa, ɗansa da dukkan mutane.”
3. Hadarin raina matsayin Annabi da sunan Tauhidi
Alƙur’ani – Surah At-Tawbah 9:65-66
وَلَئِن سَأَلْتَهُمْ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلْعَبُ ۚ قُلْ أَبِاللَّهِ وَآيَاتِهِ وَرَسُولِهِ كُنتُمْ تَسْتَهْزِئُونَ
لَا تَعْتَذِرُوا قَدْ كَفَرْتُم بَعْدَ إِيمَانِكُمْ
“Idan ka tambaye su, sai su ce: ‘Ai muna wasa da raha ne.’ Ka ce: ‘Shin da Allah, da ayoyinSa, da ManzonSa kuke yin izgili?’ Kada ku ba da uzuri! Lalle kun kafirta bayan imanin ku.”
Wannan aya tana nuni da cewa raina Manzon Allah (SAW) da sunan wasa ko wani tsari yana iya sa mutum ya fita daga imani.
4. Matsayin Annabi matsayin rahama be ga dukkan duniya
Alƙur’ani – Surah Al-Anbiyā’ 21:107
Arabic:
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ
Fassarar Hausa:
“Ba mu aiko ka ba (Ya Muhammad), sai dai rahama ga dukan talikai.”
5. Shafa’ah Taimakon Annabi (SAW) a Lahira
Hadisi Tirmidhi (3613), Sahihul Jami’:
فَيَأْتُونَ إِلَىٰ مُحَمَّدٍ، فَيَقُولُ: أَنَا لَهَا، أَنَا لَهَا
“Sai mutane su je wurin Muhammad (SAW), sai ya ce: ‘Ni ne wanda zai iya yin ta, ni ne wanda zai yi ta (shafa’ah).’”
Tawassuli ta hanyar Annabi (SAW) ba haramun ba ne matuƙar an yi shi da sanin cewa Allah ne kaɗai Mai iko da amsa.
Girmamawa da biyayya ga Annabi (SAW) wajibi ne, kuma rashin yin hakan yana iya kai mutum ga barazanar rasa imani.
Annabi Muhammad (SAW) yana da matsayi na musamman wanda Allah da kansa ya girmama shi da shi.
Yakai ɗan uwa basai ka riƙa maimaita "Ko na Annabi ne baka buƙata ba" zaka tabbatar da Tauhidi domin kuwa furta irin wannan ka iya sakaka yin biyu babu.
Allah ya kare mu, Ya kare mana imanin mu albarkacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam