14/06/2025
Iyalai da Dangin Ƴan Tijjaniyya 12 Daga Kano da aka yi Garkuwa Dasu a Burkina Faso Sun Roƙi Tinubu da Ya kawo Musu Ɗauki.
Iyalai da dangin wasu mabiya darikar Tijjaniyya guda 12 daga Jihar Kano, waɗanda ake zargin an yi garkuwa da su watanni tara da su ka gabata a ƙasar Burkina Faso, sun sake roƙon Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf da su kawo musu ɗauki don ceto ƴan uwansu.
Iyalan waɗanda lamarin ya shafa sun kuma roƙi Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, da shugabannin darikar Tijjaniyya da su taimaka wajen kubutar da ‘yan uwansu.
Da ta ke magana da wakilin DAILY NIGERIAN a Kano, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, wacce ta bayyana sunanta da Amina, ta bayyana cewa tun da mijinta ya ɓace, tana cikin damuwa da ƙuncin rayuwa.
Amina, wacce ba ta so ta yi doguwar magana saboda har yanzu tana cikin firgici da tashin hankali, ta ce tana da fatan mijinta zai dawo ba da jimawa ba.
A cewarta, ita ce tana da yara uku, kuma rayuwa ta yi tsanani tun bayan bacewar mijinta domin tana fama da wahala wajen ciyar da kanta da ‘ya’yanta.
Shi ma Bashir Tijjani, ɗa ga ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, ya ce i sun kasance cikin fargaba da rashin tabbas tun da lamarin ya faru.
Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da s**a yi, ba su samu wani ci gaba mai amfani ba wajen ganin an sake su ko samun labarin inda suke.
Rahotanni sun bayayana cewa mutanen sun bar Zawiyyar Sheikh Malam Tijjani ‘Yan mota a ranar 7 ga Satumba, suna bi ta Jamhuriyar Nijar zuwa Burkina Faso a hanyarsu ta zuwa Senegal inda aka sace su.
Muna Roƙon Allah swt Yakuɓutar Dasu Cikin Aminci.AMIIN 😭😭🤲🤲
~ Daily Nigerian Hausa