HausaMedia

HausaMedia HausaMedia. Shafin dake ilmantarwa, faɗakarwa, nishaɗantarwa duka a cikin harshen Hausa domin bunƙasar da kuma cigaban harshen da al'ummar Hausawa gaba ɗaya

06/12/2023
05/12/2023
05/12/2023

FILIN TAMBAYA DA AMSA.
Wannan wani sabon shiri ne da zan dinga gabatarwa a wannan shafin domin amsawa mabiya wannan shafin amsoshin tambayoyin su da s**a shafi kimiyya da fasaha, yanar gizo, dandalin sada zumunta na Facebook, WhatsApp, Tiktok da sauransu.
Yadda tsarin ya ke shine idan kana da wata tambaya ka yi ta kaitsaye a comment section na wannan vedio, ko ka yi mini magana ta messenger tare da gabatar mini da tambayar ka, ni kuma idan na san wannan tambaya zan ba ka amsar ta ta hanyar yin posting a shafi na, ta yadda Sauran mutane za su amfana, idan ban sani ba, zan yi bincike ta hanyar tambayar wasu, sannan na gabatar da amsar da zarar na samu.
Zan dinga gabatar da wadannan amsoshi a cikin Vedio, ko kuma text.

Haka zalika, idan na bayar da amsa, kai kuma sai ka ga cewa da akwai kuskure a ciki, muna maraba da gyara a comment section din posting din da aka yi kuskuren
shin wacce gudummawa za Ka bayar don wannan tsari ya tabbata?
Ka yi tambayar Ka a comment section, Ka yi sharing domin wasu ma si shigo cikin tsarin, haka zalika Ka gayyato abokan ka domin su ma su amfana.

05/12/2023

NIKO TESLA DAN BAIWA A BANGAREN FASAHA.
A ranar 7, January 1948 mai shekaru 86, Nikola Tesla ya mutu a dakin hotel dinsa na New York city. Tesla ya mutu ne a matsayin talaka kuma shi kadai, yana daya daga cikin muhimman mutanen da tarihin su ba zai goge a duniyar fasaha.
Nikola Tesla mutum ne da a kullum burinsa samar da abin da zai taimaka rayuwar mutane, dan baiwa ne shi da ba'a kara yin k**ar sa ba, haka zalika mawaki ne shi akan abubuwan da s**a shafi kimiyya, masanin lissafi, kwararren mai hasashen gaba, masanin kimiyyar physics haka zalika masanin yaruka har guda takwas da ya ke magana da su tamkar yaren sa na farko yarensa na Serbia da Croatia, English, Czech, French, German, Hungarian da kuma Latin, haka zalika mutum ne da ya ke da kyakkyawan hadda, don ya kan iya karanto littafin kimiyya, formulas, da wakoki duk da ha haddace batare da littafin a hannunsa ba.
Kafin mutuwar sa ya kirkiri abubuwa da dama fiye da kowanne dan Adam da ya taba Rayuwa a duniyar, Tesla induction motor, Tesla rotary converter, Tesla Phase system of power transmission, transformer, Steam and gas turbine, Tesla coil wato fasahar da ta ke rarraba Wutar lantarki wirelessly, da wasun su da dama na daya daga cikin abubuwan da ya kirkira,a bangaren fasaha da sauran bangarorin kimiyya don kuwa a kowanne bangare za ka iya samun kirkire-kirkiren Nikola duka a kokarin sa na saukakewa mutane rayuwar su.
Kari akan haka, Tesla induction motor a wannan lokaci daya ne daga cikin abubuwan da 90% na rayuwar mu ta ta'allaqa da shi, inda mu ke amfani da shi a kusan komai da komai na rayuwar mu, duk wasu kamfanunuwan da suke samar da wutar lantarki su na amfani ne da fasahar Nikola Tesla da kuma Fasahar da ya samar na tsarin rarraba wutar lantarkin.
Burin sa da mafarkinsa har ya mutu shine mayar da duk wasu abubuwan da ya kirkira zuwa Abu guda daya, wanda ya Kira wannan aikin da World Wireless System a manufar sa ta samar da wutar lantarki a duka fadin duniya komai nisan wuri batare da amfani da wata waya ba k**ar yadda har yanzu a ke yi, wanda hakan zai saukakawa mutane wajen samun wutar lantarkin cikin sauki, kuma da matukar karfi.
Amma duk da haka an dauki lokaci mai tsayi bayan rayuwar sa kafin tasirinsa da aikace-aikacensa su watsu a cikin duniya kowa ya sani, a karni na ashirin har an fi girmama Einstein da karrama shi akan Nikola Tesla.A cikin littafin The 48 laws of power, marubucin ya rawaito yadda aka yaudare shi, inda da farko yana aiki a kamfanin Edison da ke kasar Serbia wato kasar sa ta haihuwa, sai manager na kamfanin ya tura shi babban reshen kamfanin domin ya yi wani aiki, tare da alkawarin cewa idan ya yi aikin za'a biya sa wasu miliyoyin kudade na dalar amurka tun a wancan lokacin, sai dai bayan ya kammala sai aka ki bashi, ba don Kudi ya ke yi ba, don haka ya dakatar da aiki a wurin kuma ya cigaba da ayyukan sa, bayan wannan lokaci ne kuma ya gano abin da yanzu ake kira Wutar lantarki, A shekarar 1893 kamfanin GE ya saci blueprints na aikin nasa wanda Edison yana cikin su. Abu mafi muhimmanci game da Tesla shine ya sadaukar da rayuwar sa ne gaba daya wajen kirkirar abubuwan da s**a wuce lissafowa, wanda a wannan lokaci wadannan abubuwan duka wani bangare ne na rayuwar mu a yanzu, da ace za'a dauke abubuwan da Nikola Tesla ya kirkira da za ka samu cewa sai komai ya dakata a wannan duniya, shine ya gano wutar lantarki da tsarin da ake rarraba ta har zuwa wannan lokaci, AC, injin tafiyar lokaci, Tesla wave, wireless connection da mu ke amfani da shi wajen kira, bayan wadannan ya kirkiri abubuwa da dama, sannan ya hasaso wasu abubuwa da dama da ya so kirkira, sai dai rashin kayan aiki, da kuma kudi ya sanya bai kai ga cimma nasara ba, wasu kuma su ka ce lokacin kimiyyar nan bai zo ba da Tesla ya samu nasara.
Wannan kadan ne a cikin tarihin Nikola Tesla, zan cigaba da kawo muku wasu muhimman bayanai game da Abubuwan da ya kirkira, maganganunsa, abun da aka ce a kansa da sauran su, kai dai ka yi following wannan shafin, kuma ka gayyato abokanka su yi following, haka zalika ka yi sharing don wasu su amfana!
.

03/12/2023

CZ BAI CE KA YI ABINDA YA YI BA, AMMA KA KOYI DAUKAR KASADA.

Rana irin ta yau, shekaru goma da s**a gabata CZ tsohon mai kula da kamfanin BINANCE ya dakatar da aikin sa, ya sayar da gidansa tare da sanya kudaden gaba daya a bitcoin, hakan ya biyo bayan dogon bincike da nazari akan menene bitcoin da kuma abinda zai zama zuwa gaba, bayan zuciyar sa ta gamsu da abinda ya gano a binciken da yayi, sai kawai ya dauki wannan kasada da a yau ta zama sanadiyar daukakar sa.
A wani posting da CZ ya yi a shafin sada zumunta na X yace ni ba cewa na ke ka yi abinda na yi ba, mutane da yawa suna tambayar cewa ta ya mutum zai dauki wannan kasadar? Ni bayan dakatar da aiki na zan iya kara samun wani aikin cikin sauki, yanayin daukar kasadar kowa yana da banbanci, ka koyi daukar kasada, da yadda ya k**ata ka bi.

Abin nufi a wannan magana shine daukar kasada ya danganta da yadda ka ke gani, shi ya dakatar da aikin sa ne saboda yana da tabbacin zai samu wani cikin sauki, to kai idan ka san ba za ka samu ba, ka da ka gwada, idan a bangaren investment ne a crypto ka sanya abinda idan ka rasa shi ba zai yi maka mummunan tasiri ba, ta yadda zai zamar maka Marsala's ba, ka da ka sake ka ari Kudi domin sanyawa a crypto ko shiga wata kasada, shin ba ka ji labarin abinda kamfanin Netflix ya yi ba, inda wani kamfani ya bashi wasu makudan kudade shi kuma ya yi kasadar sanye stock, wanda a karshe a ka kai ga yin asara.
Wannan shine Ake kira da risk management.

Ka yi following Shafin TechMagg idan ba ka yi, ka yi liking da comments da ra'ayinka game da Abubuwan da muke gabatar wa.

02/12/2023

NA'URAR TSARO TA AMAZON
Tun sha biyar, ga watan November Amazon ya fitar da fasahar Astro Robot dinsa, wanda ya ke bayar da tsaro, ga gida, kasuwanci ko Shago, kuma yana Kula da duk wani Abu da ke karuwa da nisan kafa 5000 daga kowanne bangare na wurin da aka sanya shi.
Tin a ranar larabar aka fara sayar da wannan sakago, da zai dinga bayar da tsaron, za ta iya aiki da kanta ko kuma ka yi amfani da controller din ta na Astro App.
Zuwa yanzu tuni an fara sayar da wannan fasaha, inda za ka siyeta a farashin $1599.99, sannan ka cigaba da bayar da jimilar 179$/month, idan ka so za ka iya subscribing ring version a matsayin 20/month wanda shi kuma zai dinga ajiye maka bayanan abubuwan da suke faruwa tsaron wata shida, da dai sauran su.
SHIN KUWA KA SAN DA AKWAI WANDA TUNI YA KIRKIRI MAKAMANCIYAR WANNAN FASAHA TUN DA DADEWA DAN NIGERIA.
Hadi Usman mazaunin garin gombe a yanzu wanda wasu ke yi wa lakabi da Nikola Teslan NIGERIA, tuni ya kirkiri mak**anciyar wannan fasaha, wacce za ta ba shi damad Kula da motsin komai, da hoton abinda ke bayan gidansa na tsawon fiye da kilometre daya, ba iya wannan ba, shi na shi zai dinga Kula da wurar lantarki da kuma wasu abubuwa da dama da za'a iya yi da fasahar?
Sai dai shi yace har yanzu Bai shirya fara sayar da fasahar ba, idan kuma zai sayar za ta iya wuce fasahar ASTRO ROBOT Kudi, tunda tana yin ayyuka da dama da Astro Robot din ba ya yi.
Idan kai ne za ka siyar da fasahar ne ko kuwa?
Ka yi sharing, tare da gayyato abokanka domin su amfana.

01/12/2023

AMAZON NA SHIRIN JERA KAFADA DA SAURAN MANYAN KAMFANUNUWAN FASAHA, A MATSAYINSA NA KAMFANI SAYE DA SAYARWA.

Bayan taron da kamfanin na Amazon ya gabatar a jiya, na kaddamar da sabon GenAI na Titan Image generator da sauran abubuwa da ya kaddamar kafin wannan lokaci, wani bakon al'amari yana shirin fara afkuwa, inda Amazon ke shirin jera kafada da sauran manyan kamfanunuwa irin su OpenAI, Google, Microsoft da sauran su da dama da s**a kutsa kai zuwa cikin fasahar.

24/11/2023

TARO AKAN LOW-CODE DEVELOPMENTS.

A yau kamfanin LINKSOFT za su yi taro a headquarters na kamfanin Microsoft da ke amurka, domin tattaunawa akan sabuwar fasahar No-coding ko low-code developments

24/11/2023

KAMFANIN OpenAI SUN SANAR DA SHIRIN KADDAMAR DA BUILDER TOOLS AKAN MANHAJAR CHATGPT.

kamfanin OpenAi sun fara shirin shiga duniyar No-coding developments inda za su ƙaddamar da wani dandamali da zai ba wa masu amfani da manhajar ChatGPT za su iya samar da software ta ChatBot, akan shafin, A yanzu haka ana kan gwajin wannan fasaha inda zaka iya ƙirƙirar ChatBot da aka riga aka tsara akan manhajar ka, ko application ko da ace ba ka iya wani programming language ba.
haka zalika, sun fitar da hanyoyin da masu amfani da ChatGPT builder tools za su samu kuɗi da aikin na su.

Ku cigaba da following TechMag domin samun bayanai masu muhimmanci akan fasahar zamani, ku kuma gayyaci abokan ku domin su yi following.

23/11/2023

LinkedIn

Zuwa wannan lokaci shafukan sada zumunta sun yawaita, waɗanda ake amfani da su domin yaɗa abubuwa daban-daban, dukansu da akwai abubuwa kala-kala da mai amfani da su ya ke iya amfana da su, k**ar nishaɗsntarwa, ilmi, kasuwancin yanar gizo, Aikin yi da sauransu da dama.

Mafi yawanci mutanen mu na arewa sun fi sanin social media k**ar irinsu facebook, WhatsApp, Twitter, Telegram, SnapChat, Instagram, Tiktok da sauransu, duka Waɗannan da akwai amfani masu yawa da mai amfani da su yake iya samu, ya danganta da yadda ya fahimci manufar shigarsa social media.
Sai dai bayan waɗancan da akwai social media masu yawa da suke da matuƙar muhimmanci ace kun san su, domin kuwa za su taimaka ƙwarai da gaske wajen kawo cigaba mai yawa a rayuwar ku.
LinkedIn ɗaya ne daga cikin waɗannan social media, an ƙaddamar da ita a shekarar 2003, inda a shekarar 2016 ta zama mallakin kamfanin Microsoft. Dandamalin yana bayar da dama wajen haɗa kan mutane, inda mai neman aiki zai iya zuwa yayi posting CV din sa a ciki, haka wanda ya ke so a yi masa wani aiki, wannan ya ke nuna maka cewa daga cikin manyan amfanin LinkedIn shine samar da aikin yi, sannan kana da damar gayyatar wani da ka san zai iya aikin domin yayi applying da zarar ka ga wani aiki da zai iya.
Izuwa wannan lokaci da akwai masu amfani da LinkedIn kimanin mutane biliyan ɗaya, a faɗin duniya, A shekarar 2021 kamfanin Microsoft ya dakatar da ƙasar China daga yin amfani da daandamalin.

Zaka iya fara amfani da LinkedIn ta hanyar shiga wannan mahaɗin LinkedIn.com, ka yi register, sannan ka binciki yadda zai iya taimaka domin samun abin da kake da bukata, bincike ya tabbata da cewa hatta upwork, freelancer, Fiverr da sauransu, ba su kai Linkedin saurin samun aiki da saukin amfani

23/11/2023

FLOWDIARY

Ƙiyasi ya tabbatar da cewa da akwai fiye da mutane miliyan hamsin a faɗin duniya da ke jin yaren hausa, kashi 70% mazauna arewacin ƙasar mu ne Nigeria, da aka haife su a matsayin hausawa, kuma s**a taso da shi a matsayin yarensu.
Masana sun tabbatar da cewa, koyon abu da yaren ka, shine hanya mafi dauƙi na fahimtarsa fiye da wani yaren, wannan dalili ne ma ya sa ƙasashen da s**a cigaba suke tilasta koyo da koyarwa s cikin yarensu.

Bisa ga wannan dalili Muhammad Auwal AhmadA ɗaya daga cikin matasan arewacin Nigeriya mai burin ganin Matasan mu sun kutsa cikin harkokin kimiyya da fasaha, da dabarun kasuwanci domin dogaro da kansu ya ƙaddamar da makarantar Flowdiary wacce take gabatar da darussa da dama a cikin harshen hausa, sauƙaƙƙen bayani da kuma farashi mai k**a da kyauta, ga duk wanda ya ke fa buƙata.
Kafin ƙaddamar da makarantar Mohidden ya rubuta littafai da dama, da s**a haɗar da Zo mu gina kamfani, Sirrikan sana'o'i chasa'in da tara, duka a cikin harshen hausa, domin sauƙaƙa fahimta, ya ke kuma sayar da su a farashi mai sauƙi, da bai wuce dubu ɗaya ba, k**ar dai darussan Flowdiary da ke ba wa mutum damar siyan kowanne course tun daga beginer har ka ƙware a kuɗin da bai wuce 5k ba.
Daga cikin darussan da ake gabatarwa a flowdiary da akwai:-
1- Android Developments: domin koyon yadda ake ƙirƙirar Android app kala daban-daban, tun daga matakin koyo har ka kware .
2- Web developments: Domin koyon yadda ake ƙirƙirar website daga natakin farko Front-end dev har zuwa backend, har kuma ka zama Full stack developer gaba ɗaya, duka a farashi mai sauƙi.
3-Social media management: Domin koyon yadda zaka kula da shafukan ka na sada zumunta, promoting dinsa da yadda ya k**ata ka dinga bi domin samun mabiya
4- Digital marketing and entrepreneurship: Hanyoyin da zaka koyi yadda zaka tallata hajarka, Tips da zaka bi, domin cin nasara a kasuwancin ka na yanar gizo.
5-Cyber security and ethical hacking: ɗaya ne daga cikin skills ɗin da suke matuƙar kawo kuɗi, kuma bayan haka za ka koyi yadda zaka bawa komai na ka na yanar gizo tsaro, duka a farashi mai sauƙi.
6- China mini importation: Za'a koyar da kai yadda za ka fara ɗauko kaya daga China batare da ka je ba, domin tafiyar da kasuwancinka cikin sauƙi.

Ba iya nan Flowdiary ta tsaya ba, da zarar ka kammala kowanne darasi zaka iya printing ɗin Certificate ɗin ka, wanda za ka iya amfani da shi wajen neman aiki, da sauran su. Haka zalika idan har ka ƙware Flowdiary zata haɗa ka da waɗanda za su ɗauke ka aiki da wannan skill ɗin naka, haka zalika zasu maka jagoranci zuwa ga duk wata hanyar samun kuɗi da Abin da ka koya, wannan kuma wani abu ne da ba zaks iya biya ba, sai dai kawai ka yi godiya garesu.
Domin fara amfani da Flowdiary zaka iya ziyartar website ɗin su Flowdiary.com.ng ko ka dauko application ɗinsu a Play store ta hanyar searching flowdiary ko ks bi wannan link ɗin
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.absoft.flowdiary

daga nan sai ka yi register ka fara ɗaukar darussa, ina mai tabbatar maka da cewa za ka gode mini daga baya..


Address

Tudun Wada

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HausaMedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HausaMedia:

Share