26/07/2025
***ABINDA MAGAJIN GARIN ZAZZAU ALH. NUHU BAMALLI YAFADA AKAN SARKIN ZAZZAU SHEHU IDRIS***
لبسم الله الرحمن الرحيم
Nagode da damanda kuka bani inyi tsokaci akan Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris,
Duk Dan Sarki beda buri da ya wuce ace ya zama Sarki, zakuyi mamaki idan nacemaku Ina cikin manyan "Yan takarar neman Sarkin Zazzau a shekarar 1975,
Ina Kaduna aka sanar dani Shehu Idris yazama Sarkin Zazzau, Ana fadamun nai dariya sosai a cikin raina sbd Shehu Idris yarone, Ni Kuma a lokacin nakai shekara 60 a duniya, nasan Shehu baze Kai ko inaba a mulkin Zazzau, Banyi tinanin za'a sama wani shugabanci nagariba a wurunsa sbd shi yarone,
Tun daga ranar, nasamashi ido, kunni Dan Inga kura-kuransa da gazawarsa a mulkin Zazzau, maganar Gaskiya Banjiba Kuma banga komiba na gazawarsa a kan shugabancin Zazzau,
Shekaru 24 da Shehu yayi Yana mulkin Zazzau be tafi a banzaba, Kaduna da Nigeria sun amfana dasu,
Sarkin Zazzau Shehu yanayin abinda ya dace, yanayin abindama ba'a zata zeyiba, na shugabanci nagari, Ya gyara Fadar Zazzau duk da cewa gwamnatin Jahar Kaduna ba wani kudi take waremasaba,
Abinda zanma Shehu shaida dashi, sune HAKURI, JURIYA, KAMUN KAI, DATTAKO da SAN ADDININ MUSULUNCI, Shehu ya taimaki Musulmi da Musulunci sosai, Shehu na San mutane ga kyauta, yanama masu kudi kyauta da talakawansa,
Shehu ya hada gidajan SARAUTAR ZAZZAU a wuri daya babu rigimar sarauta
Muna rokon Allah yayima Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris Jagora yayimasa Albarka yabashi Aljanna firdausi amin.
Kunji maganar gsky daga dattijon Arziki Dan yaro, jikan Darda'u Bijimin Saraki Jikan Sarki Musa, Mai Gaskiya da rukon Amana,
Muna rokon Allah ya jikan Mai girma MAGAJIN GARIN ZAZZAU ALH. (Dr) NUHU BAMALLI, SARKIN ZAZZAU ALH. (Dr) SHEHU IDRIS, IYAYANMU, KAKANNINMU DA AL'UMMAR MUSULMI BAKI DAYA AMIN.
Daga Baban Hajiya.
#26/07/2025.