
30/06/2025
Ƙissar Matar da Ta Kasance Kullum Cikin Karanta Ziyarar Ashura.
A wani gari da ke Najaf, an ce akwai wata mata mai tsarki, mai ibada, kuma mai ƙaunar Ahlul Bayt sosai. Wannan mata ta daɗe tana tsare karatun Ziyarar Ashura a kowace rana. Kullum bayan sallar asuba ko sallar la'asar, tana zaune a wajen da ta ke karanta ziyarar Ashura, tana kuka da hawaye.
Ta kasance mai bautar Allah, mai tawali’u, bata da wani matsayi a duniya, amma ruhinta ya kasance a Karbala kullum.
Bayan wasu shekaru, wannan mata ta rasu a cikin daren Juma’a. Mijinta ya bizne ta a makabarta kusa da Najaf, a makabartar da ba ta da wata kima sosai. Kamar dai wata makabartar talakawa.
Bayan wafatin ta da wasu kwanaki kaɗan, wani mutumin gari wanda shi ma yana bin tafarkin Ahlul Bayt, ya yi mafarki. A cikin mafarkin:
Ya ga ya na tafiya cikin makabartar da aka bizne wannan mata.
Sai ya ga wani haske mai ƙayatarwa da annuri yana fita daga kabarin wata gawa.
A lokacin ne ya ji wata murya mai ƙarfi tana cewa:
"Ni Imam Husaini (as) na zo na karɓe ruhinta da kaina. Kuma na albarkaci wannan Makabartar gaba ɗaya. Duk wanda aka bizne a nan daga yau, zai sami rahama da tsari – domin akwai masoyiyata a cikinta.”
Mutumin ya farka cikin tsananin mamaki da firgici. Sai da ya sake mafarkin har sau biyu. A rana ta uku, ya tashi da azama ya nufi mijin matar domin ya tambaye shi.
Lokacin da ya isa gidan mijin matar, ya zauna da shi, ya ce:
> “Don Allah, ka gaya min gaskiya. Matarka da ta rasu kwanakin baya — me take aikatawa? Me yasa na ga irin wannan haske a makabarta? (Sai ya bawa mijin labarin mafarkin da ya yi)"
Sai mijin ya fashe da kuka, ya ce:
“Wallahi, ita matata kullum karanta Ziyarar Ashura take. Ko ba lafiya, ko da yunwa — zata zauna ta karanta ziyarar. Tana yawan cewa, ‘Ina fata Imam Husaini zai karɓe ni da kansa’.”
Darussa Daga Wannan Ƙissa:
1. Ziyarar Ashura tana da matsayi mai girma wajen Allah da Imaman Ahlul Bayt.
2. Karanta ta da daidaito, da nutsuwa, da nufin goyon bayan gaskiya — yana iya zama sanadin ceto, har a lahira.
3. Mutumin da ya rayu da Ziyarar Ashura zai mutu da ita — kuma Imam Husaini (as) yana lura da irin waɗannan bayin Allah.
4. Wurin da masoyin Imam ya kwanta — na iya zama albarka ga wasu, sanadiyyar ƙaunarsa ga Husaini (AS) sai su sa mu rahama a gurin Allah.
Tambayar farko da karshe ita ce:
WANE DALILI NE ZAI HANA MU KARATUN ZIYARAR ASHURA?
Makarantar Al-Kauthar
4/Muharram/1447