09/06/2026
GAYYATAR WA'AZIN GORON SALLAH
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai
Shugaban Kungiyar JIBWIS na Jihar Taraba, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, tare da Shugaban Majalisar Malamai, Sheikh Ahmad Muhammad Boyi, da Shugaban Rundunar Ƴan Agaji na Jihar Taraba, Ustaz Muhammad Muhammad Usman, suna farin cikin gayyatar ɗaukacin al'ummar Musulmi zuwa Wa'azin Goron Sallah da za a gudanar a Garin Gunduma, Ƙaramar Hukumar Gassol.
Ranar Taro:
Asabar 27/12/1447H (13/06/2026)
Lahadi 28/12/1447H (14/06/2026)
Wurin Taro: Harabar Masallacin JIBWIS, Garin Gunduma, Ƙaramar Hukumar Gassol, Jihar Taraba.
Malamai Masu Wa'azi
Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Sheikh Ahmad Muhammad Boyi
Sheikh Imam Barkindo Jungudo
Sheikh Dr. Salisu Ishaq
Sheikh Ibrahim Umar Abokin Sarki Wukari
Sheikh Dr. Salihu Muhammad Barau
Sheikh Isa Shehu Rugga
Dr. Kabiru Adamu Lamido Gora
Dr. Aminu Sa'ad Na'allah
Dr. Thahir Haruna Zing
Dr. Abubakar Musa Jubu
Sheikh Abubakar Ali Maitakalma
Sheikh Murtal Bello Kunini
Tare da sauran manyan malamai masu daraja.
Masu Jan Baƙi (Alarammomi)
Alaramma Mustapha Isa
Alaramma Babangida Aliyu Mayo Gwai
Alaramma Mu'awiyah Al-Hassan
Alaramma Abdurrazak Boji Ibbi
Alaramma Dauda Alkasim Wukari
Alaramma Ansaruddeen Musa
Alaramma Malik Ibrahim Jalo
Alaramma Abdurrashid Adamu Lamido Girma
Tare da sauran Alarammomi masu girma.
Allah Ya ba mu ikon halarta, Ya sanya taron ya zama sanadin ƙaruwa cikin ilimi, shiriya da haɗin kai. Amin.
Sanarwa daga:
Barrister Jameel Auwal
Sakataren JIBWIS Taraba
Ta hannun Kwamitin JIBWIS Taraba Social Media.
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَجِيبُوا لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ﴾
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku amsa kiran Allah da ManzonSa idan ya kira ku zuwa ga abin da zai raya ku.” — Suratul Anfal: 24.