26/06/2025
Duk da hayaniyar da s**a yi da da’awarsu, an doke ƙungiyar Sahyoniyawa ƙwarai, kuma an murƙushe ta ƙarƙashin farmakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ina taya ku murna bisa nasarar ƙasarmu ta Iran a kan gwamnatin Amurka. Gwamnatin Amurka ta shiga wannan yaƙi kai tsaye ne saboda ta fahimci cewa idan ba ta shiga ba, to za a rusa gwamnatin Sahyoniyawa gaba ɗaya. Ta shiga ne don ceton wannan ƙungiya, amma ba ta cimma wani abu ba.
Gaskiyar cewa Jamhuriyar Musulunci tana da damar kai farmaki zuwa cibiyoyin Amurka a yankin, a duk lokacin da ta ga dama, abu ne mai matuƙar muhimmanci. Kuma wannan abu zai iya maimaituwa a nan gaba. Idan wani farmaki ya sake faruwa, to lallai makiyi zai biya farashi mai tsanani.
.