
24/02/2025
Assalamu Alaikum. Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai!
A jiya mun gudanar da zama na musamman tare da Sokoto State Social Media Organization (SOSMO) domin tattaunawa kan cigaban jam’iyya da kuma ƙara karfafa tafiyar matasan PDP. Zaman ya gudana ne a Ofishin PDP dake Emir Yahaya, Sokoto, karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar, Murtala Abubakar Naiya.
Mun tattauna hanyoyin da za su ƙarfafa haɗin kai da jajircewar matasa a tafiyar PDP, tare da fitar da dabarun da za su taimaka wajen bunƙasa jam’iyya da ƙara baiwa matasa damar taka rawa.
Haɗin kai da jajircewa su ne ginshikin ci gaban tafiyarmu. Mu ci gaba da aiki tukuru domin inganta makomar matasa da jam’iyyar PDP. -WK