Kanawa Post News

  • Home
  • Kanawa Post News

Kanawa Post News jaridar ta daya a arewa

Ƴansanda sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasaRundunar ’yansandan Jihar Ka...
05/10/2026

Ƴansanda sun gayyaci ɗan takarar NDC, Aminu Warkal kan zargin fito da bindiga a taron siyasa

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta gayyaci ɗan takarar jam’iyyar NDC, Hon. Aminu Abdullahi Warkal, domin yi masa tambayoyi kan zargin nuna bindiga a bainar jama’a.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakinta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026.

A cewar sanarwar, rundunar ta ci karo da wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yayin da take sintirin sa ido a yanar gizo, inda ake zargin an ga Warkal yana nuna wata bindiga da ake kyautata zaton bindigar Pump Action.

Rundunar ta ce idan aka tabbatar da zargin, hakan na iya zama keta dokar mallakar bindigogi ta Fi****ms Act, tare da haddasa tsoro da fargaba da kuma barazana ga zaman lafiyar jama’a.

Sanarwar ta ce an gayyaci Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, bisa umarnin Kwamishinan ’yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

A halin yanzu, ɗan takarar na NDC yana hannun sashen leƙen asiri na rundunar (SID), inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishinan ’yansandan ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin bin doka, daba ko nuna makamai da ka iya barazana ga zaman lafiyar jama’a ba, ba tare da la’akari da matsayin wanda abin ya shafa ba.

Ya kuma shawarci ’yan takara, magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da bin tanade-tanaden Dokar Zabe, Dokar Makamai da sauran dokokin ƙasa.

Rundunar ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano kafin, lokacin da kuma bayan kakar siyasa.

Ku fadawa Azzaluman Yansiyasa wadannan namu ne su basa cin mushe, ya rage wa sauran malamai idan sun gadama suyi koyi da...
04/10/2026

Ku fadawa Azzaluman Yansiyasa wadannan namu ne su basa cin mushe, ya rage wa sauran malamai idan sun gadama suyi koyi dasu ko kar suyi mudai munsan mutunci madara ne .......!

Yadda Tawagar Tripple R Ta Dira A Viila, Inda Ta Gana Da Mataimakin Shugaban Ƙasa Da Wasu Manyan Jiga-jigan Gwamnati Dom...
30/09/2026

Yadda Tawagar Tripple R Ta Dira A Viila, Inda Ta Gana Da Mataimakin Shugaban Ƙasa Da Wasu Manyan Jiga-jigan Gwamnati Domin Jaddada Goyon Bayansu Ga Shugaba Tinubu A Zaɓen 2027

Wace fata za ku yi musu?

30/09/2026
Cutar kwalara ta bulla a gidan yarin Kurmawa da ke KanoFursunoni biyu sun hadu da ajalinsu sakamakon barkewar cutar kwal...
27/09/2026

Cutar kwalara ta bulla a gidan yarin Kurmawa da ke Kano

Fursunoni biyu sun hadu da ajalinsu sakamakon barkewar cutar kwalara a gidan yari na Kurmawa da ke jihar Kano.

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar in ji jaridar Daily Trust. Kakakin hukumar, JN Osuji, ya ce gwajin dakin bincike da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba ya tabbatar da barkewar cutar.

Ya ce an fara gano cutar ne a ranar 17 ga Satumba, bayan wani fursuna ya fara nuna alamun cutar da s**a hada da amai da gudawa.

Ayi Sharing.... Abubuwa Da ’Yan Najeriya za su yi wajen kawar da Tinubu a 2027, shi ne tabbatar da sun jefa ƙuri’arsu. S...
26/09/2026

Ayi Sharing....

Abubuwa Da ’Yan Najeriya za su yi wajen kawar da Tinubu a 2027, shi ne tabbatar da sun jefa ƙuri’arsu. Sadaukar da lokutansu a ranar zabe, Su ƙara wayar da kan mutane domin guje wa zaɓen tumun dare.

A tabbatar an ƙirga ƙuri’arku a gaban idanunku. Ku tabbatar kun raka ƙuri’arku zuwa Coalition Centre kuma ku jira. Ku kuma tabbatar cewa wakilanku (Agents) ba su karɓi kuɗi sun ci amanarku ba.

Ku tsaya ku tabbatar sai an sanar da wanda ya yi nasara a Coalition Centre. Saboda duk wata masifa da magu-magu a Coalition Centre ake yi!! kuma ayi anfani da wayoyi, Camerori wajen Daukan duk abunda yake faruwa a wajen Yin zabe, wajen Tattara saka mako. da kuma zirga zirgar Miyagun mutane da ake basu kudi Don Zakuntar mutane...

Ku daure, ku jure, ku yi haƙuri. Za a yi yaƙi na gaske kafin a kawar da Tinubu. Ku tuna cewa fa.. Mulki a Hannunsa yake..... Dole sai anyi Taron Dangi....

TINUBU MUST GO........

Da dumi dumi: Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da tawagarsa, sun sauka a birnin Tehrain na Kasar Iran bayan shafe k...
26/09/2026

Da dumi dumi: Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da tawagarsa, sun sauka a birnin Tehrain na Kasar Iran bayan shafe kwanaki wajen Taron majalisar dinkin duniya United Nations General Assembly (UNGA) Karo na 81 Wanda ya gudana a farfajiyar majalisar dinkin duniya dake binin New York na kasar Amurka.

Sheikh prof Ibrahim ahmad makari ya halarci gagarumin taro da ministan kasar masar ya shirya don samar da cibiyoyin addi...
26/09/2026

Sheikh prof Ibrahim ahmad makari ya halarci gagarumin taro da ministan kasar masar ya shirya don samar da cibiyoyin addinin musulunci a Najeriya.

Muna ma fatan alkairi Allah ya kawo babban rabo Abdullahi Dan kaduna
26/09/2026

Muna ma fatan alkairi Allah ya kawo babban rabo
Abdullahi Dan kaduna

Address

Zoo Road

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kanawa Post News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kanawa Post News:

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed media company?

Share