23/08/2025
Me Ya Sa Littattafan Hausa S**a Gaza Gogayya Da Sauran Littattafai Na Harsunan Duniya?
Bayan wani gajeren rubutu da na yi a kan gasar gajerun labarai ta Bashir Othman Tofa da aka gudanar a Kano, na samu tambayoyi a kan yanayin da littattafan Hausa suke ciki, musamman na rashin ingantattun zarurrukan labarai da kyan bugu littattafai da rashin kyakkyawan tsarin kasuwancin su a Najeriya ta yadda za a yaɗa su a duniya?
Akwai waɗanda suke ganin su kansu marubutan ba su samu gudunmawar da ta dace ba, inda sabbin marubuta ma ba sa samun kulawa da gata na horon da ya kamata, kamar yadda takwarorinsu na Turanci suke samu.
Tabbas harshen Hausa yana da miliyoyin al'umma, wanda idan aka yi amfani da ilimi da tsare-tsare masu kyau, sannan aka zuba jari a cikin harkar za a samar da dubban makaranta. Duk kuwa da barazana da ake samu daga kafofin sadarwa na zamani da na'ura mai ƙwaƙwalwa.
A halin da ake ciki a yanzu babu wani ƙasaitatcen kamfani a duniya da yake buga littattafan Hausa don kasuwanci. Ko rawar da littattafan Hausa na wancan zamani s**a taka ta samo asali ne daga gudunmawar Turawan mulkin mallaka, da kamfanonin ɗab'i na wancan lokaci.
Na yarda marubutan wannan zamani tun daga 1980 zuwa yanzu sun bada babbar gudunmawa, musamman ta tabbatar da yin rubuce-rubuce cikin harshen Hausa da yaɗa shi a duniya. Amma rashin manyan kamfanonin ɗab'i da wallafe-wallafe ya taka rawa wajen halin da rubuce-rubucen Hausar ke ciki.
Kamfanoni irin su Macmillan da Heinemann da Longman ba sa kallon marubutan Hausa. Da yawansu suna ganin ba za su samu ribar da ta kamata ba. Waɗannan kamfanoni suna da ƙarfin jari da tsarin kasuwancin zamani, ta yadda za su tura littattafansu ko'ina a faɗin duniya.
Idan da irin waɗannan kamfanoni za su rungumi marubutan Hausa, sannan a samar da abin da wasu ke kuka a kai na rashin masu bada horo (mentorship), za a samu abin da ake so. Domin shi kamfani idan yana son aikin marubuci zai tabbatar sai ya kai mizani da ake so a duniya.
Za su iya cimma haka ta hanyar shirya taron sanin makamar aiki da haɗa marubuci da edita da zai dinga bibiyar aikinsa. Kamar yadda Rupert East ya yi wa Abubakar Imam a lokacin rubutun 'Magana Jari Ce' da wasu littattafai da ya rubuta.
Amma me ake tsammani idan marubuci shi ne zai kasance mai rubutawa, mai tace kayansa, sannan ya buga shi? Bayan ya bugawa shi ne zai yaɗa shi tare yin kasuwancin kayansa.
Sannan shi ne zai shirya tarurruka tsakaninsa da makaranta don taimakawa wajen isar da abin da littafin ya ƙunsa. Sannan uwa-uba yin sharhin littafin da gabatar da tattaunawa a rubuce ko a zahiri.
Duk waɗannan ba ƙananan ayyuka ba ne dake buƙatar kuɗi da ƙwarewa a kowanne ɓangaren da na zayyano. To amma marubutan Hausa sun dogara ne wajen buga littattafansu da kansu saboda rashin waɗannan kamfanoni.
Ko ƙananan kamfanonin buga litattafai da muke da su a Arewa, yawancinsu basu da banbanci da masu aikin buge-bugen takardu. Domin ba za su iya buga littafin marubuci a tsarin da aka san shi a duniya ba. Dole sai marubuci ya sauke musu kuɗin aikin littafin, sannan da zarar sun buga za su miƙo masa kayansa.
Shi kansa ingancin bugu da ƙa'idodi rubutu akwai rauni sosai a ciki. Wannan ya sa ko makarantun mu na gida ba sa karɓar irin waɗannan littattafai, bare kuma na ƙasashen ƙetare.
Idan ana son samun cigaba mai ɗorewa sai an yi aiki tuƙuru. Dole sai masu ruwa da tsaki a cikin harkar rubutun sun haɗa kan su. Duk wani da yake da hanya ta samar da jari ko kamfanonin da za su saka jari sai ya shigo.
Ta haka ne za a iya karkato da tunanin manyan kamfanonin ɗab'i zuwa littattafan Hausa, ko kuma a samar da wasu da za su saka jari don ciyar da hankar gaba.
Akwai kasuwa sosai a cikin rubuce-rubucen Hausa. Amma harkar tana buƙatar a inganta, abin da Bature yake kira 'packaging'. A wannan zamani da ake da kafofin sadarwar zamani, akwai hanyoyi sosai na yaɗawa da tallata littattafai.
© Zaharaddeen Ibrahim Abdullahi Kallah