"Cyber-Enhanced Digital Marketing for Building Trust in the Digital Age": In today's digital landscape, trust is paramount. At Cyber Cortex, we seamlessly bridge the realms of cybersecurity and digital marketing to ensure your online campaigns are not only highly effective but also fortified against potential threats. Our commitment to safeguarding your data and brand reputation means you can confidently engage with your audience, knowing that trust is built and maintained, even in the most challenging digital environments. Trust us to empower your brand with a secure and influential online presence.
Wallahi inajin takaicin hakan, mutum da kudinsa an rabashi dasu ba gaira ba ba dalili.
Kana amfani da banki gashi kana ajiyar kudi dole kayiwa kanka wa’azi kayi karatun ta nutsu. Mudai zamu cigaba dayin iyakacin abunda zamu iya don be kamata ace muyita shiru a kan irin wannan maganganun ba don ya kamata ace mutane su farga wajen kara sanin amfanin kare kai daga Yan Kutse da Yaudara (Hackers & Fraudsters) da kullum kara karuwa suke kuma tunaninsu kara fadada yake. Abunda ya faru dake wannan video hakan ba farau bane, kuma zakuji cewa wasu yan iska aka samu da suke cutar mutane su kwashe musu kudaden bankinsu ta amfani da layikan wayarsu (SIM Cards).
Yadda sukeyi shine sunada mutane da suke turawa su sato musu wayoyin mutane wajen amfani makami ko kuma dauketa batareda mutum ya sani ba, su wayar ba damuwarsu bace, harinsu kawai shine layin wayar (SIM Card) suna cireshi daga kan wayar su sanya a wata wayar, abunda suke farayi shine duba bankin dakake amfani dashi ta hanyar amfani da codes da akeda dasu na bankuna domin USSD transactions wajen gwada siyan katin waya, bayan sun samu ainahin bakin tareda account numbersa, a gefe sunada tarin layukan waya sababbi sai su canja lambar wayar bankin su saka tasu sannan a kwashe kaf kudaden da suke ciki ba imani, ba tareda sun san ta yadda aka samu wannan kudaden ba.
Kusan kullum muka samu dama muna fadawa mutane su dinga kula da layukan wayarsu:
- [x] Su saka musu PIN, domin idan aka saka PIN din nan babu wani wanda zai iya amfani da wannan layi a wata wayar.
- [x] Kada an sace maka waya ko ta fadi kayi shakulatin bangaro da yin swapping din layinka domin yin hakan shima nada hadari sosai.
Ina nan ina rubuta littafi sukutun guda akan irin hanyoyi da zaka bi wajen kare kanta (personal security dinka) daga irin wannan ayyuka na bata gari, zai samu fitowa da zarar ya kammala, In Sha Allahu.
Allah yakara karewa.
© Ibrahim Bashir Aliyu (#binbash)
- CEO, Cyber Cortex
Hackers suna amfani da hanyoyi da dama wajen hacking mutane, Social Engineering ya kasance daya daga cikin hanyoyin kuma hanyace mai hatsari.