Arewa A Yau

Arewa A Yau Muradin Arewacin Najeriya da jama’arta ne a gaba.
(1)

TIRKASHI: Matashi Ya Yi Kira da a Gyara Dokar Wa’adin ’Yan Majalisa a NajeriyaWani matashin ɗan siyasa kuma mai fafutuka...
24/05/2026

TIRKASHI: Matashi Ya Yi Kira da a Gyara Dokar Wa’adin ’Yan Majalisa a Najeriya

Wani matashin ɗan siyasa kuma mai fafutukar wayar da kan al’umma, Comr. Abubakar Imam, ya bayyana damuwarsa kan rashin iyaka ga wa’adin wasu ’yan majalisa a Najeriya.

A cewarsa, kasancewar babu takamaiman adadin wa’adin da ’yan Majalisar Tarayya — Sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai — za su yi, na haifar da matsala ga matasa da sauran al’umma, inda ya ce hakan na sa wasu kujeru su zama tamkar mallakar wasu mutane na dogon lokaci.

Ya bayyana cewa ana samun lokuta da wasu ’yan majalisa ke shafe shekaru 10 zuwa 20 a kan kujeru, lamarin da ke rage damar sababbin shugabanni, musamman matasa, shiga cikin tsarin mulki.

Comr. Abubakar Imam ya ƙara da cewa akwai buƙatar a duba wannan ɓangare na kundin tsarin mulkin Najeriya domin samar da gyara da zai ba kowa dama daidai.

Ya yi kira da a sake nazari kan dokokin domin samar da iyaka ga wa’adin irin waɗannan mukamai, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da kawo sauyi a tsari

YANZU-YANZU: Ɗan Takarar Sanata na ADC Ya Tsallake Rijiya da Baya a Abuja, Ya Musanta Hannu a Rikicin Zaɓen Fidda GwaniA...
24/05/2026

YANZU-YANZU: Ɗan Takarar Sanata na ADC Ya Tsallake Rijiya da Baya a Abuja, Ya Musanta Hannu a Rikicin Zaɓen Fidda Gwani

Ambasada Dakta Mubarak Ahmad Tijjani, ɗan takarar kujerar Sanata a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Babban Birnin Tarayya (FCT), ya musanta zarge-zargen da ke danganta shi da tada hankali yayin rikicin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin “ƙarya, yaudara, da siyasa.”

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Tijjani ya ƙaryata rahotannin da ke yawo ƙarƙashin taken “Allah-wadai da Tada Hankali a Sakatariyar ADC ta FCT,” yana mai jaddada cewa lamarin bai faru a kowace hukuma ta ADC ba.

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ofishin mazabar Sanata Ireti Kingibe da ke Gudu, Abuja, inda ya zargi mambobin Kwamitin Zaɓe na jam’iyyar da karkatar da muhimman kayan zaɓe maimakon kai su cibiyoyin zaɓe na unguwanni kamar yadda aka tsara.

Dan takarar ya ce dubban wakilai da magoya baya sun tsaya suna jira a wurare daban-daban ba tare da tantancewa ko kayan zaɓe ba, lamarin da ya haifar da gazawar gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani.

Tijjani ya kuma yi zargin cewa Shugaban Kwamitin Zaɓen ne ya gayyace shi zuwa wurin taron da ke Gudu domin abin da aka bayyana a matsayin “taron masu neman takara,” amma da isarsa ba a ba shi damar bayyana ra’ayinsa ba, sannan aka kai masa hari.

“Ban zo tare da ‘yan daba ba, kuma ban kai wa kowa hari ba,” in ji shi, yana mai cewa shi ne aka kai wa hari kuma daga baya aka kwantar da shi a asibiti sakamakon raunukan da ya samu.

Ya ce rahotannin likitoci daga Asibitin Cairo da sakamakon gwajin CT scan daga Everight Diagnostics sun tabbatar da cewa ya samu mummunan rauni a kai, raunuka a jiki, tangarɗar hankali, da kuma zubar jini a kwakwalwa.

A cewarsa, an riga an miƙa rahotannin likitocin ga shugabancin ADC na ƙasa da kuma hukumomin tsaro da s**a dace.

Tijjani ya zargi wasu da ake zargin suna da hannu wajen karkatar da kayan zaɓe da lalata tsarin zaɓen fidda gwani da ƙoƙarin yaudarar jama’a ta hanyar yaɗa bayanai a kafafen sada zumunta.

Ya buƙaci mambobin jam’iyyar da jama’a su mai da hankali kan tambayoyin da har yanzu ba a amsa ba game da lamarin, ciki har da dalilin da ya sa aka kai kayan zaɓe zuwa wani ofishi mai zaman kansa, dalilin da ya sa aka bar wakilai a cibiyoyin zaɓe, da kuma rashin wata hujja da ke nuna cewa ya kai wa wani hari.

Dan takarar na ADC ya ce yanzu haka lamarin yana gaban shugabancin jam’iyyar na ƙasa da hukumomin tsaro, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa “adalci, gaskiya, da riƙon amana za su yi nasara.”

Ya kuma buƙaci magoya bayansa da jama’a su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa ƙarya, kuma su goyi bayan dimokuraɗiyya.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Isma’il Ta Rasu Bayan Gajeriyar Rashin LafiyaAllah...
24/05/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Isma’il Ta Rasu Bayan Gajeriyar Rashin Lafiya

Allah Ya yi wa tsohuwar jarumar masana’antar Kannywood, Wasila Isma’il rasuwa bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa rasuwar tata ta girgiza masoya da abokan sana’arta a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, inda ake ci gaba da miƙa saƙonnin ta’aziyya tare da addu’o’in neman rahama gare ta.

Muna addu’ar Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarta. Idan tamu ta zo, Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

Ameen Ya Allah.

ABIN A YABA: Dr. Adam Kachallah Mohammed Ya Zama Garkuwar Matasan Najeriya Ta Fuskar Ilimi Da Dogaro Da KaiAna ci gaba d...
23/05/2026

ABIN A YABA: Dr. Adam Kachallah Mohammed Ya Zama Garkuwar Matasan Najeriya Ta Fuskar Ilimi Da Dogaro Da Kai

Ana ci gaba da yaba wa Dr. Adam Kachallah Mohammed bisa jajircewarsa da sadaukarwar da yake yi wajen tallafawa matasa tare da buɗe musu hanyoyin samun ci gaba a rayuwa.

Dr. Adam Kachallah Mohammed ya yi fice wajen bayar da shawarwari masu amfani, ƙarfafa guiwar matasa, da kuma samar da shirye-shiryen bunƙasa ilimi da ƙwarewa domin ganin matasa sun dogara da kansu tare da zama masu amfani ga al’umma.

Mutane da dama sun bayyana cewa irin gudummawar da yake bayarwa ta taimaka wa matasa da yawa wajen cimma burinsu, samun sana’o’i, da kuma inganta rayuwarsu ta hanyoyi daban-daban.

An bayyana ayyukansa a matsayin abin koyi ga masu ruwa da tsaki, musamman ganin yadda yake nuna kishin ci gaban matasa da al’umma baki ɗaya.

Masu bibiyar ayyukansa sun ce ƙoƙarin da yake yi na ƙarfafa matasa yana da matuƙar tasiri wajen gina al’umma mai inganci da kyakkyawar makoma ga matasa masu tasowa.

— Muhammad Adamu Aisami

DA DUMI-DUMI: Ta Tabbata Dai An Kwarfe Wani Matashi a Wajen Nan
22/05/2026

DA DUMI-DUMI: Ta Tabbata Dai An Kwarfe Wani Matashi a Wajen Nan

TIRKASHI: APC Ta Hana Kashim Musa Tumsah Tsallake Tantancewa, Ya Magantu Kan Makomar Tafiyarsa Ta SiyasaƊan takarar gwam...
21/05/2026

TIRKASHI: APC Ta Hana Kashim Musa Tumsah Tsallake Tantancewa, Ya Magantu Kan Makomar Tafiyarsa Ta Siyasa

Ɗan takarar gwamnan jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Kashim Musa Tumsah, MFR, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa bayan kwamitin tantancewar jam’iyyar ya hana shi tsallakewa a zaɓen fidda gwani.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Tumsah ya ce an sanar da shi cewa dalilin rashin tsallakewar tasa shi ne saboda yawancin waɗanda s**a tsayar da shi takara ba mambobi masu biyan kuɗin jam’iyyar APC ba ne.

Sai dai ya bayyana cewa bayan tattaunawa mai zurfi da iyalinsa, magoya bayansa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙasa, ya yanke shawarar karɓar hukuncin jam’iyyar cikin lumana da kyakkyawar niyya, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙaddarar Allah.

Tumsah ya kuma gode wa iyalinsa, magoya bayansa, mabiyansa da abokansa bisa goyon baya da jajircewar da s**a nuna a tsawon wannan tafiya ta siyasa domin tabbatar da adalci, bin doka da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyya a jihar Yobe.

Ya yi kira ga dukkan magoya bayansa da su kasance masu natsuwa, zaman lafiya da bin doka da oda, tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haddasa rarrabuwar kai ko kawo cikas ga nasarar jam’iyyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

“Mun nuna wa al’umma cewa ana iya gudanar da sabuwar siyasa mai fifita muradun jama’a,” in ji shi.

Tsohon ɗan takarar ya kuma bayyana cewa duk da tsaikon da tafiyarsa ta siyasa ta samu, hakan ba yana nufin ƙarshen tafiyar KMT ba ne, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukan tallafi da alheri a faɗin jihar Yobe domin amfanin al’umma.

Hakazalika, ya bukaci magoya bayansa da su mara wa shugaban ƙasa da kuma duk wanda ya zama ɗan takarar gwamnan APC a jihar Yobe baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.

TATTAUNAWA TA MUSAMMAN: “Lokaci Ya Yi da Matasan Najeriya Za Su Kwato Ƙasarsu” — Comrd. Yahaya M. Abdullahi, Shugaban Ma...
20/05/2026

TATTAUNAWA TA MUSAMMAN: “Lokaci Ya Yi da Matasan Najeriya Za Su Kwato Ƙasarsu” — Comrd. Yahaya M. Abdullahi, Shugaban Matasan AAC na Ƙasa

A wata tattaunawa ta musamman da jaridar Leadership Hausa ta yi da Shugaban Matasan Jam’iyyar African Action Congress (AAC) na ƙasa, Comrd. Yahaya M. Abdullahi, ya bayyana cewa lokaci ya yi da matasan Najeriya za su farka domin kwato makomar ƙasarsu ta hanyar shiga siyasa da kuma zaɓen shugabanni masu gaskiya da kishin talaka waɗanda ke da riƙon amana.

Kwamaret Yahaya ya ce jam’iyyar AAC ita ce jam’iyya ɗaya tilo mafi tsayawa kan gaskiya, adalci, da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, yana mai cewa dubban matasa daga sassa daban-daban na ƙasar nan na ci gaba da shiga jam’iyyar saboda sun gaji da tsohuwar siyasar yaudara da rashin adalci da tsoffin yan siyasar ƙasar s**a shafe tsawon shekaru suna gudanarwa, rayuwar talaka kullum yana cikin Ƙunci, tashin hankali, damuwa da sauransu kuma ba wanda ya isa ya fito yayi magana.

“Ina miƙa gaisuwa ta musamman ga dukkan matasan Najeriya da masu kishin ƙasa. Yau Najeriya na cikin mawuyacin hali saboda tsawon shekaru na gazawar shugabanci, rashin adalci, rashin aikin yi, da kuma danniyar talakawa. Amma muna da yakinin cewa matasa za su iya sauya wannan tarihi idan s**a haɗu s**a tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancinsu, tare da faɗa da dukkan wani tsari na zalunci.”

Ya kara da cewa yayin ziyarce-ziyarcen da yake kaiwa jihohi daban-daban, ya gana da matasa, masu fafutuka, da shugabannin al’umma da dama da suke nuna sha’awar tsayawa takara a karkashin tutar jam'iyyar AAC.

“Abin farin ciki ne ganin yadda matasa ke ƙara fahimtar cewa siyasa ba mallakin attajirai ko masu mulki kadai ba ce. Najeriya tamu ce baki daya, kuma lokaci ya yi da matasa za su shiga gaba wajen ƙwato makomar ƙasarsu,” in ji shi.

Ya ce: “Ina kira ga duk wani matashi ko ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da yake da burin kawo sauyi kada ya ji tsoro ko ya yi kasa a gwiwa. Ku zama dan gwagwarmayar kwato yancin Jama'a, ya shiga jam'iyyarmu ta AAC domin yaki da dukkan wani mummunan mulki a fadin Najeriya.

Comrd. Yahaya ya kuma bukaci matasan Najeriya su mara wa jagoran jam’iyyar AAC baya, wato Omoyele Sowore, yana mai cewa Sowore ya shafe shekaru yana gwagwarmayar kare hakkokin talakawa da yaki da zalunci ba tare da tsoro ba.

A cewarsa: “Matasan Najeriya dole su fahimci cewa idan suna son ‘yanci na gaskiya, shugabanci nagari, da kasar da za ta ba su dama, dole su fito su yi fada ta hanyar dimokuradiyya. Omoyele Sowore ya nuna jarumta da sadaukarwa wajen yaki da cin hanci, rashin adalci, da danniyar gwamnati. Lokaci ya yi da matasa za su hada kai su zabi shugabanni masu gaskiya maimakon waɗanda s**a jefa kasar nan cikin matsala.”

Ya kara da cewa AAC ba jam’iyyar siyasa ce ta anfani kawai ba, illa wata tafiya ce ta neman ‘yanci da adalci ga talakawan Najeriya.

“Sai mun haɗu tare ne za mu iya gina Najeriya mai adalci, inda matasa za su samu aiki, talaka zai samu kariya, kuma gwamnati za ta yi aiki domin jama’a ba domin masu karfi ba,” in ji shi.

Babban abunda ya fi tayar da hankalinmu a Arewacin Najeriya yanzu shine matsalar tsaro, wannan abu ne da ya addabi jama'ar Najeriya, musamman Arewacin Najeriya, a kwanakin baya Sowore yayi wata magana inda yake cewa a cikin mako biyu zai magance matsalar tsaro idan ya zama shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa masu kawo matsalar tsaro suna Abuja, su za'a magance idan aka magance su to an kammala da matsalar tsaro, amma matukar suna yawo to lallai matsalar zai ci gaba da hauhawa a fadin Najeriya.”

“Babban Burinmu a yau shine mu tabbatar da mun magance dukkan wani damuwa da zai addabi talaka a fadin Najeriya, abu na farko shine matsalar tsaro, Arewacin Najeriya da noma kawai zamu iya rike kanmu, Kasar 'Ukraine' bata wuce jihohi uku a fadin Najeriya ba amma abun kunya har lokacin da take yaƙi sai da ta bama Najeriya tallafin abinci wannan babbar abun kunya ne, a ƙasar da muke da komai na arziki tun daga filin noma har arzikin karkashin kasa duk Allah ya bamu amma saboda shugabannin Najeriya damuwarsu kawai su azurta kansu, kullum muna cikin fama da talauci.

Haka idan muka koma bangaren tattalin arzikin kasa, muna da masu Ilimin da zasu cire wa Najeriya kitse a cikin wuta, a kullum abunda Omoyele Sowore yake cewa shine zalunci ne ya dabaibaye Najeriya ba rashin abunda ya kamata ba, muna da wadanda zasu yi ayyuka a ƙasar nan tuƙuru domin ci gaban ƙasar, amma abun kunya har yanzu mafi ƙarancin albashi a Najeriya bai wuce dubu dari ba, wasu kasashen da ba'a aiki kamar Najeriya albashin ya zarce na Najeriya kusan kaso uku, kullum ma'aikata ke wahala a Najeriya.

Ya yi wa dukkan masu neman takara da magoya bayan jam’iyyar fatan alheri tare da jaddada cewa gwagwarmayar ceto Najeriya tana bukatar hadin kan matasa daga kowane bangare na kasa.

TIRKASHI: Kashim Musa Tumsah Ya Karyata Jita-Jitar Janye Takara, Ya Ce Har Yanzu Yana Neman Kujerar Gwamnan Yobe a APCƊa...
20/05/2026

TIRKASHI: Kashim Musa Tumsah Ya Karyata Jita-Jitar Janye Takara, Ya Ce Har Yanzu Yana Neman Kujerar Gwamnan Yobe a APC

Ɗan takarar gwamnan Jihar Yobe a jam’iyyar APC, Kashim Musa Tumsah, ya fito karara domin musanta jita-jitar da ke yawo cewa ya janye daga takarar gwamnan jihar.

A cikin wata sanarwa da Sashen Yaɗa Labarai na Yaƙin Neman Zaɓensa ya fitar, an bayyana cewa rahotannin da ke cewa Tumsah ya fice daga fafatawar neman tikitin APC “ƙarya ne tsagwaronta” kuma an ƙirƙire su ne domin ruɗar da jama’a.

Sanarwar ta tabbatar da cewa Kashim Musa Tumsah har yanzu cikakken ɗan takara ne, kuma yana nan daram wajen ci gaba da fafutukar neman tikitin gwamnan APC a Jihar Yobe.

Ta ce shigar Tumsah takarar ta samo asali ne daga aniyarsa ta ganin an mutunta doka, gaskiya, adalci da kuma bin ƙa’idojin Dokar Zaɓe ta 2026 da tsarin zaɓen kai tsaye na jam’iyyar APC.

“Halin da ake ciki ba zai sa ya ja da baya ba, domin yana nan tsaye kan tabbatar da gaskiya da kare dimokiraɗiyya a cikin jam’iyya,” in ji sanarwar.

Haka kuma, Tumsah ya yi kira ga magoya bayansa da al’ummar jihar da su ci gaba da kasancewa masu haƙuri, bin doka da kuma nuna biyayya ga jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu yana da ƙwarin guiwar samun nasara idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.

Ya kuma bukaci INEC, jami’an APC da hukumomin tsaro da su tabbatar da an gudanar da zaɓen fidda gwani cikin sahihanci, gaskiya da riƙon amana.

A ƙarshe, Tumsah ya bayyana cikakken fatansa cewa APC za ta fito da haɗin kai da ƙarfi domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 idan aka bai wa kowa dama cikin adalci.

DA DUMI-DUMI: Dan Takarar Majalisar Tarayya na NDC, Ibrahim Bello Yobe, Ya Shirya Ganawa Ta Musamman da Shugabannin Jam’...
19/05/2026

DA DUMI-DUMI: Dan Takarar Majalisar Tarayya na NDC, Ibrahim Bello Yobe, Ya Shirya Ganawa Ta Musamman da Shugabannin Jam’iyya a Bade da Jakusko

Dan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Bade/Jakusko karkashin jam’iyyar NDC, Ibrahim Bello Yobe, ya sanar da shirinsa na gudanar da wata muhimmiyar ganawa ta musamman da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin Bade da Jakusko na jihar Yobe.

A cewar sanarwar da ya fitar, za a gudanar da taron ne a ranakun Asabar 23 ga watan Mayu, 2026 da kuma Lahadi 24 ga watan Mayu, 2026.

Ibrahim Bello Yobe ya bayyana cewa taron na da matukar muhimmanci wajen kara hada kan ‘ya’yan jam’iyya, karfafa tuntuba da kyakkyawar fahimta tsakanin shugabanni da mambobi, domin cimma manufofin siyasa na bai daya a mazabar Bade/Jakusko.

Ya kuma yi kira ga daukacin shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da sauran mambobin NDC a yankunan Bade da Jakusko da su fito domin halartar wannan gagarumin zama tare da bayar da gudunmawar su wajen cigaban jam’iyyar.

“Hadin kai da tuntuba su ne ginshikin nasara a siyasa, saboda haka muna sa ran samun cikakken hadin kai daga kowa,” in ji shi.

Sanarwar ta samu karbuwa daga magoya bayan jam’iyyar, inda da dama ke ganin wannan yunkuri wata babbar alama ce ta kokarin hada kan jam’iyya da kuma shirin tunkarar zabukan gaba cikin tsari da hadin kai.

YANZU-YANZU: Gashua Ta Cika Maƙil Yayin Da Dubban Jama’a S**a Fito Tarbar Kashim Musa Tumsah Cikin GirmamawaAn shaida ga...
19/05/2026

YANZU-YANZU: Gashua Ta Cika Maƙil Yayin Da Dubban Jama’a S**a Fito Tarbar Kashim Musa Tumsah Cikin Girmamawa

An shaida gagarumar tarba da al’ummar garin Gashua s**a yi wa Kashim Musa Tumsah MFR yayin ziyarar girmamawa da ya kai yankin, inda dubban jama’a s**a fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna masa ƙauna da goyon baya.

Tun daga manyan titunan garin har zuwa wuraren taro, matasa da mata da dattawa sun cika ko’ina cikin farin ciki, suna rera wakoki da kade-kade na maraba tare da daga tutoci da allunan nuna jin daɗinsu bisa zuwansa.

Taron ya kasance cikin yanayi na annashuwa da girmamawa, yayin da jama’a s**a bayyana Kashim Musa Tumsah a matsayin jagora mai kishin talakawa, wanda ke da hangen nesa da burin kawo ci gaba mai amfani ga al’umma.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa ziyarar tasa ta kara musu kwarin gwiwa da fata, musamman ganin yadda yake kokarin kusantar jama’a domin sauraron ra’ayoyinsu da fahimtar matsalolin da suke fuskanta.

Ziyarar ta kuma kara tabbatar da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Kashim Musa Tumsah da al’ummar yankin, lamarin da ya sa tarbar ta kasance daya daga cikin mafi girma da aka gani a yankin cikin ‘yan kwanakin nan.

ALLAHU AKBAR: Ƴar Kabilar Igbo Musulma Ta Farko a Garin Achi Jihar Enugu Ta Haddace Alƙur’aniAn bayyana farin ciki da al...
19/05/2026

ALLAHU AKBAR: Ƴar Kabilar Igbo Musulma Ta Farko a Garin Achi Jihar Enugu Ta Haddace Alƙur’ani

An bayyana farin ciki da alfahari bayan wata ƙaramar yarinya mai suna Ikezu Chizaram Aisha ta zama mace ta farko da ta fara haddace Alƙur’ani mai girma a garin Achi da ke ƙaramar hukumar Oji River a jihar Enugu.

Rahotanni sun bayyana cewa, Aisha ita ce ɗiya Musulma ta farko da aka haifa a garin, kuma yanzu haka tana daga cikin yara masu ƙoƙarin haddar Alƙur’ani tare da sadaukar da lokacinta wajen koyon kalaman Allah.

Al’ummar Musulmi sun yi addu’ar Allah Ya ƙara yawaita irinta, Ya sanya ta zama abin alfahari ga addinin Musulunci da al’umma baki ɗaya.

Address

Kano

Telephone

+2349124943407

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa A Yau:

Share