07/11/2025
Majalisar Malamai ta Kontagora ta shirya taron addu’a kan hare-haren ’yan bindiga karo na biyu.
Kwamitin Majalisar Malamai na Masarautar Kontagora na gayyatar al’umma zuwa babban taron addu’a domin neman kawo ƙarshen matsalar ’yan bindiga da ta addabi yankin arewacin Jihar Neja.
A cewar sanarwar da kwamitin ya fitar, taron zai gudana ne a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025, da misalin karfe 8 na safe a babban masallacin idi dake cikin garin Kontagora.
Majalisar ta bukaci al’umma da su halarci taron da cikakken haɗin kai da niyyar neman rahamar Allah domin samun zaman lafiya da tsaro a yankin.