
03/07/2025
TUNATARWA
Azumin Tasu’a da Ashura
Kungiyar Fityanul Islam of Nigeria tana tunatar da daukacin al’ummar Musulmi a fadin duniya, musamman ‘yan agaji da mambobin Kungiyar Fityanul Islam, muhimmancin yin azumin Tasu’a (Juma’a, 4 July, 2025 – 9 Muharram 1447H) da Ashura (Asabar, 5 July, 2025 – 10 Muharram 1447H).
Manzon Allah Saw ya azumci Ashura kuma ya umarci Musulmi su azumce ta. Daga baya ya ce:
“Idan na rayu zuwa shekara mai zuwa, zan azumci ranar tara 9 (Tasu’a) ma.”(Muslim
Saboda haka Sunnah ce Musulmi su azumci Tasu’a da Ashura, ko ku azumci Ashura kawai idan ba za ku iya duka biu ba.
Muna kira ga Musulmi su yi kokari su azumci wadannan ranaku, tare da addu’a domin zaman lafiya da cigaban Musulunci.
Allah Ya karbi ibadunmu. Amin.
✍️ Rabiu Babayo