Beli Media Hausa

  • Home
  • Beli Media Hausa

Beli Media Hausa Madogarar labaran ku na lamba 1 akan sabbin abubuwan da ke faruwa a cikin gida da waje. Beli Media Hausa

Muna kawo muku sabbin labarai kan: Siyasa, Kasuwanci, Wasanni, Ilimi, Lafiya, Nishaɗi da dai sauransu.

19/10/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard!

Mamudu Isa, Hadiza A Adam

YANZU-YANZU: Dangote ya rage farashin Naira 30 akan kowace lita ta man fetur din kamfanin shi daga Naira 850 zuwa Naira ...
12/08/2025

YANZU-YANZU: Dangote ya rage farashin Naira 30 akan kowace lita ta man fetur din kamfanin shi daga Naira 850 zuwa Naira 820.

SHUGABA BOLA AHMED TINUBU YA AIKE DA SAKON TA’AZIYYA GA SHUGABA JOHN MAHAMA NA GHANA....Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aik...
06/08/2025

SHUGABA BOLA AHMED TINUBU YA AIKE DA SAKON TA’AZIYYA GA SHUGABA JOHN MAHAMA NA GHANA....

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon ta’aziyya ga Shugaba John Mahama, gwamnati da mutanen Ghana bayan hadarin helikwata da ya yi sanadiyar mutuwar Ministan Tsaro Edward Omane Boamah, Ministan Muhalli Ibrahim Murtala Muhammed, da sauran mutane shida.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa Shugaba Mahama da duk ‘yan Ghana cewa gwamnati da jama’ar Najeriya na tare da su a wannan mawuyacin lokaci na babban rashi da akayi a Ghana..

Shugaban ya yi kira ga al’ummar Ghana da iyalan mamatan da abokan su da su samu kwanciyar hankali da sanin cewa masoyan nasu sun rasu suna hidima ga kasar su cikin kishin kasa.

Ya yi addu’a Allah ya basu karfin juriya bisa wannan rashi da akayi...

Bayo Onanuga
Mataimaki na Musamman ga Shugaba kasa
6 ga Agusta, 2025.

SHUGABA TINUBU YA TAYA DALIBAI UKU NA NAJERIYA MURNAR SAMUN NASARA A GASAR DUNIYAShugaba Bola Tinubu ya taya Nafisa Abdu...
06/08/2025

SHUGABA TINUBU YA TAYA DALIBAI UKU NA NAJERIYA MURNAR SAMUN NASARA A GASAR DUNIYA

Shugaba Bola Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu, Rukayya Muhammad Fema, da Hadiza Kashim Kalli murna bisa nasararsu ta zama zakarun duniya a fagen kwarewar harshen Turanci da kuma muhawara a gasar TeenEagle ta duniya ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan Birtaniya...

Nafisa mai shekaru goma sha bakwai ta samu matsayi na farko a fagen kwarewar harshen Turanci, Rukayya mai shekaru goma sha biyar ta yi fice a fagen muhawara turanci, yayin da Hadiza ta samu kyautar hazaka ta musamman (medal)

Shugaba Tinubu ya yaba wa waɗannan matasan 'yan Najeriya da wannan gagarumar nasara, kuma ya tabbatar da cewa makomar Nigeria zata kasance mai haske matuƙa tare da irin waɗannan ƙwararrun matasan.

Shugaban ya kuma yaba wa cibiyoyin ilimi yana mai cewa waɗannan nasarori shaida ne ga ƙima da ƙarfin tsarin ilimin Najeriya wajen haɓaka hazikan mutane.

Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa ilimi ginshiƙi ne na ci gaban ƙasa; don haka gwamnati ta himmatu wajen saka jari sosai a fannin da kuma kawar da cikas na kuɗi ga matasan ƙasa masu ƙaramin ƙarfin shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta hanyar Asusun Lamuni na Ilimin Najeriya (NELFUND).

Shugaba ya ƙarfafa wa Nafisa, Rukayya da Hadiza guiwa su ci gaba da jajircewa a karatunsu da fatan nasarori masu ɗorewa.

Bayo Onanuga

Maibada Shawara na Musamman ga Shugaba

6 ga Agusta, 2025

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Beli Media Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Beli Media Hausa:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share