31/07/2025
*A yau ne masu bautar ƙasa (NYSC) s**a ziyarce mu domin karfafa gwiwa da ba da gudunmawa wajen ci gaban harkokin kasuwancinmu.*
Sun gabatar da shirin *Google My Business*, wanda ke taimakawa 'yan kasuwa wajen samun bayyana da bunkasa a intanet. Wannan mataki yana da muhimmanci ga 'yan kasuwa, musamman matasa, domin fadada damar samun abokan ciniki da kuma inganta harkokin su.
Muna matukar godiya ga wannan ziyara mai albarka da kuma irin wannan haɗin kai. Wannan hadin gwiwa zai taimaka wajen inganta sana'o'inmu da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankinmu.