04/07/2025
DA ƊUMI-ƊUMI:
Jami’an Tsaro Sun Kashe 'Yan Ta’adda Sama da 500 a Jihar Zamfara, Sun Kwato Mak**ai da Mashina Fiye da 200
A wani samame da aka kai a daren jiya Alhamis, jami’an tsaron Najeriya sun hallaka fiye da ’yan ta’adda 500 tare da k**a wasu da rai a dazukan Anka, Bukkuyum, da Gummi da ke jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin Najeriya ne s**a jagoranci wannan luguden, inda s**a kwato mak**ai da dama da kuma babura fiye da 200 da 'yan bindigar ke amfani da su wajen kai hare-hare kan al'umma marasa laifi.
An bayyana cewa wannan babban samame ne da sojoji s**a kai cikin tsari da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, kuma ya yi matukar tasiri wajen rage karfin 'yan bindigar da ke addabar yankin.
Wannan ci gaba na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ta kiraye-kirayen da a karfafa tsaro a yankin Arewa maso Yamma da Tsakiya.
📰 Asalin rahoto: Rana24