Al-kalam TV

Al-kalam TV Yun kurin kawo chigaba da wayar da kan Al'umma Shine muradin mu

29/10/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Moussa Abou Niger, Abubakar Lawan, Abdullahi Idris, Saddeeq S Saddeeq Agalawa, Zahraddeen Uba Muhd, Abubakar Yusuf, Abdullahi Adamu, Sunusi Ahmad, Lawal Ado Ibrahim, Musa Isa, Shehu Abdulhamid, Aliyu Zakariyya, Auwal Yau, Yunusa Nasiru, Jibril Musa Fta, Ali Hamisu, Abba Kabir Lawan, Dan Taro Copied

."KASUWAR MAKARFI A YAU 18/09/20241. Masara (Maize) fara Mai Aure  N75.000 har Zuwa N80.000 2.  Masara Sabuwa N47.000 ha...
18/09/2024

."KASUWAR MAKARFI A YAU 18/09/2024

1. Masara (Maize) fara Mai Aure N75.000 har Zuwa N80.000

2. Masara Sabuwa N47.000 har Zuwa N53.000

3. Dawa (G/corn) N80.000.. har Zuwa N85.000

4. Dauro N104.000, Harma N106.000

5. Gero (millet) N70.000.

6. Wake fari Sabo (White beans) N150.000
Tsohon Wake N204.000

7. Wake suya (Suyer beans) N100.000 har Zuwa N105.000

8. Shinkafa (Rice) Sabuwa N53.000. Har N55.000

9.Shinkafa Tsohuwa N63.000 har zuwa N65.000

10. Kalwa Babban buhu N95.000

11. Kalwa Karamin Buhu N75.000

12. Barkono (pepper)N210.000, har zuwa
N220.000

13. Rogo N71000. Har Zuwa N72.000

14. Soborodo N24000.

15. Tomato bushashshe Kauda N190,000 har zuwa N210.000

16. Garin kwaki N60.000

17. Garin kwaki N45.000.

18. Gyada Sabuwa N160.000

20. Gyada Tsohuwa N180.000

21. Suga Mazarkwaila Feda, N42.000
Suga Kwafzo N65.000
Suga Ƴar Kwarya N35.000
Suga Kyauje N12.000

22. Shinkafa tsaba ta tuwo N153.000

23. Tattasai Tashi N150.000 zuwa N160.000

24. Shambo Bushashshe N130.000 zuwa N140.000

25. Shambo Ɗanye N25.000 zuwa N30.000

Etc Jimbo fas agro, mai nauyin 100, lg.

Labaran rana daya gabata daga tashar hausa ta dw Shirin Rana na 18/09/2024🎤😊Sulaiman Babayo ne zai gabatar da shirinmu n...
18/09/2024

Labaran rana daya gabata daga tashar hausa ta dw Shirin Rana na 18/09/2024🎤

😊Sulaiman Babayo ne zai gabatar da shirinmu na rana da misalin karfe biyu agogon Najeriya da Nijar, karfe 1 agogon GMT da Ghana.

👍Ga jerin rahotanni da za mu kawo muku inda za ku iya sauraro kai tsaye a babban shafinmu na intanet a nan👉 🔗 https://p.dw.com/p/15bt5

👉 Ma'aikatun tsaron kasashen Amurka da Jamhuriyar Nijar sun sanar da kammala janye sojojin Amurka da kayan yakinsu gaba daya daga Nijar.

👉 A Najeriya daya daga cikin manyan tsoffin sojojin kasar Janar Theophilus Danjuma ya kalubalanci manyan sojojin kasar su kawo karshen kashe-kashen da ake yi.

👉 Al´ummar Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya na cikin fargabar bullar cututtuka da ke da nasaba da gurbacewar muhalli bayan ambaliya.

👉 Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi tir da cunkoson gidajen yari a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

👂✍Za ku iya sauraron shirin da kuma bayyana ra'ayoyinku a nan shafinmu na Facebook.
(DW Hausa lifting)

Sai mun ji daga gareku👂
https://www.facebook.com/100064759114217/posts/952541163581179/?mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

18/09/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Bello Danlami, Usman Bale, Salihu Sani, Yunusa Mansur Getso, Habibu Siniya, Garba Sadiq, Yahaya Naannabi, Mohammed Lawal Zamtex Rijau, Abubakar Sadeeq

MU SHAKATA DA WANNAN~LABARIN SHEHU JAHA~ JAKIN DINARI DAYAWata rana jakin Shehu Jaha ya bata, aka yi neman duniyar amma ...
17/09/2024

MU SHAKATA DA WANNAN

~LABARIN SHEHU JAHA~

JAKIN DINARI DAYA

Wata rana jakin Shehu Jaha ya bata, aka yi neman duniyar amma ba’a samu ganin shi ba. Tun Shehu yana sa ran za’a iya ganin jaki har ta kai gay a fitar da rai. Don haka sai yace a ransa “wallahi idan na gane jakin nan dinari day azan sayar da shi” alhali jakinsa akalla zai kai dinari hamsin.

Bayan yan kwanaki cikin ikon Allah sai aka gane jaki gas hi Shehu ya riga yayi rantsuwa cewa zai sayar da shi akan dinari daya.

Da dai yaga dole sai an sayar da shi akan hakan tun da yayi rantsuwa sai kamo jakin nan ya hada da magensa ya daura masu igiya daya sannan ya tafi kasuwa yayi ta zagayawa yana talla yana cewa “ina wanda zai sayi jaki akan dinari daya tare da mage akan dinari dari amma da sharadi sai dai a sayesu a tare”

Mutane duk wanda ya zaburo ya kwashi banza da zaran yaji sharadin cewa dole sai an hada da mage ita kuma dinari dari sai yaja baya. A haka Shehu ya kare yawonsa ko tayawa babu wanda yayi.

✍️ Al-kalam tv

16/09/2024

SHUGABA BOLA TINUBU YA TAYA AL’UMMAR MUSULMI MURNAR ZAGAYOWAR MAULIDIN ANNABI.

Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Musulman Najeriya murnar zagayowar bikin Mauludin Annabi Muhammad SAW.

Shugaban ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen koyi da kyawawan halaye da karantarwar Manzon Allah.

“Yayin da muke bikin Mauludi, ya kamata mu yi duba kan irin rayuwar da Annabi Muhammad ya yi, wadda ke cike da tsarki, tausayi, kyautatawa da kuma jin ƙai, dole ne mu yi kokarin ganin mun yi koyi da wadannan kyawawan halaye.” Inji shi.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su sadaukar da ranar Mauludi domin yi wa kasa addu’a da kuma tausayawa juna.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-kalam TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Al-kalam TV:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share