Muryar Talaka Daily News

  • Home
  • Muryar Talaka Daily News

Muryar Talaka Daily News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muryar Talaka Daily News, Newspaper, .

Matasan Bauchi Ta Arewa Sun Roki Siraj Ibrahim Tanko Ya Sake Neman Kujerar Sanata a 2027 Matasan  Bauchi T Arewa sun bay...
22/05/2025

Matasan Bauchi Ta Arewa Sun Roki Siraj Ibrahim Tanko Ya Sake Neman Kujerar Sanata a 2027

Matasan Bauchi T Arewa sun bayyana roƙon su ga tsohon ɗan takarar Sanatan Bauchi Ta Arewa a zaɓen 2023, Siraj Ibrahim Tanko, da ya sake tsayawa takara a babban zaɓen 2027. Wannan ƙiran na zuwa ne sakamakon gazawar Sanata Sama’ila Dahuwa Kaila, wanda ke wakiltar shiyyar a halin yanzu, wajen samar da ci gaba tun daga lokacin da aka rantsar da shi har zuwa yau.

A cikin wata sanarwa da Matasan s**a fitar bayan wani taron gaggawa da s**a gudanar, matasan sun nuna damuwa kan yadda yankin Bauchi Ta Arewa ke fuskantar koma baya a fannoni da dama na rayuwa.

“Muna roƙon Siraj Ibrahim Tanko da ya saurari kiran al’umma, ya sake fitowa takara a 2027. Shi matashi ne mai kwazo da hangen nesa, kuma muna da tabbacin cewa zai wakilci yankinmu da cancanta da gaskiya,” in ji shugaban Matasan, a cikin sanarwar.

Matasan sun bayyana cewa ƙoƙarin da Siraj Ibrahim Tanko ya yi a baya, da irin goyon bayan da ya ke samu daga matasa da dattijon yankin, su ne ke karfafa masu gwiwar neman dawowarsa fagen siyasa. Matasan sun bayyana cewa sun himmatu wajen ganin an dawo da martabar wakilci na gaskiya a yankin, ta hanyar goyon bayan Siraj Ibrahim Tanko a zaɓen mai zuwa.

Muhammad Sani Dattijo Mataimakin Gwamnan CBN, Ya Bayyana ƙoƙarin da suke Don rage Hauhawar Farashin kayayyaki da Inganta...
14/04/2025

Muhammad Sani Dattijo Mataimakin Gwamnan CBN, Ya Bayyana ƙoƙarin da suke Don rage Hauhawar Farashin kayayyaki da Inganta Tattalin Arzikin Najeriya a Taron JP Morgan na 2025

A yayin wani taro mai matukar muhimmanci da aka gudanar karkashin inuwar JP Morgan Forum a shekarar 2025, Muhammad Sani Abdullahi, Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Kan munufofin Tattalin Arziki ya bayyana cikakkun manufofi da tsare-tsaren da za su taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

A cikin jawabin nasa mai zurfi da hangen nesa, Muhammad Sani Abdullahi ya tabo batutuwa masu sarkakiya da s**a shafi tsarin musayar kudi, hauhawar farashi, da kuma gina tubalin ci gaba mai dorewa. Ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya na daukar matakai masu karfi domin daidaita musayar kudin waje da na gida, tare da saukaka harkokin kasuwanci da janyo hannun jari daga ketare.

“Manufofin da muke aiwatarwa sun mayar da hankali kan daidaita kasuwar musayar kudi da kuma karfafa gwiwar masu saka hannun jari,” in ji shi. Ya kara da cewa, irin wannan sauye-sauyen na nuni da alamar ci gaba, duba da yadda ake samun cigaba a matsalolin da s**a dabaibaye tattalin arzikin kasar a baya-bayan nan.

Dangane da hauhawar farashi, Sani Abdullahi ya jaddada cewa CBN na aiki tare da sauran hukumomin gwamnati domin rage radadin matsin tattalin arziki da ake fama da shi, Musamman ta fuskar abinci da albarkatun yau da kullum. A cewarsa, an dauki matakan gaggawa wajen kara samar da kayayyaki da tabbatar da daidaito a farashin su a kasuwa.

Jawabin nasa ya samu karbuwa sosai daga mahalarta taron, inda aka yaba da irin hangen nesan da ya gabatar, musamman game da bukatar hadin gwiwar bangaren gwamnati da na masu zaman kansu wajen gina ingantaccen tsarin tattalin arziki.

KBC Hausa

A Yaune 17/March 2025 Cikin Hukunchin Allah Hon. Nura Usman Ganaru Yasamu Damar Assasa Tubalin Ginin Masallaci A Garin K...
17/03/2025

A Yaune 17/March 2025 Cikin Hukunchin Allah Hon. Nura Usman Ganaru Yasamu Damar Assasa Tubalin Ginin Masallaci A Garin Katuri dake Madara District Katagum Local Government a Madadin Dr Bala Maijama'a Wunti.

Hon Nura Usman Ganaru Yayi Alkawarin Gina Masallacin Ne Shekara Biyu Das**a Wuce Yau Cikin Ikon Allah Yacika Alkawari Kamar Yadda Yadauka Ansadaukar Dawannan Ginin A Alh Bala Wunti Maijama'a.

Allah Yakara Bada Ikon Cigaba Da Ayyukan Alkhairi A Kasa Baki Daya.

Address


Telephone

+2349065768750

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Talaka Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar Talaka Daily News:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share