21/07/2025
Ambasada Salga ya jagoranci taron ADC don ƙarfafa gwiwa
Daga Ibrahim Muhammad Kano
Matasan jam’iyyar ADC da Ƙungiyar Iyali Ɗaya na jam’iyyar reshen ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano, ta gudanar ta taron zaburarwa da ƙarfafa gwiwa ga ‘ya’yan jam’iyyar domin tunkarar samun nasara.
Taron an yi shi ne a ɗakin taro na Mumbayya ranar Lahadi ƙarƙashin jagorancin shugaban ADC Iyali Ɗaya na ƙasa, shugaban Inuwar ‘yan takarar Majalisar Tarayya da na jiha a PDP a zaɓen 2023 da yanzu s**a koma jam’iyyar ADC, Ambasada AbdulRahman Mainasara Salga.
A jawabinsa a wajen taron, ɗan takarar Gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023 a jam’iyyar ADC, Malam Ibrahim Khalil ya ja hankalin mahalarta taron da cewa idan da gaske mutane suke za su yi canji, to a gani a aikace, kuma su riƙe amana, su zama masu jajircewa, “Domin haka ne matakin tabbatar da samun nasara,” in ji shi.
A nasa jawabin shugaban ADC Iyali ɗaya na ƙasa, AbdulRahman Mainasara Salga, ya gode wa mahalarta taron. Ya ce, dawowarsa Kano mako biyu da s**a gabata ya ga a kowace jiha ana cewa an karɓi ADC, amma sai ya ga ya k**ata a ga motsinta a nan Kano, shi ya sa s**a shirya wannan taro na ƙaramar Hukumar Dala.
Ya yi nuni da cewa akwai ban tsoro a tafiyar da ake a ƙasar nan a halin yanzu domin a matsayinsa na haifaffen ƙaramar hukumar Dala a Gwammaja ya bar Kano ya tafi Abuja da ₦1,500 kaɗai a matsayinsa na matashi don neman na kansa duk da iyayensa suna da hali, amma ya tafi ya kwana a masallaci da kasuwa a ƙoƙarin neman halal da yaƙinin Allah shi ne mai yin komai, kuma ya yi masa.
Ya ce ya ga haƙƙoƙin da ake saryarwa na al’umma da mutane da dama, za su iya amfana idan wakilansu da ake zaɓa suke zuwa Majalisar Tarayya Abuja suna yin abin da ya k**ata. Kuma ya yi ƙoƙarin nusar da wasu daga wakilan hanyoyin da za su bi su amfanar da al’ummarsu, amma sun yi wasarere da hakan, ba sa kulawa sai dai su zo su riƙa wasu abubuwa daban.
Ya ce, wannan kishin na ganin an sama wa al’umma dama ce tasa ya shiga siyasa domin ya taimaki al’umma, kuma idan ba wannan niyya ce a ransa ba kada Allah ya ba shi nasara.
Mainasara ya ce, lokacin da ya fito takarar Majalisar Tarayya a Dala ba shi da kowa a lokacin sai wasu jiga-jiran jam’iyyar s**a nuna ba sa yin sa, amma a haka ya tsaya ya dage ya shiga cikin takara da aka so a hana shi, amma ya karɓo ta a kotu saboda niyyarsa mai kyau ce.
Ya ce, a cikin jam’iyyar PDP sun samu mutane da yawa munafukai da yawa a cikinta sun sayar da jam’iyyar suna yi mata zangon ƙasa, ta hanyar amfani da Nyeson Wike don su riƙa haifar da matsala kar a sami nasara a jam’iyyar PDP, wanda idan da an tafi a hakan har zuwa zaɓen 2027 da Tinubu ya koma an gama zaɓe.
AbdulRahman Mainasara Salga ya ce, kasancewar suna yin siyasa ne don al’umma shi ya sa s**a dawo wannan tafiyar ta haɗakar ADC da suke goyon bayan tafiyar Atiku Abubakar.
Ya yi kira ga matasa su tashi su ƙwaci haƙƙin al’umma kar su bari a riƙa wulaƙanta su ko kuma a juyar da ƙwaƙwalwarsu.
Mainasara ya jaddada cewa sun dawo jam’iyyar ADC ne don tana da mutane jajirtattu, masu kishi da gaskiya, domin sai da APC s**a nemi su bai wa shugabannin ta kuɗi don su yi amfani da su don a haifar da rashin jituwa k**ar yadda s**a shiga PDP da SDP da sauran jam’iyyun adawa, amma s**a ƙi yarda.
Ya ce Atiku Abubakar yana son jam’iyyar PDP a ransa, su ma da suke tare da shi haka, amma saboda maƙiya da munafukai da aka ƙunsa a cikinta don hana ta zaman lafiya s**a ga cewa ba za a yi wa talakawa adalci ba, shi ya sa s**a fita, “Saboda maƙiya ba ba sa son al’umma, ana sayar da su. Domin me za mu sake zaɓen Tinubu? Ya k**ata mu tashi mu taimaki al’ummar mu ta hanyar bai wa ADC goyon baya,” in ji shi.
Shi ma a jawabinsa shugaban jam’iyyar ADC na jihar Kano, Hon. Musa Shu’aibu Ungogo ya ƙarfafa gwiwar matasa a kan su tashi su jajirce wajen nema wa al’umma mafita, domin shugabanni da s**a yi gwagwarmaya na baya domin samun ‘yancin ƙasar nan tun suna matasa s**a yi s**a kafa jam’iyyu irin su NEPU da NPC da s**a amfanawa al’umma da har yanzu ake tuna irin sadaukarwa da s**a yi.
A yayin taron an gabatar da muhimmiyar faɗakarwa a kan muhimmanci da tasirin amfanin kafar sadarwa na zamani wajen wayar da kan mutane don samun karɓuwa a harkar siyasa wanda Aminu Idris Tudun Wada ya gabatar.