
17/02/2025
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Darasi Ga 'Yan Mata
Daga Amina Amisco Adamu
'Yan mata wannan rubutun nawa yau akan ku ne. Ku kiyaye bin mutumin da kuke tunanin kamar ba zai cútąr daku ba. Dan Adam sai Allàh.
Wannan matashin ba za ka taba cewa zai iya ķìșa ba. Aŝhe makãșhi ne halinsa kenan, ya fake da addini yana kíŝa.
Dubunsa ta cika ne akan wata yarinya, inda ya ķãșhe ta ashe da dan rakiya ta zo bai sani ba. Aka yi ta jira shuru karshe lamba ta daina shiga. Ba ta fita a gidan ba bincike ya yi bincike har aka gano komai.
Dan Allah mata ku yi kokarin kare mutuncin ku namiji idan yana sonki dan Allah ba sai kin je gidansu ba.
Allah Ya kyauta.