Umar F Abdul

Umar F Abdul Domin samun inganttaun labaru, da wayar da kan mutane, shi ne dalilin bude wannan shafin.

SHUGABAN KASA TINUBU YA DAKATAR DA MINISTAN AL'UMMATA DA YAWAN TALAUCI daga ofishin. A daidai lokacin da ya sha alwashin...
08/01/2024

SHUGABAN KASA TINUBU YA DAKATAR DA MINISTAN AL'UMMATA DA YAWAN TALAUCI daga ofishin.

A daidai lokacin da ya sha alwashin tabbatar da gaskiya da gaskiya da rikon amana a cikin tafiyar da mulkin talakawan Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr. Betta Edu daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba. .

Shugaban ya kuma umurci Shugaban Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ya gudanar da kwakkwaran bincike kan duk wani abu da ya shafi hada-hadar kudi da ya shafi ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta tarayya, da kuma wata hukuma ko fiye da haka.

An umurci ministar da aka dakatar da ta mikawa babban sakatare na dindindin na ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta tarayya, sannan kuma shugaban kasa ya umurce ta da ta baiwa hukumomin bincike cikakken hadin kai yayin da suke gudanar da bincike.

Bugu da kari, shugaban kasar ya dora wani kwamitin da ke karkashin jagorancin Ministan Tattalin Arziki da Ma'aikatar Kudi don gudanar da bincike mai zurfi kan tsarin hada-hadar kudi da tsarin shirye-shiryen zuba jari na zamantakewa don sake fasalin cibiyoyi masu dacewa da kuma inganta ayyukan da s**a dace. shirye-shirye a yunƙurin kawar da duk wani rauni na hukumomi don fa'ida ta musamman na gidaje marasa galihu da kuma dawo da rashin amincewar jama'a game da shirin.

Wadannan umarnin shugaban kasa suna fara aiki nan take.

Chief Ajuri Ngelale
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman
(Media & Jama'a)

Zancen gaskiya idan ba tashi matasan Sokoto, Zamfara, katsina da Sauran su s**ayi s**a bada nasu gudumawar ba za'a dade ...
04/10/2023

Zancen gaskiya idan ba tashi matasan Sokoto, Zamfara, katsina da Sauran su s**ayi s**a bada nasu gudumawar ba za'a dade ba'a shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi yankin su( Ba fata nake ba).

Eh, hakkin gwamnati ne tsaron lafiya dukiya, da kuma rayukan al'ummar da suke shugabanta, amma idan s**a kasa tsinana abin kiriki bai k**ata ace mu zuba ido a cigaba da k@she mu irin kisan da ko dabbobi basu chanchanta da ayi musu ba.

Bai k**ata ace sabida gwamnati ta gaza ku zuba ido a cigaba da bautar da iyaye, yayye da kannen mu ba.

Ni Dan jahar Borno ne mazaunin Maiduguri I'm talking from experience, Lokacin da matsalar bōko haram ya tsananta al'umma s**a cire tsammanin cewa gwamnatin wancan lokacin zata magance musu matsalar rashin tsaro ga Kuma irin cin kashi da su Yan Bōko haram din suke yi musu a wancan lokacin sai s**a tashi tsaye Dan nema wa kansu mafita.

A Maiduguri akwai Lokacin da ko sunan bōko haram mutum bazai iya ambata ba Koda a cikin gidan sa yake.

Anyi Lokacin da ake shiga gida karfe 4, 5, 6 na yamma Kuma baza a fito ba sai washe gari, ba maganar Sallar Magrib, ko Isha a masallaci.

Anyi Lokacin da normal ne ganin bìndiga a cikin gari..

Anyi Lokacin da Kuna zaune za'a zo a k@she dan uwan ku a tafi salin alin ba abinda zai faru.

Anyi Lokacin da rashin tsaro yasa aka rufe makarantu anan Maiduguri, Kai hatta University of Maiduguri sai da aka rufe...

Anyi Lokacin da tsoron shiga cikin jama'a ake yi a cikin Maiduguri sabida tsoron tashin bōmb...

Anyi Lokacin da Maiduguri ya watse aka yi gudun hijira zuwa inda mutum zai samu aminci...

Anyi Lokacin da akayi wata tara ba mobile network a Maiduguri, idan mutum Yana so yayi waya sai ya biya kudin mota yaje Damaturu..

Anyi Lokacin da duk wani Jami'in tsaro boye kan shi yake...

Har Mai Girma Shehun Borno an kawai hari Allah madaukin sarki ya Kare shi.

Rashin tsaro yasa rana tsaka kawai aka haramta Mana hawa machine Wanda har yanzu ba'a hawa.

An k@she talaka.

An kas@he jami'an tsaro

An k@she Mai kudi.

An k@she sarakuna.

An k@she Malamai

An k@she Yan siyasa

An k@she Mana Dan takaran gwamna.

An tada Bōmb a kasuwa

An tada Bōmb a masallaci

An tada Bōmb a makarantu.

Da matasa s**a gaji da irin cin kashin da ake yi musu, sai s**a tashi nemar wa kansu mafita.

S**a cire tsoro a zuciyar su, s**a fara k**a yan ta'addan, zaka ga mutum me bìndiga Yana gudun Wanda take da sanda.

Dan Bōko haram din da ake tsoro yanzu Kuma shike tsoron Yan gari, Yana gudu don tseratar da rayuwa sa..

kowa ya zama Dan kato da gora a cikin gari, matasa s**a fara aikin da Jami'an tsaro s**a kasa Yi.

Da ikon Allah cikin kankanin Lokaci matasa s**a tsaftace cikin garin Maiduguri, aka kori yan ta'adda zaman lafiya yazo.

Ku tashi ku nema wa kanku mafita in Sha Allahu Allah zai taimake ku.

Ubangiji Allah ka zaunar ka kasar mu lafiya.

✍️ Mohammed Isa Hassan

IKON ALLAHMATAR DA TA TSINCI MILIYAN 62Wannan ita ce Hajiya Aishatu Yan Guru da ta tsinci zunzurutun kudi har Dalar Amur...
08/07/2023

IKON ALLAH
MATAR DA TA TSINCI MILIYAN 62

Wannan ita ce Hajiya Aishatu Yan Guru da ta tsinci zunzurutun kudi har Dalar Amuruka Dubu Tamanin ($80,000) kimanin Naira Miliyan 62.
Nan take ta miƙa kuɗaɗen ga hukumar Alhazan jahar Zamfara.

09/05/2023
Kuyi following na sabon page namu domin samun ingantatun labaru.
09/05/2023

Kuyi following na sabon page namu domin samun ingantatun labaru.

Sabuwar Makarantar Koyarwa Kenan Wacce Sheikh Farfesa Maqari Zaria Ya Gina Da Hannunsa Domin Koyar Da YaraDaga Muftahu Y...
07/03/2023

Sabuwar Makarantar Koyarwa Kenan Wacce Sheikh Farfesa Maqari Zaria Ya Gina Da Hannunsa Domin Koyar Da Yara

Daga Muftahu Yahaya Mai Dandarani

Umar Abdullahi one the members of Maiduguri Borno state media news company. popular name call umarfabdul1 born in 1/1/19...
04/03/2023

Umar Abdullahi one the members of Maiduguri Borno state media news company. popular name call umarfabdul1 born in 1/1/1995
He probably reaserch and investigation of live and current event and piece of daily news

Address

Maiduguri

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umar F Abdul posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Umar F Abdul:

Share