06/02/2025
🚨 | Yadda Ake Dillancin Kananan Mata
A ‘yan kwanakin nan, ina samun kalubale sosai daga mabarnata, wanda irin wannan exposé ɗin yake batawa kasuwa. A yau ma, zan sake kawo muku wasu wurare da bincike ya nuna ana dillanci da kuma farautar mata, musamman kananan ‘yan mata waɗanda ba su gama sanin rayuwa ba. Na yi wannan rubutu ne don na farkar da iyaye da kuma waɗanda amanar ‘ya’ya take hannunsu, don su san abin da yake faruwa kuma su kiyaye.
ℹ️ Disclaimer : Kafin na shiga wannan bayani, ina so mai karatu ya sani—kar don ka ji na ambaci wani guri ka ɗauka na yi ne don targeting wasu ko wata sana’a. Har wa yau, akwai mutanen kirki kuma masu k**antawa.
Gabatarwa.
A yau, mun wayi gari an samu wasu batagarin da aikinsu shine saka matasan ‘yan mata a cikin harkoki na banza, irin su lesbianism da kuma karuwancin gaban iyaye. Yarinya tana gaban iyayenta amma karuwanci take. Ku biyo ni a hankali don jin yadda irin waɗannan abubuwan suke kasancewa.
1. Masu Daukar Hoto
Yanzu abin da wasu batagari daga cikin masu daukar hoto suke yi shine kai ziyara duk wani wuri da ake biki ko tarukan mata, especially event centres. Kuma suna zuwa ko ka gayyace su ko ba ka gayyace su ba. Da zarar sun shigo, sai su fara farautar mata ƙanana marasa yawo. Daga nan sai su ɗauke su hoto kyauta, sai su karɓi lambar waya da sunan idan hoto ya zama ready za a tura musu.
Bayan an tashi biki, shi mai photo yana da shafi a Instagram. Sai ya je ya saka waɗannan hotuna don kawalai da ‘yan iska su gani. Idan mutum ya ga yarinyar da ta masa, sai ya kirata a waya ya ce tazo karɓar hoto. Idan ta zo, sai ya ba ta hoton sannan ya kawo kuɗi masu kauri ya bata, ya ce gashi, wani ya ganki yana son ki. Wasu ma har iPhone ake ba su, a ce gift daga wani unknown admirer. To shikenan, daga nan sai a ce tazo wuri kaza, daga nan magana ta kare—sai wanda Allah ya so da rahama. Irin wannan ta faru bila’adadin. Shi mai hoto ya gama aikinsa, sai a biya shi kudin hada wannan harka.
2. Gidan Makeup/Gyaran Jiki da Ire-Irensu
Suma masu gidajen makeup da gyaran jiki suna da k**anceceniya da masu gidajen hoto. Domin bayan sun yi wa mace makeup, suna da iPhone mai camera mai kyau. Sai su ɗauki hotunanki, sai a ajiye. Su kuma mata, dama ba su da wayo wasu daga cikinsu—ganin an ce za a saka ta a Instagram, sai ta fara murna. To, itama daga nan za a fara tura hotonta group-group na kawalai. Idan ta yi, sai a kirata a mata introducing wani, daga nan shikenan.
Sannan bayan haka, ‘yan le****ns sun mayar da gidan makeup k**ar wani transit station. Domin idan an zo, za a yi ta zantuttuka na ƙarya, ana nuna kuɗi, ana maganar kuɗi don yarinyar ta ji ta yi sha’awa. Daga nan sai ta riƙa ganin to su gasu suna fantamawa, itama sai ta yi sha’awa, daga nan ake recruiting ɗinta. Kafin ka ce kwabo, an kaita. Shi yasa ƙannen mu da yawa muka ƙi bari su yi training ɗin Makeup Artist, saboda gudun faɗawa. Don Allah, maza waɗanda matansu suke makeup, ku zauna da su ku tambaye su—wallahi labaran da za ku sha ba su da adadi.
Wata majiya ta tabbatar min da cewa har sawa suke a rika bi gida gida ana kawo janyo musu yara. Misali, yarinya zata rika zuwa neighbours dinsu gidan wata kawa haka. Sai ta rika mata hirar samun kudi. Da kuma kayata mata wasu abubuwa na morewar rayuwa. Ko kuma ta fadi wani abu da zai sa ayi wata fita ta musamman don kawai aje gidan wannan kawaliya. Mai bada wannan labarin tace, kawar tata zuwa tayi har gida tace mata suje wata unguwa. Da shigarsu gida sai taji k**ar dama an san za'a kawo ta. Sai ga wasu yan bariki nan sun shigo. Akai ta wasu hirarraki na banza a karshe da s**a tashi tafiya sai s**a basu 50k. Ita waccen yarinya sai aka ce ta dauki 20k sai ta barwa yarinyar 30k tunda itace bakuwa a cikinsu. Tace daga nan bata kara kula waccen ba. Domin clearly bata ta take so ayi. So, haka suke recruiting yan mata har cikin gidan iyayensu.
3. Hostels Din Jami’o’i
Hostel sai dai Innalillahi! Yanzu haka, duk inda ka san akwai wani hostel a ƙasar nan, to abubuwan da suke faruwa a wurin sai addu’a. Idan aka ce weekend ya zo, haka za a riƙa turo motoci daga wasu jahohin irinsu Abuja, Kano, Kaduna, wasu kuma kuɗin ticket ɗin jirgi ake turawa. A riƙa dibar ‘ya’yan mutane, ana kaisu Abuja, ana kwana da su.
Ranar Monday da sassafe, yarinya ta biyo jirgin farko, ta dawo school k**ar bai faru ba. Shi yasa idan ka je security offices na jami’o’i, ka yi hira da su, sai ka ji k**ar abin ba da gaske ba. Abortion cases babu adadi. Kuma ba wanda zai iya hana wannan.
Kawai mafita shine yarinya ta zauna a gidan ubanta, ta yi karatun nan. Idan kuma ba ka da gida a garin, ka nemi wani naka, ta zauna a gurinsa. Kuma idan kuna ganin k**ar ba gaskiya bane, idan ka san wata mai zama a hostel, ka tambayeta labarin abin da yake faruwa a hostels, za ka sha mamaki.
Akwai case na wata yarinya da ta rasu. Ita mazauniyar wani hostel ne a daya daga cikin jamioin kasarnan. Kuma irinta suna sa yawa. Cewa iyayenta yayi zasu tafi SIWES. Ashe wani Alhaji ne yake so su tafi Dubai shakatawa. Haka kuwa akai - s**a tafi wajen watanta biyu a hotel room a Dubai. Ciwon ajali ya same ta kafin azo gida ta rasu. Kuma da mutum ya rasu case ya zama babba. A karshe dai iyayenta sun cika da mamaki yadda wadda take zaune a Hostel tana SIWES amma gata a Dubai ta mutu.
📍 Sannan iyaye ku rika kaiwa yayanku ziyarar bazata domin muna da labarin cewa mata da yawa da suke cewa suna zaune a Hostel ba a hostel din suke ba. Zuwa suke su k**a dakuna a wajen makaranta tare sa samari su rika kwana tare. Komai tare. Wasunsu sunyi ciki yafi a kirga. Daga 100 level har final year. Idan ya gaji da ita kuma sai ta sake sabon saurayi shima ya karbi nasa rabon. Haka suke wa kawunansu.
Jama’a, sai mun ƙara dagewa da addu’a da kuma saka ido. Muna cikin musiba. Allah ya kare zuriyar mu daga wannan fitintinu.
---
Muhammad Ubale Kiru
Copyright Reserved ©