Bayajidda24

Bayajidda24 Ingantattun Labarun Duniya Cikin Harshen Hausa

Zaben 2027: Haɗakar Bala Mohammed Da Peter Obi Nasarace Ga Al'ummar NajeriyaKungiyar Matasa ta Yankin Neja Delta (NDYC) ...
17/03/2025

Zaben 2027: Haɗakar Bala Mohammed Da Peter Obi Nasarace Ga Al'ummar Najeriya

Kungiyar Matasa ta Yankin Neja Delta (NDYC) ta jinjinawa hadin gwiwar Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, wanda kuma shi ne Shugaban Gwamnonin PDP, da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi. Kungiyar ta bayyana haduwar su a matsayin matakin da zai kawo sauyi a siyasar Najeriya, domin yana dogara ne akan juna, kishin kasa, da hangen nesa na ci gaba.

A wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke bukatar jagoranci na gari da ke kula da bukatun al’umma, Bala Mohammed da Peter Obi sun zama sabbin shugabanni da za su iya kawo sauyi. Bala Mohammed ya nuna jajircewarsa wajen hadin kan kasa da gina manyan ababen more rayuwa, yayin da Peter Obi kuma ke da suna wajen ingantaccen shugabanci da sarrafa tattalin arziki cikin gaskiya. Hadin gwiwarsu alama ce dake nuna cewa siyasa ta Najeriya na tunkarar sabon salo na gaskiya da ci gaba.

NDYC ta kwatanta wannan sabon salon siyasa da tsoffin 'yan siyasa kamar Atiku Abubakar, wadanda ke makale cikin tsarin siyasar da ke da alaka da son zuciya. Sabanin irin wadannan ‘yan siyasa da ke kokarin hawa mulki don biyan bukatun kansu, Bala Mohammed da Peter Obi suna wakiltar shugabancin da ke mayar da hankali kan gaskiya, nagarta, da ci gaban kasa.

Kungiyar ta jaddada irin nasarorin da Bala Mohammed ya samu a Bauchi, musamman a bangaren ilimi, kiwon lafiya, da gyaran birane, wanda ya nuna cewa yana da kwarewar tafiyar da gwamnati. Haka kuma, irin salon tafiyar da mulki na Peter Obi a jihar Anambra alama ce ta shugabanci mai inganci da dogaro da tattalin arziki mai dorewa. Idan aka hada karfin su a 2027, Najeriya na iya samun gagarumin ci gaba.

NDYC ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa, musamman matasa, da su goyi bayan wannan hadin gwiwa domin tabbatar da cewa 2027 ba zai zama shekarar sake maimaita tsoffin ‘yan siyasa ba, sai dai shekarar da za a fara sabon salo na shugabanci nagari. Kungiyar ta bayyana cewa zamanin siyasar da ke cike da kage da lalacewa ya kare yanzu lokaci ne na shugabanci na gari, gaskiya, da sakamako mai kyau ga al’umma.

SIGNED
Comrade Israel Uwejeyan
National Coordinator, Niger Delta Youth Congress (NDYC)

Yanzu haka Datar MTN SME tana tafiya Successfully a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD. Kamfanin MTN sunyi susp...
15/03/2025

Yanzu haka Datar MTN SME tana tafiya Successfully a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD.

Kamfanin MTN sunyi suspended din Datar MTN SME har sabuwar da s**a kawo shiyasa ta kare a kasuwa masu ita kuma sun zabga mata kudi da kyar ake samota wurin mutanen kudu shiyasa za kuga ba kowane Application din Data bane za kuga Datar SME a yanzu ba, karshe dole kowa ya koma siyan MTN GIFTING kafin su sake kawo wata sabuwar Datar tasu.

Yanzu haka Datar MTN SME tana tafiya a cikin Application din ABBA PANTAMI DATA LTD, itama MTN GIFTING 1GB Naira 355 tana tafiya Successfully.

Duk wanda SME ta mishi tsada sai ya sayi MTN GIFTING.

Kuyi Download din Application din ABBA PANTAMI DATA:
👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.abbapantamidata.app

Mai bukatan karin bayani, ya tuntubi daya daga cikin customer care ta WhatsApp;
09138275183
08126081967
07046868000
07061347599.

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami zata ɗauki nauyin dalibai dubu daya domin rubuta jarabawar shiga jami...
22/02/2025

DA DUMI-DUMI: Gidauniyar Professor Isa Ali Pantami zata ɗauki nauyin dalibai dubu daya domin rubuta jarabawar shiga jami'a (JAMB)

Gidauniyar Professor Isa Pantami tana sanar da jama'a cewa zata biyawa dalibai 1000 ƴan asalin jahar Gombe masu ƙaramin karfi ƙudin jarabawar shiga jami'a (JAMB). Wannan yana cikin manufofin wannan gidauniyar na ganin an samarwa matasa ingantaccen ilimin zamani.

Cikin mutane 1000, Professor Pantami ya ɗauki nauyin aɗadin mutane 550 sai kuma daliban shi; Salisu Abdurrazak Saheel ya ɗauki nauyin mutum 200 da kuma Nafi'u Muhammad ya biyawa mutum 250.

Wannan ƙoƙari ne na ganin an ƙarfafa matasa masu tasowa da kuma ƙara musu ƙarfin guiwa domin samun ƙwarewa da kuma zama jagorori nagari a cikin al'umma.

A cike form ta wannan ta Link dake a cikin comments section:

Allah ya bawa masu rabo sa'a.

Ministan Tsaro Ya Jagoranci Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Na Jihar Jigawa Zuwa Ɗaurin Auren 'Yar Tsohon Kakakin Majalisar Jih...
09/02/2025

Ministan Tsaro Ya Jagoranci Jiga-Jigan Jam'iyyar APC Na Jihar Jigawa Zuwa Ɗaurin Auren 'Yar Tsohon Kakakin Majalisar Jihar

Mai girma Ministan Tsaro na Nigeriya HE Mohammed Badaru Abubakar CON, mni ya jagoranci dukkanin masu ruwa da tsaki na Jam,iyyar APC na Jihar Jigawa da sauran Mukarraban Gwamnatin Jigawa zuwa wajen Daurin auren diyar tsohon kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Alh. Idris Garba Jahun wanda aka daura auren a ranar asabar-8-ga wannan wata na Fabarairu a Babban masallacin Juma,a na garin Jahun.

Mai girma Ministan ya sami tarya ta musanman daga Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alh. Aminu Usman Gumel a madadin Gwamnan Jiha, Mallam Umar A Namadi fca, sauran wanda s**a rufa masa baya sun hada da Sakataren Gwamnatin Jiha Mallam Bala Ibrahim da Shugaban Ma,aikatan a Fadar Gwamnatin Jiha Alh. Mustafa Makama da Yan Majalisar zartarwa dana Dokoki na Jihar Jigawa, da Yan Majalisar Tarayya da sauran mukarraban Gwamnatin Jiha.

Haka zalika mai girma Ministan ya sami rakiyar, Shugaban Jam'iyyar APC na Jiha Alh. Aminu Sani Gumel, da Ma,ajin Jam, iyyar APC na Kasa Alh. Basheer Usman Gumel, da Jigo a Jam,iyyar APC na Jiha Alh. Isah Gerawa, da Darakta Janar na yakin neman zaben APC a shekarar 2025 Alh.Lawan Ya,u Roni da Alh. Ubale Hashim da Tsafaffin Shugabanin Kananan Hukumomin Jihar da sauran dubban magoyabayan Jam, iyyar APC.

Mati Ali.
PA Media & Publicity to the Hon. Minister of Defence

07/02/2025

Zarge-zargen Naja'atu Muhammad akan Nuhu Ribadu cike suke da rashin makama.

07/02/2025

Fitaccen ɗan gwagwarmaya Comr Hamza Saulawa ya caccaki Naja'atu Muhammad kan zarge-zargen da ta yi ga Malam Nuhu Ribadu

04/11/2024
30/10/2024
01/06/2024

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bayajidda24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share