
11/07/2025
Yadda Aka K**a Mabarata 210 Dakan Dauko Kananan Yara Haya Don Yin Bara A Abuja
Gamayyar jami'an tsaro karkashin Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta k**a mabarata 210 a yayin wani samame a wurare da dama da nufin tsabtace birnin Abuja, domin kawar da mabarata, yan bola, da 'yan “one-chance," da sauran masu gararamba akan titunan birnin.
Hukumar Babban Birnin takuma nuna takaici akan iyayen da ke bada 'yanyan su haya da nufin aje ayi bara dasu.
Mukaddashiyar Daraktar Jin Daɗi ta Hukumar Babban Birnin, Gloria Onwuka, tace da yawan mabaratan da aka k**a ba suda alaƙa ta jini da yaran da suke bara da su, wanda da yawa daga cikin kananan yaran hayar su suke daukowa daga wurin asalin iyayen su, wasu kuma daga cikin mabaratan suna kwaikwayon sa bandeji na karya ajikin su domin karɓar taimako. Yaran da yawa an kawo su daga jihohi k**ar Kano da Katsina da sauran wasu jihohi.
Mabaratan sun haɗa da maza 80, mata 58 da yara 72, kuma an kaisu cibiyar gyaran hali dake garin Bwari.
An kuma tabbatar da k**a 'yan one-chance wayanda yanzu haka suna a hannun 'yan sanda don zurfafa bincike.