08/04/2025
KWANKWASIYYA KENAN
Captain Jibrin Nalado Aliyu na daya daga cikin yan Jihar Kano da Jagora Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki nauyin karatun su zuwa Kasar Jordan domin koyon tukin Jirgin sama. Yana daya daga cikin mutum 100 da s**a amfana inda a halin yanzu da yawan su suna aiki da kamfanoni daban daban.
Yanzu wannan bawan Allah shine shugaban karamar Hukumar Minjibir. Wannan ya nuna karara yadda Kwankwasiyya ke cicciba alummar Jihar Kano musamman matasa domin cimma burukan su na rayuwa.
Duk alummar da ta ci gaba, za ka samu wannan alumma ta bawa Ilimi muhimmanci ne. Wannan ce ta sanya a halin yanzu, Gwamanan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf, ya himmatu wajen ganin ya gyara komai daya shafi Ilimi domin Jihar Kano ta kere sauran Jihohi ta wannan fuska.
Kafin zuwan Jagora Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Gwamna, matuka Jirgin sama basu fi guda 10 ba a Jihar Kano. Wannan ce ta sanya ya dauki nauyin matasa 100 a wannan bangare kadai kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Yanzu dole idan ana maganar yawan matuka Jirgin sama a Najeriya kuma kwararru, Jihar Kano dole na sahun gaba.