27/06/2022
Wani matashi ya Mika takardar korafi ga Gwannatin jihar katsina, kan zargin TSB da saida offer tare da wasu korafe-korafe.
A ranar 14june2021 Wani matashi ya gabatar da takardar korafe-korafen Saba ka,ida da rashin bin dokar daukar aiki na malaman sakondire ga Gwannatin jihar katsina. Matashin mai suna shamsuddeen Lawal karbaba, Dandume, ya sha wallafa zarge-zarge ga hukumar daukar malaman sakondiri TSB, akan rashin yin daidai da kuma sabawa tare da karya dokokin daukar maaikata na kasa da kuma na jihar katsina.
Acikin takardar korafin wadda ya mika a ofishin Gwamnan na katsina, Shamsuddeen karbaba, ya roki Gwannatin jihar katsina da ta dubi korafin su da idon rahama, wajen ceto katsinawa daga kama-karya, da zargin saida takardar daukar aiki(offer), tare da nuna fifiko ga yan uwa da abokai, wajen daukar aiki.
Matashi ya nuna cewa, ansan Gwannatin jihar katsina da bada mahimmanci ga harkar ilimi, tare da bin dokokin da tsari wajen ayyukan ci gaban al,umma, amma seda kash, hukumar TSB tana San ta zubar ma katsinawa kima a idon yan Nijeriya. Sannan tana so ta zubar da mutuncin Gwannatin jihar katsina, duk da kokarin Gwannatin wajen kawo tsare-tsare masu amfani da cigaban katsinawa.
Acikin takardar korafin, shamsuddeen karbaba, ya kara da cewa, ya kai kusan shekara Goma yana koyarwa ta wucin gadi(casual teaching staff), Abin mamaki wasu daga daliban da ya koyar a sakondiri, har sun samu aikin koyar wa mai cikakken albashi (permanent and pensionable), amma su haryanzu suna casual, tare da cewa ya kammala NCE Kimanin shekara goma, kana ya kammala digiri kimanin shekara biyar. Dalili kuwa shine, kamar yadda yayi zargi, yawancin mutane a yanzu basa samun aiki da TSB hakanan ta hanyar interview, saidai a saida masu da takardar daukar aiki, ko kuma suna da uwa a gindin Murhu.
kazalika, matashin ya roki Gwannatin jihar katsina, da ta kafa kwamiti na kwararru, da zasu binciki lamarin, tare da yin garanbawul ga huku