11/06/2025
Anas Yusuf na Nasarawa United Zai Karɓi Naira Miliyan 3.6 Don Lashe Kofin Eunisell Boot a Gasar NPFL
Ɗan wasan gaba na Nasarawa United, Anas Yusuf, yana shirye ya karɓi kuɗin lada na Naira Miliyan 3.6 bayan ya zama babban ɗan kwallon da ya fi zura kwallaye a Gasar Firimiyar Najeriya ta 2024/25 (NPFL), inda ya ci kwallaye 18.
Za a mika masa lambar yabo ta Eunisell Boot a wani taron ban girma da za a gudanar a ranar Jumma’a, 13 ga Yuni, 2025, a Radisson Blu Hotel, GRA Ikeja, Lagos.
Kamfanin Eunisell, wanda ke kan gaba wajen samar da kayan aikin man fetur da sinadarai a yammacin Afirka, shi ne ke daukar nauyin wannan gagarumin lambar yabo. Sun daidaita darajar kowace ƙwallo da Naira 200,000, wanda ya kai jimillar Naira Miliyan 3.6 ga Anas Yusuf saboda kwallaye 18 da ya ci.
Tun lokacin da aka fara bayar da wannan lambar yabo a shekarar 2018, an riga an karrama shahararrun 'yan wasan gida kamar su Junior Lokosa (2018; Kano Pillars), Sunusi Ibrahim da Mfon Udoh (2019), Israel Abia (2020), da Chijioke Akuneto (2022).
Anas Yusuf ya shiga cikin wannan jerin taurari masu kwarewa, kuma ya zama na biyu daga Nasarawa United da ya lashe wannan lambar yabo, bayan Sunusi Ibrahim a shekarar 2019.
Shugaban kamfanin Eunisell, Chika Ikenga, ya bayyana cewa:
> “A Eunisell, muna mutunta hazaka da ƙoƙari. Eunisell Boot ba kawai lambar yabo bace — alama ce ta goyon bayan ci gaban ƙwallon Najeriya da karrama ƙwazon matasa. Wannan nasarar Anas Yusuf ta nuna abin da zai iya faruwa idan baiwa ta haɗu da dama.”
Kamfanin Eunisell tun 2015 yana ɗaukar nauyin ƙungiyar Abia Warriors FC, wanda ke ƙara nuna jajircewarsu wajen tallafawa ƙwallon ƙafa a gida Najeriya.
Taron shekarar 2025 zai kuma nuna cikar shekaru 10 da kamfanin Eunisell ke tallafawa wasanni, tare da niyyar ci gaba da haɓaka baiwa a gida.