19/12/2021
Nigerian government guys getting the upper hand as they fight the bandits in zamfara/sokoto area. The fight should have been done long before now, as the bandits caused immutable destruction of millions of civilian population and properties in the area
Dakarun Nijeriya sun tashi maɓoyar Turji, inda su ka kashe ƴan ta'adda da dama a dajikan Zamfara da Sakkwato
Rahotanni na baiyana cewa an illata jagoran ƴan ta'adda masu fashin daji, Bello Turji bayan da ya samu muggan raunuka yayin da jiragen yaƙin sojoji su ka kai hari maɓoyarsa da kuma sansanonin ƴan tashin daji, kamar yadda jaridar PRNigeria ta jiyo da ga wata majiya da ga ɓangaren jami'an tsaro.
Haka-zalika jiragen yaƙin gamaiyar rundunar dakaru ta Sintirin Haɗin Kai sun hallaka ƴan fashin daji a dajikan Zamfara da Sakkwato da sassafiyar Lahadi.
Majiyar sirri ta rundunar soji ta tabbatarwa PRNigeria cewa an kai gagarumin harin da a ka kai a dajikan ta sama da ƙasa ne a Shinkafi da ke Zamfara, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni a Sakkwato.
Majiyar ta ce kawo yanzu dai ba a tantance adadin yan ta'addan da a ka hallaka a hare-haren ba.
PRNigeria ta jiyo cewa sauran yan fashin dajin da su ka samu raunuka kuma su ka tsere, sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin ƙasa a cikin jeji.
Majiyoyin tsaro na sojoji sun tabbatar da cewa hare-haren da a ke kaiwa ƴan ta'addan a Arewa-Maso-Yammacin Nijeriya na haifar da ɗa mai idanu kuma a na samun nasara.