Tangaran

06/08/2024
Kayan abincin daba talakawa ake rabawa ba, ’yan jam’iyya kadai ake bawa, inkai ba karensu bane babu abinda zasu baka, sa...
06/08/2024

Kayan abincin daba talakawa ake rabawa ba, ’yan jam’iyya kadai ake bawa, inkai ba karensu bane babu abinda zasu baka, sau nawa aka raba abincin suwaye suke samun tallafin?, shin yayi maganin matsalar?.

Iya kwana nawa tallafin naku zai dauki mutane?, shin abincin da zaku raba zai kai har karshen rayuwar mutane ne?, yaudara ce kawai in zakuyi abinda mutane suke so kawai kuyi.

Amma maganar wani tallafi yaudara ce karyace munafurci ne, adawo da tallafin mai, wutar lantarki da lafiya, sannan a bude boda, idan kukayi haka ku rike kudinku da tallafin abincin bama bukatarsa.

Gobenmu data yayanmu kawai mukeso tayi kyau.

Yayin taron majalisar zartarwa ne Ministan Yaɗa Labarai, Muhammed Idris ya shaida wa ƴan jarida cewa Shugaba Tinubu ya u...
15/03/2024

Yayin taron majalisar zartarwa ne Ministan Yaɗa Labarai, Muhammed Idris ya shaida wa ƴan jarida cewa Shugaba Tinubu ya umarci jami'an tsaro da su ƙubutar da yaran Kuriga kuma "a tabbatar da cewa ba a biya 'yan bindigar ƙudin fansa ba."

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4c8SL29

Masana na ganin cewa Amurka da sauran kasashen Yamma ba sa kai irin wannan taimako na tsaro, sai inda su ma za su amfana...
15/03/2024

Masana na ganin cewa Amurka da sauran kasashen Yamma ba sa kai irin wannan taimako na tsaro, sai inda su ma za su amfana.
Tangaran

Wasu rukunin lauyoyi a jihar Kano, ƙarƙashin Barista Badamasi Sulaiman Gandu, sun yi ƙarar Mawakin nan Dauda Kahutu Rara...
19/04/2023

Wasu rukunin lauyoyi a jihar Kano, ƙarƙashin Barista Badamasi Sulaiman Gandu, sun yi ƙarar Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara, wajen Mai martaba Sarkin Katsina da Mai martaba Sarkin Daura.

Rukunin Lauyoyin, sun aike wa Sarakunan biyu takardar kokensu, kan zargin Rarara da yin wakoki yana aibata manyan yan siyasar jihar Kano.

A cewar Lauyoyin, wakokin da Rarara yake yi suna janyo zage-zage da cin zarafi a tsakanin jama'a, inda s**a ba shi shawarar, ya gyara harshensa a gaba, sannan ya fito ya nemi afuwa ko kuma su ɗauki mataki na gaba.

Sheikh Sudais ya kaddamar da wata na’ura wadda za ta taimaka wajen hana yara bacewa a masallatan Ka’aba da na Annabi. Na...
13/04/2023

Sheikh Sudais ya kaddamar da wata na’ura wadda za ta taimaka wajen hana yara bacewa a masallatan Ka’aba da na Annabi.

Na’urar za ta samar da wata takardar shaida da za a rinka makalawa a hannun kanana yara a duk lokacin da za su shiga daya daga cikin masallatan.

Za a rubuta sunan yaro da kuma lambar iyayensa a kan takardar, wanda hakan zai bayar da damar kiran iyayen yaro da zarar ya bace.

Yara da dama na bacewa a cikin jama’a a masallatan Ka’aba da na Annabi saboda yawan mutanen da ke ziyartar masallatan.

📸 - Haramain Sharifain

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke nan lokacin da ya kai ziyara masallaci da ƙabarin Annabi Muhammadu (SAW) a Madina ...
12/04/2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke nan lokacin da ya kai ziyara masallaci da ƙabarin Annabi Muhammadu (SAW) a Madina ranar Talata.

📸: Haramain Sharifain

Dan ƙasar Masar Omar Mohammad Hussein ya lashe musabaƙar Ƙur'ani ta duniya da aka yi a Tanzaniya.Omar ya samu kyautar mi...
10/04/2023

Dan ƙasar Masar Omar Mohammad Hussein ya lashe musabaƙar Ƙur'ani ta duniya da aka yi a Tanzaniya.

Omar ya samu kyautar miliyan 23 na kuɗin Tanzaniya, daidai da dalar Amurka 10,000 (fiye da naira miliyan bakwai).

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'unAllah ya yiwa mai ɗakin Alhaji Aminu Ɗantata Hajiya Rabi Tajuddeen Galadanci da aka f...
09/04/2023

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un

Allah ya yiwa mai ɗakin Alhaji Aminu Ɗantata Hajiya Rabi Tajuddeen Galadanci da aka fi sani da Mama Rabi rasuwa.

Mama Rabi ta rasu a ƙasar Saudia bayan ta sha fama da rashin lafiya.

Ƴaƴan da ta bari su ne Alhaji Tajuddeen Ɗantata da Hajiya Batulu Ɗantata da Hajiya Jamila Ɗantata da Hajiya Aliya Ɗantata Malama Batulu Ɗantata.

Muna addu'ar Allah ya gafarta mata Amin.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tangaran posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Tangaran:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share