
28/07/2025
GAREKU TIJJANAWA
Maulana Sheikh Ibrahim Inyass yana cewa:
كَــذَا رَفْـــعُ رَايَاتِ الْحَنِيفَةِ مُعْلِنًـــا
بِإِبْطَـــالِ آرَا كَرْدَنَـــالَ الْمُضَيَّـــعِ
أُزِيـــلُ خِلاَفًـــا بَيْـــنَ قَوْمِ مُحَمَّــدٍ
فَيَرْبُطُنَا التَّوْحِيدُ مِــنْ كُلِّ مَوْضِـعِ
فَنَمْشِي عَلَى نَهْــــجِ الْأَمِينِ سَوِيَّــةً
نُـتَابِعُــــــهُ فَالْكُــــلُّ جِـــدُّ مُتَبَّــــعِ
Wato:
Buri na in daga Tutar Musulunci a bayyane, sannan na lalata duk wani Ra'ayin Cardinal makaskanci (wato Jagoran yada Addinin Nasara)
Sannan burina na kawar da Sabani tsakanin Al'ummar Annabi Muhammad S.A.W sai Tauhidi ya haɗa mu daga kowanne muhalli.
Duk mu yi daidai wajen tafiya akan tsarin Annabi Muhammad S.A.W, sai kowannen mu yayi kokari wajen biyayya ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam.
Wanda duk yake fada shirin hadin kai, cikin Yan Faila to ya sani yana fada ne da Manufofin Shehu Ibrahim Inyass kai tsaye, kuma ku sani tashi a hada kan Musulmi umarnin Allah ne, umarnin Manzon Allah ne, don haka wannan aikin baya jiran wani mutum ya yarda ko kar yarda.
ALHAMDULILLAH KULLUM NASARA TANA KARA BAYYANA A GAREMU
Idris Usman Ahmad Hadejia