13/07/2025
TARIHIN TSHOHON SHUGABAN NIGERIA JANAR MUHAMMADU BUHARI (RTD)
HAIHUWA:
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga Disamba, 1942, a garin Daura, Jihar Katsina. Ya fito daga iyalin Musulmi kuma Fulani. Mahaifinsa, Mallam Hardo Adamu, manomi ne kuma Malami; mahaifiyarsa kuma Hajiya Zulaihat, ta fito daga Zaria.
ILIMI:
Ya fara makarantar Primary School ta Daura, daga nan ya wuce Middle School Katsina.
Daga baya ya samu gurbin karatu a Katsina Provincial Secondary School (wanda aka fi sani da Government College Katsina).
Bayan kammala sakandare, ya shiga Nigerian Military Training College (NMTC) a Kaduna a shekarar 1962.
Daga nan sai ya je Mons Officer Cadet School a Aldershot, Ingila, sannan ya karɓi horo a India, USSR (Rasha) da America.
RAYUWAR SOJA DA SHUGABANCI NA MULKIN SOJA (1983–1985)
Ya shiga soja a shekarar 1961.
Ya taka rawa a yakin basasar Najeriya (1967–1970), ya rike mukamai da dama kamar Haka;
Gwamnan Jihar Arewa-Maso-Yamma (1975–1976).
Kwamandan rundunar soja ta 3.
Kwamishinan man fetur a lokacin mulkin Janar Murtala Mohammed.
A ranar 31 ga Disamba, 1983, ya jagoranci juyin mulki da ya kifar da gwamnatin Shehu Shagari, sannan ya zama shugaban kasa na mulkin soja daga 1983 zuwa 1985.
An kifar da shi ta hanyar juyin mulki a shekarar 1985, a lokacin Janar Ibrahim Babangida.
RAYUWAR BAYAN MULKIN SOJA:
Bayan kifar da mulkinsa, an tsare shi har tsawon shekaru fiye da biyu ba tare da tuhuma ba.
Ya zama daya daga cikin jagororin da s**a nemi a tsaftace Najeriya daga rashawa da almundahana.
GWAGWARMAYA TA SIYASA:
Ya tsaya takarar shugabancin ƙasa sau uku:
2003 (tare da ANPP) – ya fadi.
2007 (tare da ANPP) – ya fadi.
2011 (tare da CPC) – ya fadi.
A 2015 ya sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC bayan da CPC da wasu s**a hade.
A karo na hudu, sai ya samu nasara ya zama shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2015, ya sake lashe zabe a 2019, ya kammala mulkinsa a 29 ga Mayu, 2023.
MUHIMMAN AIKI DA CIGABA A LOKACIN SHUGABANCINSA
Ya ƙaddamar da yanayin yaki da rashawa (Anti-Corruption War).
Ya kafa N-Power da wasu shirye-shiryen tallafi ga matasa da marasa galihu.
Ya jagoranci gina layin dogo (Railway Projects) da tituna a sassan Najeriya.
Ya yaki kungiyar Boko Haram, duk da cewa har yanzu ta cigaba da kai hare-hare.
Ya ƙaddamar da naira re-design policy da kuma yaki da satar kudaden gwamnati.
ZARGI DA SUKAR MULKINSU:
A lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023, an zargi gwamnatin Buhari da abubuwa da dama, ciki har da:
1. Rashawa:
Duk da ya yi ikirarin yaki da cin hanci, an zargi wasu jami’ansa da karkatar da kudade.
Ana ambato batun Abba Kyari da wasu manyan gwamnati da s**a fuskanci zargi.
2. Tabarbarewar Tsaro:
An zargi mulkinsa da kasa magance matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa maso yamma da arewa ta tsakiya (banditry da kidnapping).
Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da kai hare-hare duk da kokarin gwamnati.
3. Matsin Tattalin Arziki:
Farashin kaya ya tashi, hauhawar farashi (inflation) ya yi muni sosai.
Kudin Naira ya ruguje sosai, matsalar kudaden kasashen waje (Forex) ta tsananta.
An shiga matsanancin matsin tattali bayan COVID-19 da kuma janye tallafin man fetur.
4. Rashin Jin Dadi ga Jama’a:
Talauci ya karu sosai a lokacin mulkinsa.
Ana zargin gwamnatinsa da rashin kulawa da bukatun talakawa, musamman ma a karkara.
An yawaita yajin aiki da gurguntar da fannin ilimi (har da ASUU Strike mai tsawo).
5. Rikicin Kabilanci da Addini:
Wasu sun zargi gwamnatin da nuna son kai (nepotism), musamman wajen nade-naden shugabanci da mukamai.
RAYUWA DA MUTUWARSA
Bayan kammala mulki a 2023, ya koma gidansa a Daura, Jihar Katsina.
Ya dauki hutu daga harkokin siyasa.
Ya rasu a shekarar 13-7-2025.
Da Minene Y’an Kasar nan zasu tuna da Shugaba Buhari?
Nasir Ibrahim Janbuzu 2025